MASARAUTAR JORDAN BOOK 3 CHAPTER 10 BY MAI_DAMBU MASARAUTAR JORDAN BOOK 3 CHAPTER 10 BY MAI_DAMBU Www.bankinhausanovels.com.ng Lokacin da aka fito da Babyn, aka kawo musu k’in karb‘a yayi yana kallon Nurse din da ta kawo babyn, dakyar ya bud’e baki yace. “Ina mata ta?!” Sunkuyar da kanta tayi cikin sanyin jiki tace. “Tana ciki sai dai muna kokuwar dawo da numfashita ne, dan yana kwacewa.” Kamar wacce zai bugata da kasa yayo kanta. “Ina mata ta nace.” “Kay! hakur sir! Muna bakin kokarin mu akanta.” Shigewa tay! ta barshi a gurin, sai Safa da marwa yake. Ko kalfon yaron dake hannun Ghanwyu bai yi ba, suna tsaye Nurse din ta kuma fitowa ta amsht yaron ta shiga dashi, sannan ta koma, ciki bayan mintuna goma sha biyu ta kuma fitowa da sauri, ga baki daya sun birkitawa Ashraf lissafi. Dan kaiwa da komowar da suke kad’ai ya isa ya tabbatar maka SAFINAH tana cikin wani halt. Zama yayi ya cusa hannunshi cikin gashin kan shi, yana jin tashin hankalin da ya ci kaniyar wanda suke ciki. Www.bankinhausanovels.com.ng Kuma abin takaici duk yadda Bil…