ZANEN DUTSE CHAPTER 7 KARSHE BY AISHA-SHAFIEE
ZANEN DUTSE CHAPTER 7 KARSHE BY AISHA-SHAFIEE
Www.bankinhausanovels.com.ng
Gidan a share yake tas, dama ya gaya mata tun a hanya, yace ya saka yaron da yake masa shara kafin zuwanta ya gyara, don haka sai taga kamar jiya suka tafi yau suka dawo. Komai yana nan inda yake ba’a taΙa ba, hatta Ζ΄ar ragowar dubu Ιayanta da ta bari a cikin wardrobe tana nan, don haka tana ajiye kayanta banΙaki kawai ta shige tayi wanka, ta janyo daya daga cikin dogwayen rigunanta mai sauΖin nauyi wata Ζ΄ar fale-fale kalar sea green ta saka, ta feshe jikinta da Ιaya daga cikin turarukanta da bata taba sawa ba sannan kai tsaye ta nufi wajen sahibul qalbinta… Kitchen.3
Madaki bai Ζaraso ba har a lokacin don bayan sun iso gari, direbobi biyu suka tadda a parking lot na airport Ιin, Ιaya ya kawo motar Mubarak Ιaya kuma Baba Saminu ne da motar Madaki, kuma sai bayan sun rabu da Mubarak ne sun shigo motar yake gaya mata cewar yayi booking appointment zai tsaya a asibiti ganin likitansa don haka bayan sun sauke shi, ita kadai Baba Saminun ya Ζaraso da ita gida sannan ya koma Ιauko shi.
Ta nufi kitchen Ιin zuciyarta na yawo a gajimare kan tuna yadda gabadaya tafiyar ta shafe hannunta na cikin nasa yana zana wani abu kamar adadin yadda zuciyarsa ke Ζaunarta, kuma saboda Mubarak a tare dasu basu yi wata magana mai tsawo ba amma lokaci-lokaci ya kan tambaye ta wani abu game da kwanakin da suka shafe basu haΙu ba, kwanakin da har yanzu bata ga laifinsa ba don bai nemeta ba, mahaifinsa ya rasa cikin mutuwa irin wadda tafi taΙa zuciya da shiga ciki, mutuwar bazata, to kuwa don shi yafi kowa Ιokin aure sai ya manta komai ya neme ta a cikin dubunnan jama’ar masarautar nan? Mutanen da ko a yau da suka taho an share makoki ma amma ba kowa ne ya gama tafiya ba.4
Dukkan tunaninta sai yabi iska a lokacin da ta buΙe Ζofar kitchen Ιin nan tayi arba dashi, haΙadden kitchen Ιin da a yanzu babu wani kokwanto ta san zata rayu dashi tsawon lokaci, shima a share yake tas, Ζ΄an dim fitilolin nan na Ζasan drawers Ιinsa na haskawa yayin da lubalensa na jikin window yake a rufe… Ya Allah! Ashe tayi kewarsa kamar me…!4
Labulen windon ta fara budewa sannan ta nufi fridge ta buΙe don taga lafiyar kayan cikinsa, ilai kuwa duk da sanyin da yake yi su karas da kabeji dake Ζasa sun fara ruwa ta gefensu wasu ma sun narke gaba Ιaya. Don haka ta fito dasu ta ware Ζ΄an ragowar da suka rage masu kyau sannan ta wanke su ta canja musu waje, kafin ΖwaΖwalwarta ta shiga lisasafin abinda zata dafa mai sauki, don yamma ta fara yi kuma ta san ba lallai Madaki ya kai magriba ba.
Ta nufi store ta buΙe tana kallon kayan abincin sai idonta ya kai kan kwalin wata taliya mai irin siffar shinkafa, don haka a lokaci guda ta yanke shawarar yin jollof dinta, sai ta danyi farfesun ragowar kifin da ya rage mata guda Ιaya a fridge.
Wuyar girki shine in baka sami kayan aiki akan lokaci ba, da yake tana da komai har markade a fridge cikin lokaci kankani sai ta hada ruwan jollof Ιin har m ya tafasa ta zuba taliyar, tana yi kuma tana grating din atturuhu da albasa na farfesun bayan ta fito da kifin daga fridge, cikin Ιan lokaci sai gashi shima ta gama hada shi kitchen din ya baΙe da Ζamshin curry kala-kala. Sai kuma tayi tunanin ta Ιanyi coslow tunda bata saka nama a jollof Ιin ba don haka ta nufi fridge ta fito da kabeji da karas kawai ta fara yankawa tana ganin ai yanzu ma zata gama komai, abinda bata sani ba shine lokaci ya tafi da yawa itace kawai dake jin dadin aikin bata gani ba.
Kuma hakan ne yasa kwata-kwata bata ji Ζarar buΙewar Ζofar kitchen Ιin ba sai gani tayi alamun mutum na tahowa gabanta, tana tsaye ne a tsakiyar kitchen din daga gefen island Ιin nan, ta dora plate Ιin da take yanka kabejin akan island Ιin yayin da ita take tsaye, jin motsi yasa idonta ya kai hanyar Ζofar ya dawo kafin ta sake maida shi da sauri ta kalli Madakin dake shigowa, hannayensa duka biyu sanye cikin aljihun wandonsa yayin da lumsassun idanunsa ke kallonta.
Ta kalli Ζofar bayansa sannan ta sake dawowa ta kalle shi a lokacin da ya tsaya a Ιaya Ιarin teburin.
“Wa’alaikum salam.”
STORY CONTINUES BELOW
Ta amsa sallamar da bata ji ta ba har a lokacin da mamaki akan fuskarta, sai ya motsa gefen bakinsa cikin wani abu da bata tabbatar murmushi bane sannan yace.
“Nayi sallamar, baki ji ni bane.”
Kamar ta bashi amsa da cewar don bai yi maganar da Ζarfi bane sai kuma ta fasa, ta gyada kanta kawai sannan tace.
“Sannu da zuwa.”
“Yauwa.” Ya amsa a gajarce yayin da idaunsa suka zamo kan hannayen ta da kuma farantin kabejin da take yankawa.
“Baki gaji da hanya ba kike aiki?”
Muryarsa ta fito a hakali yana kallon yadda yatsunta ke rike da wukar ba tare da ta cigaba abinda take yi ba, wani abu ne ke bi takan zuciyarsa a lokacin, wani abu da bai san menene ba, yana ΖoΖarin fasa ginin daya lullube ta, bai san menene shi ba, nutsuwa ko kuma dadi na cewar aΖalla yana da wani abu mai muhimmanci a rayuwarsa, bai rasa komai gabaΙaya ba.
Allah ya sani shi ya manta ma da wani lissafin abinci balle ya hango cewar in har shi bai damu ba ita zata nemada sun tsaya tun a hanya sun siya ya hutar da ita, amma kuma shima yanzu da yaji Ζanshin sai yaji cewa cikinsa ya faΙa don ko breakfast Ιin safe da aka kawo musu kaΙan kawai yaci ya tashi ya shiga neman Sunusi akan yaje banki ya ciro masa kuΙi don na hannunsa sun Ζare.
Kamar tace ‘Ta gaji, amma saboda shi take yi…” Sai kuma ta fasa don watakila basu Ζaraso gabar wannan kai tsayen ba, saboda haka ta cigaba da yankanta a hankali sannan tace.
“Baka da lafiya dama?”
Ga mamakinta sai yayi wani abu da ya tabbatar mata cewa sun bar irin rayuwar da suka fara a gidan ta farko kafin ya bata amsa, kujerar jikin island Ιin yaja ya zauna daidai saitin inda take tsaye sannan ya ajiye wayoyinsa biyu akai.
“I’m fine, kawai naje check-up ne saboda heartburn Ιin daya dameni tun jiya.”
“Menene heartburn?”
Kai tsaye ta tambaye shi ba tare da ta Ιago ba, don ita kalaman turancinsa ba kowanne take ganewa ba, watakila nan gaba zata gaya masa cewa karatunta iyakarsa secondary kuma secondary ma ta cikin gidan Sarki. Sai ya Ιanyi shiru shima kamar ya manta sunan abin da hausa kafin yace.
“Wannan abin da yake tasowa daga Ζirjin mutum mai zafi…”
“Oh kwannafi?’
“Right, shi.”
Sai ta gyada kanta kafin tace.
“Allah ya sawwake Allah ya baka lpya.”
“Ameen Jay.”5
Muryarsa ta fito alamun yaji daΙin addu’ar, amma ba wannan ne yasa ta Ιago ta kalle shi ba, sunan da ya faΙa ne, J? Ita yake nufi? Sai dai kallon da yake mata yasa ta kasa wani tunani mai kyau ta haΙiye yawu ba shiri ta sake hadiyewa, don duk dauriyarta wannan lumsassun idanun nasa sai da suka sa zuciyarta ta buga sau biyu a lokaci guda.
“Me zaki hada da cabbage Ιin?”
“Coslow.” Ta amsa a take kamar yin maganar ne zai kore idanunsa da take ji kamar suna bi ta kan fatar ta ko kuma tunanin da zuciyarta ke son fadawa, amma kuma sai yayi shiru bai Ζara cewa komai ba, gwara suyi maganar gwara yace wani abu tun kafin ta rasa Ζarfin cigaba da yanka kabejin.
“Ai kana ci ko?” Ta tambaya muryarta na ΖoΖarin sarkewa.
“Ina ci, indai zaki bani.”
Me? Tuna mata zai yi da tana girki babu shi? Sai ta cije leΙΙenta na Ζasa a hankali sannan tace.
“Zan baka, indai likitanka bai hana ka ci ba.”
