NI DA YAYA SADEEQ CHAPTER 2 NI DA YAYA SADEEQ CHAPTER 2 Www.bankinhausanovels.com.ng _____Jin jina kai Inna tayi, sannan ta nufi hanyar d’akin da Momy take, ta ‘kwan ‘kwasa musu kofa, ta d’an jima a bakin ‘kofar, kafin Momy ta bud’e ta fito, “ina kwana hajiya”. Momy ta gaisar da hajiya+ cikin sakin fuska Inna ta amsawa surukar ta “ya ba’kun ta?”. “Lafiya lau”. Momy ta bata amsa, “to alhamdu lillah”. A cewar Inna ta dora da cewa “kiya ‘kuri na tashe ki kina tsaka da bacci”. “babu komai Inna” cewar Momy, Inna ta cigaba da cewa “daman Garba ne wai tun asuba yake ban d’aki”. Har yanzu bai fito ba, Siddi’ka tace “yau kamar bashi ba yana tayin wasu abu irin na taba’b-‘bu” shine nace “bari na tada ki muje bayin mugani ko lafiya”. Momy tace “Hajiya Inna badon karkice na raina ki ba da bazani ba tunda shi bayajin magana”. Inna tace “Ha’kuri zaki Aisha muje mugani ko lafiya kinga da ya idar da sallar asuba yake tafiya gurin aiki, amma yau shuru”. “To”. Momy tace badon ranta yaso ba, tabi inna ban ‘dakin Koda su Momy suka ‘kara sa ba…