ZANEN DUTSE CHAPTER 7 KARSHE BY AISHA-SHAFIEE

ZANEN DUTSE CHAPTER 7 KARSHE BY AISHA-SHAFIEE
ZANEN DUTSE CHAPTER 7 KARSHE BY AISHA-SHAFIEE                    Www.bankinhausanovels.com.ng  Gidan a share yake tas, dama ya gaya mata tun a hanya, yace ya saka yaron da yake masa shara kafin zuwanta ya gyara, don haka sai taga kamar jiya suka tafi yau suka dawo. Komai yana nan inda yake ba’a taɓa ba, hatta ƴar ragowar dubu ɗayanta da ta bari a cikin wardrobe tana nan, don haka tana ajiye kayanta banɗaki kawai ta shige tayi wanka, ta janyo daya daga cikin dogwayen rigunanta mai sauƙin nauyi wata ƴar fale-fale kalar sea green ta saka, ta feshe jikinta da ɗaya daga cikin turarukanta da bata taba sawa ba sannan kai tsaye ta nufi wajen sahibul qalbinta… Kitchen.3 Madaki bai ƙaraso ba har a lokacin don bayan sun iso gari, direbobi biyu suka tadda a parking lot na airport ɗin, ɗaya ya kawo motar Mubarak ɗaya kuma Baba Saminu ne da motar Madaki, kuma sai bayan sun rabu da Mubarak ne sun shigo motar yake gaya mata cewar yayi booking appointment zai tsaya a asibiti ganin likitansa don haka baya…