Ta san har yanzu kallonta yake, abinda bata sani ba shine har yanzu alhini ne ko kuma ciwon ne yasa waΙannan lumsassun idanun nasa ke ka kallonta kasa-Ζasa haka?
STORY CONTINUES BELOW
“Doctors Ιina suna da kirki, basa hana ni cin dadi, gishiri ne kawai basa so in cika ci da yawa.”
“Coslow shine daΙi?”
“Bashi da daΙi?” Ya dawo mata da tambayarta.
Sai ta girgiza kanta.
“Yana da dadi a wajen Ζ΄an gayu, amma ni bai dame ni ba.”
“Meye ya dame ki?” Yana harde hannayensa akan taburin sanda ya tambayi hakan, wadannan dogwayen hannun nasa.
Jidda bata taΙa wani iya kewaye-kewaye ko Ζarya ko iyayi ba, saboda haka kai tsaye cikin Ζ΄ar sakewar hirar tace.
“Manja, yaji, ko kuma duk wani abu da za’a saka masa atturuhu da albasa yaji kuma maggi sosai.”
A yanzu ta tabbata abinda yayi a Ιazu murmushi ne, don ba kallonsa take yi ba amma har sautinsa yanzu taji.
“Shi yasa baki da Ζiba ashe.”
Sai ta Ιago ta kalle shi mamaki na haskawa a fuskarta.
“Bani da Ζiba? Baddo kuwa kullum cewa take yi ina da jiki, tace nafi Jamila ma.”
Ya gyada kansa.
“Eh kina da jiki, amma baki da Ζiba, ina ganin kamar zan iya karya Ζugunki da hannuna kawai.”
“A ina…”
Maganar Jidda ta katse saboda wani Ιangare na ΖwaΖwalwarta da ya kwalla ihu a cikin kanta, tambayarsa zaki yi a ina ya taba gani?? Sai kawai ta sunkuyar da kanta sannan ta canja zancen da cewar.
“Babu grater a kitchen Ιin nan ko?”
Bai bata amsa kai tsaye ba, taji alamun ya cigaba da kallonta, idanunsa na shigarta don tana jin tasirinsu har a cikin yatsun Ζafarta.
“Zaki fini sani don yanzu kitchen Ιin naki ne ai Jay, duk sanda kike bukatar wani abu idan kiyi list kawai zan bawa Baba Saminu ya kawo miki.”
Abubuwa da yawa sun hadu a cikin wannan maganar, Kitchen Ιin nata ne sannan sunan Ιazu ya sake faΙa, J… Sunan da zai dinga kiranta dashi kenan? farkon sunanta… J. Ya Salam! Ashe zata taba samun suna mai dadi haka? Amma tsaya, bayan haka me yace ne? Tayi list Ιin abinda take so a kitchen Ιin? Da yawa fa, ko dai tace ya bata kudin ne kawai taje kasuwar da kanta? Zai ga zaΖewarta kuma ai, don a ka’ida ma bashi yake da alhakin siya mata kayan girki ba iyayenta ne, kuma saboda kawai auren ya faru a banbarakwai ne da ta sani Baddo zata yi iya kokarinta itama ta siya mata duk abinda zata bukata. Don haka tunda dai shi ya tambaya yanzu ba roΖa tayi ba, zai ga list kuwa.2
Saboda haka ta gyaΙa kanta sannan tace.
“Insha Allah, Madallah. Allah ya saka da alkhairi.”1
Watakila ya amsa amma dai bata ji ba, wayarsa Ιaya da ta shiga vibrating akan island Ιin ya dauka ya shiga waya da wani Habibu har ma aka hada shi da wani Samuel ta cikin wayar, don haka ta karasa yanka karas Ιinta Ζanana sannan ta mike taje wajen girkinta, ta kashe wutar kifin amma taliyar bata gama ba har a lokacin don tana da Ιan tauri fiye da asalin taliya, sai ta tsaya a jikin sink don ta sake wanke karas da kabejin kafin ta dawo ta hada coslow Ιin.
Madaki ya dago daga wayar da gama a lokacin ya kalle ta, watakila don ya kwana biyu bai ganta bane, amma yana ji kamar fuskarta ta canja masa, kamar ta shafa wani abu daya kara fito da komai na zanen fuskar tata. Ya san haka ya santa dama tun farko, kullum fuskarta babu kwalliya amma a yanzu sai yake ganin kamar ta saka wani abu ne daban, musamman yadda kalar fatarta take, wani abu tsakanin baki da fari, kamar ruwan Ζasa ko na taΙo a lokacin da akayi ruwa, koma ace shayin da yasha madara da bournvita.1
Tunda suka taho a hanya yake jin wani abu ne ke yawo a cikin kansa yana gaya masa cewa da gaske yayi kewarta don yana jin kamar wuta ce zata tashi duk sanda ta Ιago ta kalle shi idanunsu suka haΙu, idan tayi masa magana kuwa, muryata na ratsawa ne har cikin ruhinsa, yana gaya masa cewa yaci ace sun wuce wannan matakin a yanzu, saboda haka sai kawai ya ajiye wayarsa ya isa gare ta a hankali kuma ba tare da yace komai ba ya tsaya a bayanta sannan yasa duka hannayensa biyu ya riΖo Ζugunta ya manna ta da jikinsa sannan ya sanya fuskarsa cikin wuyanta yana shakar Ζamshin turaren da ta fesa.8
STORY CONTINUES BELOW
Gayawa zuciyarsa yake cewa daga yau babu sauran wani abu da zai sake masa katanga da ita, ya san har yanzu bata bashi amsar daya nema ba amma he doesn’t care anymore, tunda har ta yarda ta biyo shi suka dawo ya san ta karbe shi kenan cikin rayuwarta don haka ko bata fada masa komai ba, ya samu amsarsa don haka ba zai iya dinga hana zuciyarsa abinda take so ba.
“Thank you for coming back, thank you Jay.”
(Nagode da kika dawo, nagode Jay.)
Ya faΙa a hankali yayin da fatar bakinsa ke gogawa a gefen wuyanta.4
Duk wata jijiya ta jikin Jidda ta shiga juyawa a take, tunaninta ya Ιauke sannan wani abu ya shiga hurawa a jikinta, yadda numfashinta ke busawa akan fatar wuyanta kaΙai yasa tunaninta hargitsewa, zuciyarta ta shiga bugawa a cikin kunnenta sannan Ζafafunta suka shiga rawa ta yadda duk da yana riΖe da ita, ta dinga jin kamar zata faΙi don haka babu shiri ta juyo da sauri a cikin hannayen nasa ta riΖo gaban rigarsa kamar hakan ne zai hana shi, sai dai kuma ba abinda ya kara ma illa sake riΖe ta da Madaki yayi sannan ya sunkuyo da fuskarsa ya lalubo gefen kunnenta a hankali yace.
“Can I kiss you?”6
Tambayar ta Ζwala wata Ζatuwar tsawa a cikin kan Jidda, ba shiri ta Ιago da fuskarta ta kalle shi idanunta na haskawa wani abu da bai gama tantance shi ba, sai kuma tayi saurin sakin rigar tasa zata matsa baya amma hannayensa dake riΖe da ita suka tuna mata cewa Ζarshen takunta kenan.
Sai kawai ya matso da fuskarsa ya kara goshinsa da nata sannan idanunsa suka sauka a lips Ιin nata.1
“Just one kiss…”
Hade da numfashi ya furta maganar cikin wani irin sauti da yasa ta rufe idanunta a lokaci guda tana jin kafafunta na Ζara lugwuiguicewa kamar dafaffiyar taliyar hausa. Ganin haka yasa ya matso da fuskarsa yayi brushing saman leΙΙensa akan nata sannan muryarsa ta sake fitowa cikin raΙa.1
“… Kinji?”
Jidda bata san sanda ta shiga Ιaga masa kai ba saboda wani irin abu da take ji yana ΖoΖarin hargitsa mata ΖwaΖwalwa, kuma ba tare da bata lokaci ba ya karkatar da kansa kaΙan sannan ya haΙe Ζ΄ar TAZARAR DAKE TSAKANINSU.2
Sai dai a daidai wannan lokacin ne limamin dake masallacin unguwar ya zaΙi yin kiran sallar magriba sannan wayar Madakin dake kan island ta shiga vibrating tana motsi akan glass Ιin alamun shigowar wani kiran. Jidda taji sanda yayi wani sauti kamar na Ζorafi kafin ya matsa da fuskarsa a hankali, idanunta a rufe suke amma ta tabbata taji sautin murmushinsa kafin ya zame hannayensa duka biyu daga jikinta.
“Ki jira ni Jay, zamu cigaba daga inda muka tsaya.”11
Abinda taji yace kenan kafin su juya dukkaninsu a tare, ita ta juya ta dafe jikin sink, yayin da shi kuma ya nufi wayarsa ya Ιauka sannan ya fita daga kitchen Ιin yana amsawa.
Ana idar da sallar kuwa bayan Ζ΄an mintuna kaΙan sai gashi ya dawo, a lokacin Jidda ta gama girkin har ta zuba a plate kasancewar babu wani flask mai girma a gidan, ta ajiye musu akan dining har da irin lemukan da yake sha a fridge da ruwa sannan ta tafi Ιaki yin tata sallar, don haka sanda ta fito yana zaune a dining Ιin yana jiranta, ya ciro cokalin dake daya plate din ya hada a nasa, kuma tun tana Ιan jan jikinta har ta saki jiki suka ci abincin, yana gaya mata cewa yayi daΙi sannan a hankali yana bata labaruka da suka danganci abin kala-kala, santi yake a fili amma bai sani ba, itama kuma bata faΙa masa saboda ΖwaΖwalwarta nata lissafin abinda ya faru Ιazu sannan a gefe guda kuma ta san aΖalla yana hirar ne don ya kore alhinin da yake ciki, don har yanzu tana iya jin hakan a muryarsa ma, magana kawai yake amma da damuwa a sautinsa.2
Saboda haka tayi ta binsa da gyada kai har suka gama cin abincin ta kwashe kayan, kuma da yake da sauran kayan data Ιata a kitchen sai wanke kwanukan ya dauke ta lokaci, har ya fita masallaci bata gama ba, don haka tana Ζarasawa da ta fito taga baya nan sai itama tayi sallarta anan falon sannan ta nufi Ιaki da niyyar yin brush da wanke fuskarta.
