UWAR GIDAN BAHAUSHE CHAPTER 6 BY SHATU UWAR GIDAN BAHAUSHE CHAPTER 6 BY SHATU Www.bankinhausanovels.com.ng Kafin wani lokaci kowa yasan cewar Rayha aure zaayi Mata, hakan yasa Yaya Ismail yaga wannan dama ce gareshi Dan ya aureni, idan yaso zai tsiri karatu se kawai mu fita overseas muyi karatun mu dawo. Ummaah ya samu ya fada Mata abinda yake tunani se tace Masa+ ” Ismail me yasa Sofy kawai kake so?” Saboda Anty jidda ta fara zugata tana fada Mata me yasa zata Bari dan da take ji dashi Wanda akwai high tendency zai iya rike sarautar masarautar Kano ya Kare da auren Yar makiyiyar su, Ummaah ta fara tunanin Anya zata Bari auren yayi. ” Ni kawai Ummaah Ina sonta, Dan Allah kada ki Bari na rabu da ita. Bansan ya zanyi ba” Da fuskarta a tamke take Dan haka Anty jidda tace Mata tayi, Amma ganin yadda rabin ran nata yake ta marairaice mata yasa ta sassauta tace ” Se kace ba namiji ba. Bari na Kira kawun ka naji” A lokacin ta Kira Baba Wanda ke zaune gefen Anty Rumasa’u tana zuba mishi abinci, ya Kai hannu itama ta …