ZURI'A DAYA BOOK 1 CHAPTER 8 BY SA'ADATU WAZIRI GOMBE

ZURI'A DAYA BOOK 1 CHAPTER 8 BY SA'ADATU WAZIRI GOMBE
ZURI’A DAYA BOOK 1 CHAPTER 8 BY SA’ADATU WAZIRI GOMBE  Www.bankinhausanovels.com.ng  Duk jikin mu ya yi sanyi ni da Maryam, take naji hawaye sun zomin, na ce. “Abdulhameed kai yaro ne, a matsayin shekarun ka da karatun ka ai ya yi wuri ace kana da aure, kuma ga ta da lalura, shin ya zaka yi da karatun ka?” “Granny idan za a yarda na auri Aziza a yanzu a cikin wannan halin zan iya hakura da komai har karatun na tsaya na lura da rayuwar ta saboda nasan na girma zan kuma iya kula da ita don haka yanzu na fadawa Daddy haka ne shi yasa muka zo nan tare domin ke kadai ce za ki yarda da haka auraminita”, Umma wannan haka yake, gaskiya ya fada, ki daure ki yarda da hakan”. “Jafar babu damuwa tun da ZURI’A DAYA muke, babu wani abu da zai gagara a ciki, amma ku dan yi haKuri ka ci gaba da fahimtar Abdulhameed, insha Allahu shi ne zai auri Aziza bayan ta ji sauKi, amma dai mu jira mu ga yadda hukuncin da Ubangiji zai zartar”. “Shi kenan, Allah Ya bata lafiya, bari mu Karasa gurin Mustapha din”. Haka s…