STORY CONTINUES BELOW
Sanda ta shiga dakin taji alamun babu iska don haka ta tuna ashe tun da suka dawo bata bude windows din ba don haka taje ta buΙe su sannan ta Ιage labulen daya ma ta soke shi a jikin Ζarafan windon, bata kunna fitilar Ιakin ba kawai ta kunna ta toilet Ιin ta shiga, kuma har ta gama brush Ιin tana mitar taurinsa a ranta saboda shima wannan matar mai saida maganin gargajiya ce ta siyo mata, ta wanke fuskarta tata sannan ta fito, tana murΙa Ζofar kuma abinda idonta ya fara gane mata shine Madaki tsaye a cikin Ιakin, a gaban wardrobe Ιinta ya buΙe kofofin gabaΙaya yana Ζarewa kayan ciki kallo.
Ta sako kafarta waje sannan ta rufe Ζofar a hankali amma duk da haka Ζarar ta shiga kunnensa tasa shi juyowa ya kalleta, hasken fitilar waje ta windon nan data bude ne kawai a Ιakin amma duk da haka tana iya ganin fuskarsa da kuma idanunsa wanda suka tuna mata da zuwansa na farko Ιakin sanda yazo da tambayoyin kalubalantar ta, kuma kamar wancan lokacin idanun nasa sun zurma ciki suna Ζara fitar da sheΖin maiΖonsu, sai dai a yanzu ta sani cewa damuwa ce kawai da alhini.
“Su kenan kayanki?”
Muryarsa ta tambaya a sake yana kallonta bayan ya rufe wardrobe Ιin. Abinda take tunani daban ne a wannan lokacin, babu dankwali akanta don wannan bandakin na cikin Ιaki ita ganinsa take kamar dakin shima don haka bata wani damuwa da sai ta saka Ιankawali, kuma shuku ne Ζanana akanta sai jelar bata fi kamu biyu ba an tufke ta a can baya don haka ta tabbata fala-falan kunnayenta sune a fili… Su yake kallo ma yanzu.6
Sai tayi Ζarfin halin girgiza kanta daga inda take tsaye sannan tace.
“A’a, akwai wasu a gida.”
“Ina nufin anan, wannan sune kaΙai kayanki?”
Sai ta Ιaga kai lokacin da ta Ζaraso bakin gadon ta dauki Ιankwalin da tayi wulli dashi akai.
“Eh, amma na taho da wasu suna cikin ledar da take booth din motarka.”
Shima ya karaso gabanta sanda take fadin hakan don haka babu wani Ιata lokaci yasa hannayensa duka biyu ya tallafo gefen fuskarta sannan yace.
“Ba motata ba, motarmu zaki ce, from now on duk abinda na mallaka kema naki ne Jay, don in har zan iya saki a zuciyata to zan iya baki duk wani abu dana mallaka, kin gane?”1
Kamar malami da dalibarsa sai ta gyaΙa kanta a cikin tafin hannun nasa alamun ta gane Ιin, kuma duk da haka sai bai janye hannun ba.1
“Hakan ya tuna min, baki bani amsata ba na ran nan…”
Yaji sanda fuskarta ta motsa a cikin hannun nasa alamun ta hadiye wani abu amma duk da haka bata dago ta kalle shi ba, sai ya matso da tasa kamar zai Ζara goshinsa a saman nata sannan a hankali muryarsa ta sake fitowa.
“Ko kawai mu tsallake wannan part din?”
Ga mamakinsa kawai ta miΖo hannayenta itama ta riΖo nasa sannan ta girgiza kanta kafin muryarta ta fito a hankali.
“Kar mu tsallake, nima ina son in gaya maka cewa zuciyata tana sonka, ina son in zauna da kai tsawon rayuwata sannan ina son in taimake ka ta duk hanyar da zan iya, na yarda cewa Allah ya riga ya haΙa Ζaddararmu waje Ιaya saboda tun kafin in sanka zuciyata ta riΖe sunanka kuma ban taba mantawa ba.”3
Madaki ya rufe idanunsa ya buΙe su a lokaci guda yana godiya ga Allah a cikin zuciyarsa kafin ya shiga motsa babban Ιan yatsansa a gefen fuskarta a hankali sannan yace.
“Waye ya gaya miki sunana?”
Yaji ta Ζara motsa fuskarta kamar mai shirya furta wani abu babba sannan muryarta ta sake fitowa akan hannunsa.
“Karantawa nayi a jikin takardar asirin dana taΙa tonewa.”
Tana fadin hakan ta Ιago ta kalle shi, don haka idanunta suka nuna mata yadda yanayin fuskarsa ya shiga canjawa zuwa mamaki cikakke, sannan ya matsa da fuskarsa baya yana kallonta kamar a lokacin ya fara ganinta.
“Asiri? Wane irin asiri?”
Ta girgiza kanta, hakan ya motsa hannayensa.
“Ban sani ba, na san dai Fulani ce tasa akayi kuma wadanda suka binne sunce wai zai sa baza ka dawo Lagos ba a lokacin sannan Ιayan kuma zai sa kayi duk abinda Fulanin tace ba zaka yi mata musu ba, amma duka na tone su, na farko laya ce da takarda na biyu kuma wani abu ne mai jini sai muka Ζona shi dani da Sadiya.”
“Tun yaushe wannan ya faru kuma me yasa baki taΙa gaya min ba?” Muryarsa ta fito fayau! Don saboda tsananin mamaki ba zaka iya tsinto komai a ciki ba.”
“Tun kafin in sanka ne, kuma ban san yaushe ya dace in faΙa maka ba, kuma ma naga al’amarin ya riga ya wuce ne.”
Wani abu ya ratsa tun daga kan Madaki har tafin Ζafarsa, ba wai zancen asirin ba don wannan kwanannen zance ne ya san cewa tun daga lokacin da Mai martaba ya danΖa masa dukiyarsa a tsaye take akansa, kuma addu’oin da yake dagewa dasu su suke sawa Allah ya ke kare shi daga sharrinta, don haka abin mamakin shine yadda Jidda ta kasance Ιaya daga cikin kariyar tasa, wace irin zuciya ce da ita ne wai? Tun bata sanshi ba take sa kanta a cikin hatsari don kare shi? Allah ya riga ya haΙa rayuwarsa da tata amma har ya bari da farko zuciyarsa ke zarginta kan wani abu daban, kan wani abu da baya son tunawa ma.
Sai kawai yasa hannu ya sake Ιago da fuskarta a hankali sannan ya dawo da fuskarsa ya kara goshinsa a saman nata.
“I love you so much Jay, ina so ki sani cewa kece abu mafi muhimmanci bayan mahaifina daya taba shigowa rayuwata kuma kece fatan dana daΙe ina rokon Allah ya bani, ba zan taba cutar dake ba Maijidda, zan riΖe ki amana kuma ina fatan Allah ya bani damar ninka miki fiye da farin cikin da kika kawo min a rayuwata…”
Kuma bai jira komai ba ya haΙe leΙΙensa da nata a hankali cikin wani irin salo nasa shi kaΙai, wani irin salo da yasa Jidda ta sake damΖe hannayenta akan nasa sannan tafin Ζafarta ya Ιaga sama don tana ji ne kamar wani abu ne ke janta zuwa can sama, kamar zai yi fiffike ne ya tashi da ita zuwa wata duniya tasu su biyu kawai.
A hankali ya Ιan ja daga jikinta amma ba tare da ya raba fuskarsa da tata ba sannan muryarsa ta fitowa a hankali yana kallon idanunta dake rufe.
“Kin yarda dani Jay? Kin yarda da duk abinda na faΙa?.”
Idanunta a rufe suke, gashinsu a sauke ba mai tsawo ko laushi ba amma a cike yake taf cikin layi mai kyau, sai ta Ιaga kanta a haka ba tare data bude idon ba, kuma bata daina Ιaga kan ba har bayan ta san ya fahimce ta Ιin, so take ya Ζara sani shima cewa a shirye take ta zama abu mafi muhimmanci a rayuwar tasa, ya san cewa zata zauna tare dashi a kowanne yanayi na farin ciki ko baΖin ciki, zata shiga har cikin zuciyarsa ta fahimci kowanne faΙuwa da tashin dake jikinta, ta san duk wani ciwonsa ta yadda zata zama haske a duk wani waje da yake da duhu a cikinta.
Madaki ya Ζara kissing Ιinta a hankali kuma wannan karon yafi kowanne tasiri don har sai da jikinta yayi rawa a cikin hannunsa sannan numfashinta ya shiga kakkatsewa, sai ya zame hannunsa Ιaya daga fuskarta ya riΖo ta sosai a cikin jikinsa yana Ζara gaya mata wani saΖo da bai taΙa gayawa kowacce mace a duniya bayan ita ba, wani saΖo da yayi kaca-kaca da duk wani ragowar lissafi da tunani Jidda, don haka bata san sanda ta maida hannayenta biyu ta riΖo wuyansa ba itama, manyan yatsunta biyu sirara suka sauka a gefen Adam’s apple Ιinsa daga kowanne gefe tana jin motsawarsu yayin da bakinsa ke motsawa, kuma hannunta a wajen shine wani abu da ya Ζara susuta dukkan wani sanity na Ibrahim Ahmad Madaki!2
Iska ta tuge labulen da Jidda ta Ιage daga can jikin windo a lokacin, don haka hasken da yake shigowa ta waje ya disashe, duhun Ιakin ya baiyana, wani irin duhu mai lumshi.2
Kuma a cikin wannan duhun ne, tushen wata sabuwar rayuwa ya wanzu.”Nadiya…”
Muryar Abdallah ta kira ta cikin wayar dake kare a kunnen Nadiyan, a lokacin tana zaune ne akan bedside drawer Ιakin Safina bayan ta baro Ιakin mahaifiyarta, Fulani.+
“…Yaushe zan zo in Ιauke ku?” Ya tambaya.
