ZURI'A DAYA BOOK 1 CHAPTER 7 BY SA'ADATU WAZIRI GOMBE

ZURI'A DAYA BOOK 1 CHAPTER 7 BY SA'ADATU WAZIRI GOMBE
ZURI’A DAYA BOOK 1 CHAPTER 7 BY SA’ADATU WAZIRI GOMBE  Www.bankinhausanovels.com.ng  Har yanzu bata iya motsi, ga dai alamu tana da rai ba mutuwa tayi ba, amma idan ka ganta ka zata ta mutu. Alh. Jafar, Alh. Aminu da Mustapha suna zaune a (officc) din manyan likitoci guda biyu suna yi musu tambaya. Dr. Sha’aibu yace, “Kamar yadda muka tambayeku cewa tsawon awanni nawa aka yi da faruwar wannan al’amari ku kace baku sani ba Yadda binciken mu ya nuna ta shafe awanni uku cikin wannan yanayi wanda jinkin da rashin samun taimako a lokacin da abin ya faru ya janyo mata illoli da dama, na farko dai a yanzu tana cikin koma zata jima a haka, idan Allah Ya kawo cikin sauki zata iya farkawa ta dawo cikn tunaninta, idan kuma aka samu rashin sa’a zata iya zautuwa gaba daya ko kuma tayi mantuwar abinda ya gabata a baya (losing memory). Illa kuwa ta mutuncinta anyi mata sosai, amma zamu yi iya yinmu don ganin munyi nasara akan aikinmu” “Lahaula wala Kuwwata illa billah! Ya Allah Ka fitar da yarinyar nan d…