YAR NAJERIYA CHAPTER 5 BY SUMAYYAH ABDULKADIR YAR NAJERIYA CHAPTER 5 BY SUMAYYAH ABDULKADIR Www.bankinhausanovels.com.ng Saheeb, yana falon su a zaune yana jiran fitowar Hasna’u cikin tsananin bacin rai bayan shigewar Nusaiba dakin Mama. Ya ji shiru-shiru har wajen mintuna talatin ba Hasna’u, sai yayi tunanin ko ta canza shawara tana wankan ne don haka ya cigaba da jiran ta yana yi yana duba agogon hannun sa yana tsaki, don ba karamin bata masa rai Nusaibah ta yi ba har bai san sanda yayi furucin da ya yi ba, kuma an ce Magana Zarar Bunu ce… ta riga ta fita, bashi da ikon mayar da ita.1 Tsoron shi Allah tsoron shi kada ta je ta hada shi da Mama, don haka yayi maza ya bi ta dakin Maman, ilai kuwa yana gab da shiga ya ji ta tana waya ya kuma tabbatar ba da kowa bane da Mama ne “…..wannan zabiyar ta Unity ya kawo mana gida har yana neman duka na don nace bazan bata soso na da sabulu na tayi wanka ba har da cewa……”. Saheeb ya yi maza ya doke wayar daga hannun ta ta fadi kasa, ya bi ta ya take da takalmin sa ta warga…