Wani guntun murmushi ya suΙuce a fuskarta ba shiri.
“Au ka fasa turo securityn su tafi damu? Ko ka manta ne kira na Ζarshe da kayi abinda kace kenan?”
“Lokacin raina a hasale yake, for god’s sake ta yaya zaki tsallake kasar nan har ki tafi U.S ban sani ba? Munzo kusan mu bakwai da freinds Ιina yi muku gaisuwa amma akace min wai ba kya nan, and I tried your line God knows how many times ban same ki ba, so yaya kike so reaction Ιina ya zama a lokacin dana same ki?”
Nadiya ta cije leΙΙenta, gaya mata yake yi yazo gaisuwar mahaifinta da iya abokansa su bakwai kawai, babu Ζ΄anuwansa ko Ιaya balle kuma uwa-uba iyayensa, kuma har dan bai same ta ba zai iya buΙe baki yayi Ζorafi bayan sai da akayi arba’in Ιin mutuwar sannan suka bar Ζasar, kuma bayan Ιan guntun text Ιin sa da ta gani a cikin wayarta bai Ζara waiwayar tata sai bayan arba’in Ιin, a idonta ta hango Ζ΄anuwan mijin Aisha yadda suka dinga sauka mota-mota har sai da aka share makoki, shi kansa mijin nata kwanansa biyu a garin.
Ta sani cewa yin Ζorafinta a wannan lokacin bashi da wani amfani, don ba sau Ιaya ba ba sau biyu ba yayi abubuwa makamancin waΙannan Ιin kuma maganarta bata canja komai ba, balle a yanzu da take jin zuciyarta na tsoron sake jangwalo wani abun da zai sa abubuwa suka Ζara Ιaci a tsakaninsu.3
A yanzu ta fara gajiya da wannan zaman da take yi, wata biyu an share makoki kowa ya tafi ya barta, Aisha ta koma gidanta tuni sannan Safina kuma ta koma makaranta, an gama dukkan wata hatsaniyar sarauta kuma duk yadda aka kai ruwa rana, duk wata fafutuka da Saifudeen Ζannen Mai martaba suka yi, sarauta ta kuΙuce daga gidansu.
Saifudeen bai samu sarautar ba, cin hanci da siyasa sunyi kaka-gida sunyi baΖe-bake ta kowanne Ιangaren masu zaΙen Sarkin, anyi amfani da karfin naira da kuma na siyasa an danΖa sarautar garin Kiyari ga zuri’ar gidan Auwalu Rumfa, babban jikan gidan mai suna Yakubu shi ya maye wajen zaman mai martaba, wani mutum mai Ζarancin addini da kuma son zuciya, don haka alhini ya Ζaru a zuciyoyin mutane ta yadda har bayan an share makokin arba’in jama’a basu bar jimami ba.
Kuma bayan an share makokin ne Saifudeen ya haΙa ta da wani cousin Ιinsu da yake waba wajenta mai suna Ashraf suka je har U.S kai Fulani asibiti, kuma har sun dawo anyi mata aikin gashi ta fara jin sauki ma don tun kafin su taho tana fahimtar dukkan wani abu da ake gaya mata har ma ta kanyi tambaya kan wasu abubuwa da suka faru a baya duk da maganarta bata fita sosai.
Satinsu uku acan yanzu kuma satinsu Ιaya da dawowa, amma har ta fara gajiya don duk da akwai mahidimta a Ιangaren ammad ba abinda take yi tunda suka dawo Ιin sai kula da Fulanin, don har yanzu ko hannunta bata iya Ιagawa, matsalar da aka magance a U.S ta ΖwaΖwalwarta ce kadai amma shanyewar jikinta na nan ba abinda ya canja duk kuwa da gashin Ζashin da ake mata safe da yamma.
Don haka a hankalinta san cewa wannan zaman ba shine mafi alkhairi a wajenta ba, sannan kuma ta lissafa taga cewa in har ta dage kan rabuwa da Abdallah a yanzu to ba Ζaramin kuskure zata yi ba don da kyar ne idan zata sake samun wani kamarsa saboda dame zata yi taΖama a yanzu? Uban da ya mutu? Sarautar da ba tasu ba? Ko Uwar da baza ta taba iya tsaya mata a komai na harkar rayuwa ba? Dama bayan muΖamin mahaifinsu, da Fulani suke takama wajen cewa itace Ζafarsu a ga duk wasu duk manya-manyan mutane na Ζasar nan, amma a yanzu da ita da babu banbanci kadan ne fon haka dame zata bugi Ζirji tace zata samu miji wanda yafi Abdallah? Yaro, kuma mai kuΙi da tashe irinsa? idan tayi sa’a wataΖila sai dai irin manyan alhazawan nan da suka tara Ιan kuΙinsu ta shiga a ta uku koma ta huΙu.
STORY CONTINUES BELOW
Wata rayuwa da bata jin zata taba iyawa, don ta sani cewa duk Ιacin ran da take fuskanta daga gurin Abdallah ko mahaifiyarsa, idan ta tuno kammaninsa da kuma dukiyarsa zuciyarta kan Ιan sarara da wani abun, aΖalla ko ba komai ta san zata ci mai kyau tasha ta kwanta a waje mai kyau. Shi yasa take ta lallashin zuciyarta da wata Ζarya mai ma’ana, Ζaryar xmr cewata da cewar ko ba komai yana sonta ko don Ζ΄ar data haifa masa.
Kuma ta yarda cewa wannan itace irin tata Ζaddarar rayuwar, tata jarabawar… dama ance sunan Ζaddadar guda Ιaya ne, sai dai siffofinta mabanbanta wanda ya danganta da rayuwar kowanne bawa.
Ita ga irin tata nan, don tun daga tasowarta a duniya, ta samu dukkan wani farin ciki da jin daΙi, bata taba neman komai ta rasa ba, sai a yanzu da Ζaddarar tata ta faΙa kan wani abu da yafi Ζarfin ikonta, rashin kulawar miji da kuma rashin soyayyar Ζ΄anuwansa.
“Baka gaya min ba, Mama ta yarda mu dawo Ιin ne?”
Taji alamun ya gyara kwanciyarsa daga cikin wayar sannan yace.
“Dama ranta ya Ιaci ne a ranar but komai ya wuce, har tace in miki gaisuwa ma.”
Sai ta haΙiye yawu a hankali tana jin wani Ιangare na zuciyarta na matsewa, ba zai taΙa ganin laifin mahaifiyarsa ba ta sani, amma ko mai rangwamen hankalin zai san wannan abinda ya faΙa bai dace ba, ta yaya za’ayi mata gaisuwar mahaifi ta wannan sigar? Sigar da sai itace ta tambaya ma.
“So, inzo Ιin ne ko in turo a Ιauke ku?”
A yanzu wannan abinda ya matse a zuciyarta ya wargaje don bata san me ya dace tace ba kuma, tunda al’amarin nan ya faru bai ko taba tambayar ya halin mahaifiyarta yake ba, sannan lokacin da yazo gaisuwar sun tafi kaita asibiti ko ita bai gani ba balle Fulanin, amma har yake tambayarta wai yazo? ita tata uwar ba komai bace a wajensa kenan tasa ce kawai mutum… Babu yadda zata yi sai kawai ta sunkuyar da kanta tana kallon yatsunta dake motsi akan rantsatstsen material Ιin dake jikinta, Ζwalla ta taru a idonta kafin tace.
“Duk wanda kaga yafi dacewa Abdallah.”
“Shikenan idan na sami dama cikin satin nan zan shigo, in kuma abubuwa sun riΖe ni zan turo driver kawai ya taho daku.”
Ance wai mai hankali ake gayawa magana har ya fahimci saΖon cikinta, don haka bata yi wani mamaki ba dashi bai fahimci shaguΙen cikin maganarta ba.
“Kince tayi bacci ko?”
Ta san wa yake nufi, Ζ΄arsa. Don ita kaΙaice halittar da take jin zai nema a rayuwarsa bayan mahaifiyarsa, itama kanta ta san albarkacinta take ci, don haka sai ta gyada kanta kamar yana ganinta kafin ta amsa.
“Eh taci abinci ne sai tayi bacci.”
Bakinta ya furta Ζaryar da bata yi wani hasashe a cikinta ba don bata ga dalilin da zai sa ta farantawa mutumin da bai damu da nata farin cikin ba.
“You’re sure kuma ba wani abu da ya same ta?”
“Lafiyarta Ζalau.”
“Okay, to sai kin ji ni kenan.”
“Insha Allah.”
Tana faΙin hakan ya kashe wayarsa Ιib, kuma ta san ita da ta sake jinsa wataΖila sai ranar da zai turo a Ιauke sun… Don ko zata kira shi ma in ya Ιauka yau ba lallai ya Ζara Ιauka gobe ba, don kamar sauran maza irinsa ya riga yasa a zuciyarsa cewa duk abinda zata yi masa don dukiyarsa ne kawai ba wai don wata kyautatawa ta daban ba.
