NI DA YAYA SADEEQ CHAPTER 6 NI DA YAYA SADEEQ CHAPTER 6 Www.bankinhausanovels.com.ng ______dawo da kallan sa yayi izuwa gare ni ya wurga min harara kana ya kalli Zuby da take cika tana ba tsewa saida ya saki fuskar sa ya fad’ad’a ta da Murmushi yace “uwar gida sarautar mata duk kishin ne haka ko gaisawa kin ki bari muyi ki kwantar da hankalin ki akan wannan abar”. Ya nuna mata ni da hannu kana ya cigaba da cewa “ina da ke mai zanyi da ita ko baki kare mata kallo bane? Ko matan duniya sun kare bazan so wannan abar ba danni kallon na miji nike mata”. Muryan Zuby a dakushe tace “to halakar ka da ita da zaka zo gurina sai kazo da ita, ni wallahi har kasa naji na tsane ta saboda ko macen kuda bana son tare beka bare kuma macen da da halakar aure zai iya shiga tsakanin ku, ina kishin ka ina yi maka son da bazan iya kwatan ta maka ba idanuwa basa iya ganin sa dan Allah Sadeeq kada ka ci amana ta ka soni koda rabin san da nike maka ne “. Idan Zuby har ya cika da kwalla, Sadeeq kuwa jikin sa yayi sanyi a …