UWAR GIDAN BAHAUSHE CHAPTER 4 BY SHATU UWAR GIDAN BAHAUSHE CHAPTER 4 BY SHATU Www.bankinhausanovels.com.ng Na dawo na zauna a parlon na rasa me yake min dadi a zuciyata, na saka kaina cikin cinyoyina na fara kuka a hankali, saboda komai nawa a nutse yake. Ina cikin kukan naji muryar Baba Yana sallama, nayi saurin mikewa na goge fuskata sannan na amsa masa Amma muryata Bata fita ta rigada ta dashe. Daya shigo seda ya kalleni for like 30secs kafin ya dauke kan shi yace ” Har yanzun Kuna zaune Baku shirya ba?” Na sunkuyar da kaina jin hawaye Yana ziraro min ta gefen idanuna, nayi saurin saka hannuna na goge Amma na kasa Masa magana, haushin shi nake ji kamar na rufe shi da duka Allah ya yafe min, ” Ni zamu wuce da Rumasa’u da Ayaan, kawun ku zai zo ku tafi” Na gyada Kai Ina sake goge idanuna Bai jira komai ba ya fice daga gidan, na bi bayan shi da kallo se Naga he seems strange kamar ba Baba Dana sani ba. Na Kara sakin kuka Anisah na kuka jikina, nafi awa zaune kafin na Mike na fara harhada kayan namu, na Gama …