Wayarta ta sake Ζara kafin ta tashi daga wajen, A’isha ce, ta Ιauka sannan ta kara a kunnenta.
“Yaya jikin Mama?”
A’ishan ta tambaya bayan sun gaisa.
“Da sauki, don har ta tambaye ki ma shekaranjiya.”
“Maganar tata ta fara fitowa sosai?”
STORY CONTINUES BELOW
“A’a, kamar da dai, amma ana ganewa.”
“Allah ya Ζara sauki, dama kira nayi inji har yanzu Abdallahn bai kira ki ba?”
Nadiya ta cije leΙΙenta daga gefe tana danne wani abu dake shirin tasowa a cikin ranta kafin ta faΙa mata wayar da suka gama yi yanzu dashi, sai dai ta canja kusan rabi na zancen ta kuma Ιoye abubuwa da yawa, amma duk da haka dai labarin ba mai gamsarwa bane.
“Allah ya sawwake Adda, nima ina ganin gwara ki koma Ιin, ko ba komai watarana zaki ci ribar haΖurinki.”
Nadiya ta gyada kanta.
“Insha Allah Ishsh, Allah zai dube mu, insha Allah. Kinyi magana da Muhammad Ιin?”
Kamar tana ganinta, Aisha ta girgiza kanta daga can Ιangaren.
“Har yanzu bai neme ni ba Addah, na gaya miki tunda na dawo baya ko bi ta kaina, yau kwana biyu kenan ma ban ganshi ba, kafin ya dawo nayi bacci, in dai zai fita kuwa yawanci har na gama shiryawa na shiga Cikin Gida, don haka bama haduwa kuma wallahi ni yafi min ma, don ko daga nesa na hango shi gabana sai ya faΙi.”
“Kar ki damu komai mai wucewa ne, atleast Ζ΄anuwansa na sonki don haka ki karΙi wannan ni’imar ma ki godewa Allah, wannan itace Ζaddarar rayuwarmu Ishsh, amma nayi imani watarana ni dake Ιin duk zamu ci ribar ko haΖurinmu insha Allah.”
“Insha Allah.” Aishan ta amsa kuma da haka suka yi sallama kowanne zuciyarsa a Ζulle.
Nadiya ta miΖe ta fita zuwa falo na farko daga nan cikin Ιakin, wani haΙaΙΙen falon Fulanin mai Ιauke da komai kalar maroon da gold, anan kan kujerar ta tadda Hidaya tayi barci da Ζ΄ar ledar chocolte Ιinta a hannu, ashe dai ba karya ta yiwa Abdallah ba, sai ta Ζarasa ta kashe makeken screen din plasma dake nuna tashar cartoon sannan ta dawo da Ιauke ta, ta kaita Ιakin Safina inda suke kwana yanzu ta canja mata kaya zuwa na barci sannan ta dauko wiper ta goge mata gefen bakinta da ya Ιaci da alawar, ta lulluΙe ta ta kashe fitilar Ιakin sannan ta fito.
Ta wuce duka sauran falukan da a yanzu suka zama tamkar kango saboda rashin mai zama a cikinsu har zuwa wani d’an karamin falo dake manne da turakar mahaifiyarta.
Hafsat Muhammad Gani (Fulani).
Dattijuwar mace ce da kallo Ιaya zaka yi mata daga nesa zuciyarka ta motsa saboda tausayin halin da take ciki, musamman in zaka ganta a lokacin da likitoci suka taru akanta ana aikin yi mata gashin Ζashi ta koina, sai zuciyarka ta matse har ka tuna ubangiji da dukkan irin ikon da yake zartarwa akan rayuwar kowanne bawa.
Tana kwance ne amma idanunta a tsaye suke ta kafe su tana kallon Ιanta Saifudeen wanda ke zaune a gabanta da labarin cewa zasu bar masarautar nan da sati guda su koma gidan mai Martaba na cikin GRA wanda yake sa rai cewa idan anzo raba gado zai faΙo wajensu.
A halin da ake ciki dukkan wani Ιangare na zuciyarta ya riga ya gama dagargajewa a Ζirjinta, tana jin Ζirjin nata ne fayau kamar Allah bai taΙa halittar komai a wajen ba don abubuwan da suka same ta da wanda ta gani da idanunta sunyi Ζarfin da zuciyarta ba zata iya Ιauka ba balle har ta iya fassara su a ranta, tun daga lokacin da hankalinta ya dawo har ta fahimci rasuwar mai martaba bayan ta Farouk Ιin da hankalinta ya gushe a cikinta, shikenan komai na cikin zuciyar tata ya mutu, ta zama bata da wani emotion ko na misΖala-zarratin, hatta shi kansa Ιakin cikin sai ta fahimci cewa wata rahama ce ta ubangiji ga bawa ya fuskance shi.
Tun bayan lokacin data fara fahimtar abubuwa a wannan asibitin na U.S da aka kaita, ta matsu da tambayar dukkan abinda ya faru don wanda zata iya tunawa kaΙan ne kafin gushewar hankalinta.
Ta san dama ance mata ta rasa aminiyarta jakadiya Babbba, ance mata ta mutu, ta tafi da duk wani buri da ta shafe rayuwarta tana gina shi, sannan akace mata ta rasa Ιanta kuma, Ιan da rabi na cikar burinta ya ta’allaΖa akansa… Bayan farkawarta kuma sai aka tabbatar mata da cewar ta rasa Mai martaba shima, ta rasa miji kuma uban Ζ΄aΖ΄anta, ta rasa wani ginshiΖi na rayuwarta, akace mata yau duniyar da take ciki babu Ahmad, babu wannan Ahmadun data so fiye da komai a rayuwarta kafin ruΙin shaidan yaci galaba akanta.13
STORY CONTINUES BELOW
Don haka halin da take ciki a yanzu ta tabbata babu wani abun awo a duniyar nan da za’a auna ya fitar da kalmar da zata fassara shi. Taci burika da yawa a rayuwarta, tun daga zamanin Ζuruciyarta, lokacin da Allah ya Ζaddara aurenta da mai martaba, tun daga wannan lokacin shaiΙan ya fara rinjayar zuciyarta na cewar tayi duk fafutukar da zata yi wajen ganin ta tarawa Ζ΄aΖ΄an da zata haifa tarin dukiya da kuma damar mulki ta yadda har bayan Ιaruruwan shekaru sunanta da nasu ba zai goge a tarihi ba, a ganinta wannan shine ribar zuwa duniyar ba ka tafi a manta da kai ba.
Kuma mahaifiyarta ita ta fara Ιora ta kan turbar bin malamai tun tana sane da cewa hakan ba daidai bane har tazo ta manta dukkan wani fatanta ya ta’allaΖa a gare su, musamman da Madaki ya zama Ζalubale a cikin rayuwarta. Hakan yasa ta ture komai gefe hatta tarbiyyar Ζ΄aΖ΄anta da kuma soyayyar da take wa mijinta, ya zama fufutukar bin bokaye shine abu mafi muhimmanci a wajenta.
Wata fafutuka da ko ta sami nasara akan wani abun sai wata matsalar da ta fi shi kuma ta Ιullo don haka sai ta zama kamar mai hakan rijiya….. Tana girma tana Ζara mu’amalantar mutanen dake yin abinda yafi nata wanda hakan yasa zuciyarta ta Ζara ΖeΖashewa kuma bata taΙa hango rashin dacewar abinda take yi ba balle har ta fahimci talalar da rayuwa ke mata. Sai da komai yazo Ζarshe tukunna sannan a yanzu ta afka cikin ramin nadama wanda ta kira da mara amfani.
Kuma mafi ciwon abun shine rashin lafiyarta a yanzu, ta kan kasa yarda a duk lokacin da ta kalla taga cewar wai yau mace kamar ita, FULANI! itace kwance jiki a shanye maganarta bata ko fita kuma babu wani abu da zai tayar da ita sai Allah, ubangijin dai data juyawa baya tun farko. Duk waΙannan tarin kuΙin data Ζallafa rai akansu da bokayen da ta shafe rayuwarta tana bautawa basu da Ζarfin ikon yi mata komai a yanzu, hatta tarin Ζawayenta manyan mata irinta da take taΖama dasu, Nadiya ta shaida mata ba kowa ne ma yazo dubata ba balle har ayi mata ta’aziyyar Ιa da kuma mijin data rasa.
Sannan mafi rincabewar al’amarin a yanzu gidan sarautar ma yafi Ζarfinsu, duk tsawon shekarun data Ιauka tana zuba mulki a cikinsa a yau ya koma tamkar ba’ayi ba, lokaci ya wuce da damar da ta shagaltar a banza kuma babu mai ikon canja komai, dole ne su fita su bawa masu zamani waje suma su taka tasu rawar.
Madakin dai da ta shafe rayuwarta tana ΖoΖarin ganin bayansa a yanzu shi kaΙai ne ya sami dukkan wani alkhairi don ko ba’a gaya mata ba ta san cewa wannan auren nasa da ta zama sanadiyyarsa ya gyara rayuwarsa ta Ιangare da za’a iya cewa bayan rasuwar Mai martaba a yanzu, shi bashi da wani aibu a tasa rayuwar, don ta ganshi kafin ya tafi, yazo ya dubata duk da a lokacin bata cikin haiyacinta sosai.
Kuma Saifudeen ya shaida mata cewar shi ya samo asibitin da aka kaita a U.S har ta sami rangwamen sauΖi a yanzu, sai dai duk da haka zuciyarta bata ganin farinsa har yanzu, zuciyarta ta riga ta gama mannewa da tsanarsa tun asali don haka ba abinda zai taΙa canjawa duk da irin nadamar da take ciki a yanzu. Don a tunaninta ma ba don shi ba, ba lallai ta dore wajen bin bokaye ba har ta sami wannan nakasar, sannan dukiyar da yake amfani da ita a yanzu wajen kula da ita ai ba tasa bace ta mijinta ce kuma uban Ζ΄aΖ΄anta, don haka babu wani abin birgewa da yayi a wajenta.
