UWAR GIDAN BAHAUSHE CHAPTER 13 BY SHATU UWAR GIDAN BAHAUSHE CHAPTER 13 BY SHATU Www.bankinhausanovels.com.ng Naji saukar shi daga gadon, naji Kuma fitar shi daga dakin, Amma gajiyar da Kuma baccin da ke cikin idanuna se Suka hana ni na bude idon, ban Kara kwakwaran motsi ba se wajen karfe goma na safe sannan na tashi, shima Rana ce ta cika dakin ta damu idanuna, Babu yadda zanyi Dole haka na Mike Ina jin jikina duk yayi min tsami kamar nasha duka. Na daga kafafuna cikin dabara na wuce toilet, daga idanuna nayi na kalla toilet heater se Naga ta ma tafasa, I had a hot bath da yasa na danji Dadi sannan na fito na dawo dakin, yadda na barshi haka nan yake, se na fara tunanin Ina Albi yaje da safiyar nan, se na Kuma tuna ko ya leka wajen matar shi. Na zauna gefen gadon bayan na jona hair dryer a socket na busar da kon sannan na shafa Mai na Kama da band. Na goge jikina na shirya cikin bakin lace me adon orange flowers. Nayi stretching sheets din gadon, daga karshe se na yaye sheet din na dakko sabo na shimfida,…