ZURI'A DAYA BOOK 1 CHAPTER 14 BY SA'ADATU WAZIRI GOMBE

ZURI'A DAYA BOOK 1 CHAPTER 14 BY SA'ADATU WAZIRI GOMBE
ZURI’A DAYA BOOK 1 CHAPTER 14 BY SA’ADATU WAZIRI GOMBE  Www.bankinhausanovels.com.ng  Shi kenan Abdulhameed, insha Allahu zan taimaka maka a fitar da hakKin Allah akan ka, tunda hakan ya faru, amma kasan dole sai munje kotun tare sun yi maka tambayoy sannan su aiwatar maka”, Murna ce ta bayyana a fuskar hameed, ya tashi ya rungume Malam Liman yana kuka, nan take tausayin Hameed da Kaunar sa suka cika ransa, nan ya tambaye shi akan ya fada masa cewa ina iyayen sa suke da zama? Ya kada harshe ya ce, “Baba kamar yadda na fada maka cewa mahaifina baya goyon bayan da a hukuta ni, don haka yasa na na gudo nan har Allah Ya hada mu da kai, don haka ka wakilci Iyaye na ka zama cewa kai yayan Babanane nazo mala da wannan labarin shine ka kawo ni nan don ayi min bulalar”. Liman da kansa ya bashi masauki a gidan sa cikin dakin yaransa manya guda uku, ya hada su guri daya shi kuma ya bashi daki daya don ya samu ya sake sosai. Kwanan sa biyu a gidan ranar nan sun dawo daga kotun Musulunci da yamma an ga…