Tana jin ma da Allah zai iya Ζaddarawa ta miΖe, zata iya cigaba da neman kassara Madaki ta wata hanya daban bata bin bokayen da a yanzu taga cewa bata Ιullewa ba…3
(Allah ya kiyashe mu daga sharrin zuciya, dama haka yake, ance wasu ko zasu je lahira su dawo halinsu ba zai taΙa canjawa ba don shi Ιin zanen dutse ne.)7
***
08:19AM
Lagos.
Gidan Mubarak.
“Mubarak? King?… Sarki?”
Muryar Khadija ta kira duka sunaye ukun a lokacin sa ta durΖusa a gaban Mubarak tana kallon fuskarsa, idanunsa ba ita suke kallo ba, hange yake ta saman kafaΙarta cikin zurfin tunanin da a kwana biyu yake yini yana tashi dashi.
STORY CONTINUES BELOW
“Ya akayi wai?”
Muryarsa ta tambaya ba tare da ya kalle ta ba.
Sai ta miΖo hannunta ta tallafo fuskarsa ko ta wane Ιangare.
“Ka kalle ni mana…”
Ba musu ya dawo da idon nasa ya kalle ta.
“Bani da lafiya naje asibiti.” Ta faΙa kai tsaye don ta san in ta tsaya jan zancen tsaf zai iya tashi ya tafi wani abun.
“Really?… Ya akayi ban sani ba?”
“Ζazu da safe da naje kai su Aliyu makaranta na tsaya asibitin nan na gefen makarantarsu.”
Sai ya gyaΙa kansa alamun yana saurarenta.
“So, anyi min test ance wai…”
“Wai me?”
A lokaci guda yanayin fuskarta ya canja zuwa tsantsar farin ciki, ta sake sirranta muryarta sannan cikin Ιan ihu tace.
“We’re going to have a baby!”3
(Zamu samu Ζarin baby!)
“Da gaske kike Yaarym? Da gaske?”
Shima ya tambaya murmushi na haskawa har a idanunsa.
“Wallahi, sunce wai 5 weeks.”
Sai ya riko hannayenta duka biyun ya ratsa yatsunsa a tsakani.
“Ya Allah! I’m so happy, wallahi nayi farin ciki sosai, shekara nawa kenan? Shekarar Hanan nawa?”
“Shida.” Ta faΙa da dukkan farin cikinta itama.
Sai ya rufe idanunsa ya buΙe sannan a hankali ya furta kalmar.
“Alhamdlilah.”
Daidai lokacin kuwa da wayarsa dake gefen gadon ta shiga Ζara, ba shiri ya saki hannayenta ya Ιauki wayar kuma sunan da ya gani a jiki yasa wani bari na zuciyarsa lafawa. Sai dai kafin ya Ιaga ya juyo ya kalli Khadijan yace.
“Ina Salwa?”
Mamaki ya Ιan kama Khadijan, me yasa zai tambaye ta? Bayan ya san cewa fiye da wata guda tun bayan da ya dawo da ita daga gidan kangararrun da yasa aka tsare ta zamanta baya wuce cikin Ιakinta sai kuma Ιan Ζaramin falon su Hanan da Tvn ciki ba abinda take nunawa illa tashoshin Cartoon. Amma sanin yadda halinsa yake a cikin Ζ΄an kwanakin nan yasa ta ture mamakin tace.
“Tana Ιaki.”
“Kice ta saka hijabinta ta fito main falo yanzu zata yi baΖo.”
Ba shiri mamakin kan fuskar tata ya dawo har ma yafi na da kafin tace.
“Bako? Salwan? Daga ina?”
“Zan miki bayani anjima, for now just let her know.”
(Zan miki bayani anjima, a yanzu ki sanar da ita tukunna.)
Kuma da haka ya nemi hanyar Ζofa ya fice, takunsa akan tiles Ιin mai Ζarfi kamar yadda zuciyarsa take da Ζarfi da kuma yaΖini akan abinda yake shirin aiwatarwa. Ya wuce main falon nasu ya bude Ζofar waje ya fita,a compound Ιin wata mota ce ke haska kyallinta cikin hasken fitilun wajen.
Kuma ya Ζarasa sai Ζodar mazaunin direba ta buΙe kuma tar idanunsa suka hasko masa wanda ya fito daga ciki.
Habibu.
“Ranka ya dade Barka da fitowa, ai nazo tun Ιazu ina ta gwada wayarka network yaΖi signaling, sai yanzu na samu.”
“Ba komai, ka Ζarasa duba takardun LAT?”
“Eh, and I came across some errors, amma na kusa Ζarasa su ma Insha Allah.”
Sai Mubarak Ιin ya gyada kansa.
STORY CONTINUES BELOW
“Dont rush, ai muna da isashshen lokaci.”
“Insha Allah.” Cewar Habibun yana Ιan sunkuyar da kansa kamar mara gaskiya.
“Mu Ζarasa ciki, yanzu zata fito.”
Saura kaΙan Habibu ya sake buΙe bakinsa ya tambaya cewa wai da gaske Mubarak Ιin yake har yanzu babu wasu sharaΙai da zai gindaya masa a wannan al’amarin? Don tunda ya same shi sati biyu da suka wuce da zancen daya faranta ransa kuma ya bashi mamaki har yanzu bai bar tunanin cewa zai kafa masa wasu sharaΙai akan al’amarin ba.
Cewa yayi wai yana neman alfarmar daya auri Ζanwarsa, zai bashi gida sannan zai sa hannu Madaki ya kara masa muΖami a kamfaninsu. Kuma bayan hakan babu wani sharaΙin abinda zai yi kawai abinda yake so shine ya auri kanwar tasa, sai dai ya gaya masa komai game da ita, rashin jinta har ma da irin mutanen data mu’amalanta kafin ta dawo wajensa, kuma shi wannan ba matsalarsa bace don duk Ζ΄anmatansa ma irin halayyarsu kenan, kuma in dai yana tare dasu to cikin sassauΖan mataki yake raba su da kowa ya zama in bashi Ιin ba babu maganar wanda suka isa su saurara.
Don haka kamar an kawo kuka gidan mutuwa ne, komai taurin kan wannan Salwar ya san cewa ya buga da wanda suka fita kuma ba zai canja tsarinsa ba akanta, in ma mutuwa zata yi shi ba ruwansa indai har ya riga ya sami gida da Ζarin muΖaminsa, ba dai neman kai ake da ita ba? To tabbas kuwa an kawo ta daidai wajen daya dace. Yasa hannu ya danne button Ιin wayarsa dake vibrating alamun shigowar kiran Lulu, ya kaΙa kansa sannan yayi murmushi a fili kafin yabi bayan Mubarak da yayi gaba, ya riga ya gama da wata Lulu kuma a yanzu filin na Salwa ne kafin yaci moriyar ganga…2
Salwa ta kalli cikin idanun Khadija a lokacin da take faΙa mata saΖon Mubarak, kuma bata yi mamaki ko kaΙan ba balle har ya kai na Khadijan da take gani a fuskarta, dama ai ta riga ta sani ta san cewa dole akwai abinda Mubarak ke shirya mata shi yasa itama ta biye masa suka yi wannan wasan tare, don ta riga ta tsara cewa zata nuna masa cewa da gaske tayi nadama irin nadamar da yake son gani a tattare da ita, Allah barshi duk ranar da zuciyarsa ta bashi tabbaci ko yaya ne game da ita, sai ta samu Ζ΄ancin da zata Ιalle zuwa inda zata kafa sabuwar duniyarta.7
Don a yanzu zuciyarta ta riga ta gama haΖura da Madaki, ba don ta daina sonsa ba sai don ta san in har ta dage sai shi Ιin, to zata yi biyu babu ne, babu shi Ιin kuma rayuwarta ba zata taΙa tafiya a yadda take so ba.
WataΖila kuma ta taka rawar tata da kyau, tunda gashi har ya yanke shawarar yi mata aure a tunaninsa cewa ta shiryu, don haka suje zuwa, ai auren ma shine hanya mafi sauΖi ga Ζudirinta da take son cimmawa, ta hanyarsa zata samarwa kanta Ζ΄ancin da in ta tafi baza su sake ganinta ba kuma har abada, don haka ko waye ya kawo zata yarda ta aure shin kafin taci moriyar ganga… ta yar da kaurenta!4
***
#Majid
Washegari, Lahadi.
08:10Am.3
“Kana nufin shima Habibun ya yarda zai aure ta?”
Madaki ya tambaya ta cikin wayar da yake yi a safiyar ranar lahadi, yayin da yake kishingiΙe kan kujerar tsakiya ta falonsa, falon da har yanzu ke bada sassanyan Ζamshin turaren da Jidda ta baΙe gidan dashi a jiya, don babu wanda ya sakta taje ta Ζona busashshen Ιawon lemon da ta dade tana tarawa wai maganin sauro ne, da koina a gidan ya baΙe da Ζauri kuwa ba shiri ta kunna turaren wuta ya bi ta kansa.
“Yes, nasa yazo gidan jiya sun gaisa kuma daga shi har ita kowa ya tabbatar min cewa ya zai zauna da Ιaya.”
Muryar Mubarak ta amsa ta cikin wayar.
“Habibu is like family to us, amma kai kanka Mubarak ka san halinsa da gyara, so I wish wani daban ka samo mata bashi ba ko don Ζ΄aΖ΄an da zata iya haifa dashi.”
