NI DA YAYA SADEEQ CHAPTER 1
NI DA YAYA SADEEQ CHAPTER 1 Www.bankinhausanovels.com.ng _______A zaune nike a kan tabarma cikin baranda isaka na kad’a bishiyar mangwaron da ke tsakiyar gidan mu Ganyen ta na fad’owa ‘kasa gunin burgewa Dambu ne a gabana cikin wata ‘yar samira inaci ina sud’e yatsun hannu na saboda dambun yayi min dad’i banason ya’kare Kawata Ladiyo. Ce ta shigo gidan mu hannunun ta rike da goshin ta yana zubar da jini koda na d’aga kaina na kalle ta bance mata komai ba Na maida kaina kasa na cigaba da cin dambu na, Saida na cinye dambun tas Sannan na kora da ruwa, Baki na bud’e iya ‘karfi na Nayi wata katuwar gyatsa tarashin mutunci, Irin wacce idan yaya Sadee’k ya na guri nayi yake buge min baki.+ Kallan Ladiyo nayi Na ta’be baki nace “Ladiyo lafiya kika zo ki ka tsaya min a kai ko aiko akayi?”. Ladiyo. Dama jira take in tambaye ta, saboda tasan in bani na tambayeta ba tana iya fad’a min na bata kunya tana kuka take fad’a min abinda ya faru. Tace “Kinsan yaron da jiya muka barar mai da markad’e ai Dazun…