ZURI'A DAYA BOOK 1 CHAPTER 6 BY SA'ADATU WAZIRI GOMBE

ZURI'A DAYA BOOK 1 CHAPTER 6 BY SA'ADATU WAZIRI GOMBE
ZURI’A DAYA BOOK 1 CHAPTER 6 BY SA’ADATU WAZIRI GOMBE  Www.bankinhausanovels.com.ng  ZURI’A DAYA CHAPTER Cikin wani irin yanayi yake mata magana, ya ce. Matar daga ina haka? Kamar kuwa kin san ke na fito ko zan hango ki sai gashi kuma na ganki”. Tayi murmushi ta ce, “Ba wani nan, don ka ganni ne yasa ka ce haka. To daga gidan rasuwar nan nake Haana ta hana mu sakat shi ne Ammi ta ce na zo gida da ita mu zauna ko tayi barci, don taga alamun fita kawai zata yi a gurin, gashi ta ishe mu da surutunta da baya Karewa, don ita ba zata gane wane hali ake ciki ba. Kuma nima dama na gaji, ji nayi kai na ya fara ciwo shi ne nake son mu koma gida mu dan runtsa kafin su dawo, gashi kuma rana ta soma takewa”. ““(Okay) nima ban jima da dawowa daga gidan ba, don bana son hayaniya. Oya to muje na raka ku gidan mana”, A’ah, da ka ma barshi mun Karasa, kaima kaje ka huta”. Bai bata amsa ba ya sa hannu ya dauke ki ya saka ki a kafada suka jero suna hira, ke kuwa kin fara surutunki kafin ku Karasa har bacci y…