“Mdee ka yarda dani, na riga na auna komai na san me nake yi, Habibu shine daidai da Salwa, idan har na samo mata akasinsa kamar na bata Ζofa ne da zata cigaba da halayenta don wallahi har yanzu bata yi nadama ba, ina ganin hakan Ζarara a idanunta, so kamar yadda hausawa suka ce ne Ιan birni shine maganin Ζ΄an birni, na san idan har zan riΖe Habibu da wasu alΖawuran to ba zai taΙa bata wata Ζofar da zata yi wani abu ba. Beleive me.”
STORY CONTINUES BELOW
Madaki ya gyada kansa kafin a hankali yace.
“Allah yasa hakan shine mafi alkhairi, amma please kar ka cigaba da takurawa yarinyar nan Mubarak, atleast ka san mata da biki, ka barta tayi abinda take so in har zancen auren ya tabbata.”
Mubarak bai amsa ba don ba zai amsa abinda ba zai iya ba, ya riga ya tsara komai a cikin kansa cewar daya sanyo magabata a cikin maganar, a rana Ιaya za’a Ιaura auren ba wani taro, ko mutum shida ne sun isa wakilci, kuma duk tarin Ζ΄anuwansu wasu gwaggoninsu guda biyu kawai zai sa su kaita gidanta a ranar, babu wani taro balle ma a saka ran dafa ko Ζwayar shinkafa da sunan murna.
Saboda haka sai kawai ya juya akalar zancen nasu ga fafutukar da suke ciki a yanzu na ΖoΖarin ware dukkan wata riba da kamfanin Royal K ya samu daga lokacin da aka fara tara ribar zuwa yanzu saboda harkar rabon gadon Mai martaba da za’a fara wani watan.
Babu yadda Mubarak baiyi ba da farko akan cewa su haΙa kudi su biyu koda kuwa sai sun hada da wani ne su siya kamfanin ya koma nasu gabaΙaya amma fafur Madakin yaΖi, sai da ya matsa ne sannan ya fit masa wata tsohuwar takardar wani agreement da Mai martaban ya taΙa rubutuwa cewa ko bayan ransa bai yarda a haΙa kamfanin cikin gadonsa ba ko kuma a saida shi ga wani saboda kudi, ya rubuta cewa ko naira biyar kaΙai ake samu daga cikinsa yana son wannan kuΙin ya zama abu guda Ιaya da zai cigaba da haΙa kan Ζ΄aΖ΄ansa ya zama akwai dai wani abu da ya haΙa su ba kowa an bashi gadonsa ba ya kama gabansa.
Don haka wannan takardar da sa hannun Sarkin da komai ita zai gabatar ga masu rabon gadon in an tashi sai kuma zunzurutun kudin ribar kamfanin da aka tara don a fara raba musu kafin zagayowar kowacce shekara kuma ya dinga kawowa akai-akai. Kuma yayi alkawarin cigaba da aiki a kamfanin iya tsawon ransa in har ba Saifudeen da yake babba a yanzu ne yayi niyyar canja shi ba. Don ya yarda cewa babu wani aiki da zaiyi a duniya wanda yafi ya cigaba da raya kamfanin mahaifinsa kamar yadda ya Ιora shi akai tun farko, kuma ya yarda cewa babu wani kuΙi da zai samu wanda zasu fi albashinsa daga wannan kamfanin albarka, don iya albashin da yake samu ya san zai ishe shi tsawon rayuwar da zai shafe tare da Jidda har ma da Ζ΄aΖ΄an da zasu haifa nan gaba.
Kuma a haka wayar tasu da Mubarak ta Ζare, dama ya kira shi ne kan wani code da yake son ya karΙa na kayansu da suka iso daga tashar shige da ficen jirgin ruwa ta ikkon.
Madaki ya bar wayarsa anan falo sannan ya koma daki, Ζafafunsa na taka tiles Ιin Ιakin a hankali don kar ya tashi Jidda dake bacci duΖunΖune cikin bargon gadonsa, dama kiran wayar Mubarak Ιin ne ya fito dashi falo don kar ya tashe ta. Sai dai yana shiga cikin bargon kuwa ta buΙe idanunta.
“Ζarfe nawa?” Muryarta ta tambaya a lokaci guda
Ya san tunani take cikin sati ne, kar lokaci ya Ζure mata bata tashi ta haΙa masa breakfast ba don haka maimakon ya amsa mata sai kawai yasa duka hannayensa ya janyo ta jikinsa a hankali sannan yace.
“Bamu tashi ba, go back to your sleep.” (Ki koma baccinki).
“Ka gaya min time Ιin tukunna.” Muryarta ta sake fitowa a hankali daga jikinsa, sai ya sunkuyo da fuskarsa daidai saman kanta yadda zata fi jinsa yace.
“Ζarfe Lahadi, daidai lokacin da ya kamata ace kina jikina, so dan Allah kar ki tashi kin san gobe i-yanzu ba zan sami wannan damar ba.”
Jidda bata gama wartsakewa ba amma duk da haka ta shiga jin sak irin abinda taji a lokacin da ya fara gaya mata cewa yana sonta a masaukinsa na Kiyari, kuma irin abinda take ji a duk lokacin da ya furta mata wata maganar da tayi wa zuciyarta daΙi, wai yaushe zata saba ne?
Sai ta Ιago da kanta ta kalle shi, muryarta a hankali can Ζasa ta sake cewa.
“Na san weekend ne, amma duk da haka zamu ci abinci ai ko?”
STORY CONTINUES BELOW
Ya girgiza kai yana kallonta kafin yasa hannunsa ya maida kanta ta kwanta.
“Ki koma baccinki Jay, idan mun fara jin yunwar zan tashe ki.”
Ta san abinda yasa ya damu da kar ta tashin, tunanin gajiyar da tayi yake na aikin data sha jiya wajen haΙawa Jamila wasu Ζ΄an Ζananan jakunkunan data gano a kasuwa wanda zata rabawa Ζawayenta da biki, suna da kyau sosai amma basu da zip a jiki saboda haka da tayi tunanin zasu fi kyau da zip Ιin sai tasa ya bawa Baba Saminu ya siyo mata zips Ιin a kasuwa tare da gum Ιin da zata manna, kuma da yake suna da yawa sai ta Ιauki lokaci tana yi har sai da hannun nata ya Ζage.
Don haka bata sake cewa komai ba sai ta Ζara gyara kwanciyarta akan Ζirjin nasa yayin da yatsanta Ιaya ya shiga bi a hankali kan adon zaren jallabiyarsa, zuwa wani Ιan lokaci kuwa baccin ya sake Ιaukarta yayin da shi kuma ya jawo tab Ιinsa ya shiga dube-duben ayyukansa da ya saba.
Kuma ba ita ta sake farkawa sai wajen Ζarfe sha Ιaya saura na safen, a lokacin ita kaΙai ce a gadon sai sharar baccinta take Ιin haka ba shiri ta tashi ta fito falo inda daga nan ta tagar falon ta hango shi daga can compound yana ta faman fito da wasu takardu daga bayan motarsa yana Ιorasu a saman motar yayin da yake waya. Kayan jikin sa wannan sealed Ιinkin ne na maza, ta fahimci kusan duka kayansa haka suke kuma cikin kalolin da basu fi guda biyar ba, amma he looks perfect, style Ιin ya karΙe shi tare da yanayin jikinsa, baya buΖatar wani abu daban kuma don ya Ζara haiba da kwajininsa. A cikin ranta ta godewa Allah ta sake gode masa da baiwar da yayi mata, don a yanzu Madaki ya cike kowanne gurbi na zuciyarta ta yadda take ganin kome zaiyi mata ba zata taΙa tsanarsa ba.
A cikin wata biyu kawai ya haskaka rayuwarta da wata irin kyautatawa da kuma Ζaunar da bata taba hangowa kanta ba, tana jin kamar ko zai zo daga baya ya Ζwace komai nasa, zuciyarta baza ta taba manta wannan farin cikin ba da kuma irin feelings Ιin daya haddasa a ranta.
Kuma kamar yadda ya sake cika mata kitchen da kayan abinci haka kayan sawa ma a yanzu har ta kan manta ranar data sa wasu, kowanne cikin ra’ayinta don yawanci stores suke zuwa tare ta zaΙo wanda take so, me Baddo tace mata ne wai?… In ta karΙi Ζaddararta hannu biyu ita zata fi kowa amfana da hakan…
Har ta gama tsaiwarta a falon nan tana kallonsa bai juyo ba, waya kawai yake yi yana faman bankaΙa takardu, kuma ta san ba zai wuce harkar kamfani da kuma rabon gadon Mai martaba da yace mata ana shirin yi ba. Don haka ta juya Ζafafunta ta shiga harkokinta, tayi wanka sannan ta tafi Kitchen koΖarin hada musu breakfast tunda gidan babu shara.
Kuma sanda ta gama soya doya da sauce Ιin kwan da tayi shima a lokacin ya gama gama wayar ya shigo ciki, har yana ΖoΖarin kunna Tvn falon da ita bata taΙa damunta ba ko sanda take shan zamanta ita kaΙai balle a yanzu da tayi waya ma, don ita yanzu hankalinta gabaΙaya ya ta’allaΖa ne akan haΙaΙΙiyar wayar daya bata ba Tv ba.
Kuma wannan itace sabuwar rayuwar da suke shimfiΙawa a gidansu tsawon watanni biyu, akwai shaΖuwa da fahimtar juna sosai a tsakaninsu, a yanzu ya san duk wani tarihinta kuma itama ta san nasa don Jidda wata irin mutum ce open-minded, duk abinda ke ranta zata faΙe shi kai tsaye ne sai dai in har yayi nauyi sai ta san yadda zata sakaya shi cikin magana, yayin da Madakin yake mai tsananin kulawa da appreciation kan dukkan kulawarta gare shi, tunda wani abu ne da bai taΙa samu ba, bai ma san yaya yake ba don haka zuciyarsa cikin Ιokin hakan take da kuma ΖoΖarin gujewa duk wani abinda zai dame ta balle har a iya samun akasi.
