YAR NAJERIYA CHAPTER 6 BY SUMAYYAH ABDULKADIR

YAR NAJERIYA CHAPTER 6 BY SUMAYYAH ABDULKADIR
YAR NAJERIYA CHAPTER 6 BY SUMAYYAH ABDULKADIR                    Www.bankinhausanovels.com.ng  Hasna’u na shiga gida kai tsaye bangaren su ta nufa da sassarfar ta, Hajjo matar Kawu na zaune kofar dakin ta tana kallon ta ta shige bata ce mata komai ba, kayan ta da aka shigo da su duk Hajjo ta sa an tule mata a kofar dakin Innar ta. Don ma kada a fara cewa a dakin ta zata zauna. Tun daga kofar sassan take kwada sallama tana fadin. “Inna kina kusa? Inna gani na dawo!” Ta sa kai a rumfar, duhu dudum, ya bakunci idanun ta, Inna bata kunna aci-bal-bal da ta saba kunnawa ba, ko mai yasa?. “Inna lafiya kike zaune cikin duhu haka? Wai kina ina ne ko gyaran murya bazaki min ba in sallah kike yi?” Ta fada tana lalube a cikin dakin. Sai ta jiyo gyaran muryar Kawu daga bayan ta, yana haska tocilan yana tahowa. Yace “Hansai dakko kayan ki ki biyo ni” cikin damuwa tace “Kawu ina Inna ne? Ko bayi ta zaga?” Kawu yayi gaba bai kula ta ba, sai ta bishi da gudu-gudu cikin alamu na fara shiga rudu, har ta riga s…