TAWA TA SAMENI CHAPTER 35 BY HALIMA ABDULLAHI K/MASHI

TAWA TA SAMENI CHAPTER 35 BY HALIMA ABDULLAHI K/MASHI
TAWA TA SAMENI CHAPTER 35 BY HALIMA ABDULLAHI K/MASHI Www.bankinhausanovels.com.ng  Mun tsaya  ranta kar na kusanci yarinyar kuma ba zan iya ba tunda ina tsananin sonta na zabi ba zata haihun ba to ynxu tun bamu je ko ina ba gashi ta samu ciki,Dr Salihu yace kaima ka san dole ne tayi cikin tunda ba wani mataki ka dauka ba sannan zaka cutar da ita in har kace ba zata haihu ba akwai nau’in zalinci,yaynmu yace naso a dan dauki lokaci ne sannan na san yanda zanyi na shawo kanta na san bai kamata nabi son rantaba na saba ma Allah, amma ina son na ganar da ita a hankali,Dr ya ce gashi ka soma magana a gabanta yace wannan ba wani abu zan shawo kanta, ni kam lokacin na kifa kaina a tebir din likita sai kuka nake yi, cikin da Www.bankinhausanovels.com.ng na kwallafa rai shi ne yaynmu yace a cire min ko da yake ba mamaki tunda dama yaynmu ba wai yana sona ba an dai bashi ne,soyayyar da yayi ta nuna min don ya mori albarkatun kirjina ne,ina wannan tunanin suka shigo yaynmu ya zo gurina ya kamani muka ida ko…