Idan ranakun weekend ne ba inda yake fita sai masallaci ko kuma in har zasu fitan ma to zai Ιauke ta ne suje zagaya gari tare, saboda ko gidan Mubarak sau Ιaya ya taba kaita bayan ita da Khadijan sun dame shi da Ζorafi tunda ita dasu Hanan suna yawan zuwa wani lokacin daga makaranta ma zasu tsaya, kuma shima baya son zuwan nata ne saboda Salwa duk da cewar bama su haΙu ba sanda taje Ιin don bata fito daga Ιakinta bar ya dawo ya Ιauke ta, kuma ko shi da ya nemi ganinta Ζiri-Ζiri Mubarak Ιin kallonsa yayi yace ‘A’a’.
STORY CONTINUES BELOW
Idan ranakun aiki ne kuma ya kan shafe rabin aikinsa yana duba lokaci don jiran la’asar tayi ya koma gida, a yanzu ya yarda cewa cikar farin cikin kowanne namiji a duniyar nan shine bayan fafutukar neman halalinsa ya koma gida ya tarar da matarsa cikin kyakkyawan hali tayi kwalliya tana jiransa, a gefe daddaΙan abincin da hannunta ya tanada masa sannan a cikin idonta labarin kewarsa kala-kala. Watarana ma sai ya kasance har da Ιansu rike a hannunta, watakila ma biyu ko uku…
In yayi wannan tunanin sai yayi tsaki a ransa, yaga wautarsa a fili sanda Mubarak ke roΖonsa da cewar yayi aure tuna lokacin amma yaΖi… Sai dai da yayin fa? Zai samu Jidda ne?
***
November, 19.
“Sati Ιaya ko?”
Jidda ta tambaya a lokacin da ta tsugunna a gaban Madaki ta miΖo masa kunun farar shinkafar data yi tun safe ta ajiye a flask, yanayin garin irin na sanyi ne daya fara shigowa amma baiyi yawa can sosai ba, don haka sun saki labulayen gidan gabaΙaya harda na kuma koina an kunna fitulu, Tv na nuna tashar films Ιin holywood yayin da ake wani film mai taken ‘Little Women’, kuma in banda sassanyan Ζamshin Air freshner dana turaren wuta ba abinda ke tashi a iska sai ko na Ζamshin sababbin kujerun da suka sake a falon.
Madaki ya Ιago ya kalle ta daga kan screen Ιin MacBook Ιin dake gabansa inda a gefenta ya baza tarin takardunsa.
“Sati Ιaya a me?” Ya tambaya a hankali da Ιan guntun murmushi a gefen leΙΙensa yayin da idanunsa ke kallon kayan jikinta da taje ta sake bayan doguwar rigar atamfar da ta saka tun safe, wani wando ne fari da bai kai har karshen Ζafarta ba, sannan Ζasansa yayi beza ne gabadaya kamar an saka almakashi an yayyanka shi, rigar jikinta kuma lemon green ce mai hannun vest, tana da tsawo ta baya amma ta gaba bata Ζarasa ma cinyarta ba. Kanta babu Ιankwali don a yanzu ya riga saba mata da rashinsa, in dai yana gida da ta saka ma Ζ΄an mintuna ne zai cire shi, sannan bata yin kitso ma, yafi son a koyaushe ya zura hannunsa ciki ya tsefe tsawonsa.
Ta gyara zamanta a gabansa sannan ta kai kofin nata kunun baki kafin tace.
“In munje Kiyari nake nufi zamu yi sati Ιaya? Kaga kaima zaka yi naka fafutukar rabon gadon nan.”
“Who told you? Ni ba abinda zanyi, zan basu takarda ne kawai su gani, kuma da sun yarda shikenan na gana komai, idan naje na gaishe da Hajja, kinga kenan ko washegari in kin gama sai mu ta taho.”
Ba shiri ta haΙiye ragowar kunun dake bakinta.
“Washegari? Haba mana, bikin Jamila ne fa, duk shirin dana daΙe ina yi?… Ko Baddo ai baza taji dadi ba kawai in kwana Ιaya in tafi, bayan ba’ayi komai da bikina ba.”
Tsakaninta da Allah ta fadi maganar ba tare da sanin tasirin da tayi a zuciyar Madaki ba, don kallonta yayi na Ιan wucewar sakanni biyu kafin ya ture labtop Ιin dake gabansa a hankali zuwa gefe sannan ya kamo hannunta ya jawo ta jikinsa sannan kamar koyaushe ya haΙa fuskokinsu waje Ιaya.
“Idan taro kike so Jay, ki bari duk ranar da Allah ya bamu baby, zan haΙa miki shi har sai kin ce min ya ishe ki…”
Yayi shiru yana kallon gashin idanunta dake kallon Ζasa kafin muryarsa ta sake fitowa. Yana son wannan Ζ΄ar kunyar tata ko kuma yadda take nuna masa cewa yana da effect akanta, don har yanzu ko taΙa ta yayi zai ji sanda zata Ιan zuki numfaahi ko kuma jikinta yayi rawa kaΙan.
“… Ko kuma mu haΙa kawai ma yanzu, sai mu samo reason Ιin da zamu gaya mutane in mun gaiyace su?”
Sai ta Ιago idonta ta kalle shi.
“Muce me?”
Ya Ιaga kafaΙunsa har tata fuskar ta motsa.
“Ko muce musu bamu yi komai da aurenmu ba, ko shaddar Ιaurin aure ban saka ba sannan kema ko Ιan gwaggwaron nan ba’a Ιaura miki ba.”1
STORY CONTINUES BELOW
Ba shiri murmushi ya suΙuce a leΙΙenta, murmushi kamar dariya ma kafin tace.
“Cewa zasu yi bamu da hankali…”4
Madaki bai san sanda yayi murmushin ba shima kafin yace.
“I dont care Jay, in dai zai sa ki daina tunanin wani abu game da aurenmu wallahi zan iya yi.”
Sai ta girgiza kanta.
“Bana tunanin komai, ban taba tunani komai ba Allah, na faΙa ne kawai don ka barni in kwana da yawa.”
Sai ya sake yin murmushi yana riΖo hannunta dake zagaye da kofin kunun sannan yace.
“Kar ki damu zaki kwana iya son ranki, saboda dama ni da Saifudeen zamu kai Fulani Kaduna wajen wani mai magani, so asha biki lafiya.”
A take Jidda ta dawo da murmushin kan fuskarta harma yafi na da sannan tace.
“Inshallah. Allah ya kaiku lafiya, Allah ya dawo daku lafiya, nagode sosai.”
“Ameen.”
Ya furta a hankali sannan ya riΖo fuskarta da hannunsa Ιaya.
“Sai dai nafi son Ιayan Jay, wannan addu’ar ina samunta daga dubunnan mutane, shi kuma Ιayan naki ne ke kadai.”
Ta san me yake nufi, don haka ta rufe idanunta da sauri yayin da wannan abin data saba dashi ya shiga ratsawa cikin jijiyoyinta kafin muryarta ta fito tar daga maΖogwaronta.
“I love you.”
“Say it again..” (Ki sake faΙa.)
“I love you.”
“Again…” (Ki Ζara.)
“I love you…”
“Again…”
“I love you so much Em. I love you, wallahi ina sonka da gaske!”
Madaki yayi wani irin murmushi mai zurfi daya taΙo har wani Ιangare na can cikin zuciyarsa kafin a hankali ya haΙe tazarar dake tsakaninsu.
Wani Ιari na zuciyarsa ya furta addu’ar…
Nagode da sabon fatan saka bani a rayuwata ya Allah…!
*
#FashinBaΖi.
Ansha sha’anin bikin Jamila da angonta Sulaiman a daidai lokacin da ubangiji ya riga ya kaddara faruwarsa…
Anyi auren Salwa da Habibu, kuma Ζuddirin kowannensu ya rushe a lokacin da zaman aure yasa su duka suka fahimci cewa ba kowacce ganga ce ake gama cin moriyarta a rayuwa ba balle har ayi tunanin yar da kaurenta, rahama da alkhairin aure yasa kowannensu ya sauka daga sharrin zuciyarsa sun zamewa junansu sanadin gyaruwar Ζaddarar rayuwarsu…
Saifudeen ya ajiye sarautar Turaki, ya buΙe katafaren kamfanin tsarin gine-gine (Architecture) abinda ya karanta a makaranta, alaΖarsa da Madaki ta inganta ta sanadin sanin abubuwan dake gudana a kamfanin Royal K, sannan ya auri wata cousin Ιin kishiyar mahaifiyarsa (Nene Hadiza) wata Ζaddara da inda Fulani na kan ganinyarta, faruwarta zai zama tamkar a mafarki…
Nadiya da Aisha sun cigaba da zaman haΖuri a gidan mazajensu, ga dai kuΙi fal amma babu isashshen farin ciki, yayin da autarsu Safina ta gama makaranta kuma samuwar miji yayi wuya a wajenta, Ζaddararsu rayuwarsu ta faru ne da taimakon halin mahaifiyarsu…
Jidda ta cika burinta akan Suraj (saurayinta na farko) lokacin bikin Jamila ta haΙu da yarinyar da yake so har cikin zuciyarsa, watakila kwatankwacin yadda taso shi itama kafin ya nemi Ιata rayuwarta, kuma tunda tasa yarinyar nan a kwana ta shiga fallasa mata duk munanan halayensa da ita yake Ιoye mata, bata Ζyale ta ba sai da ta tabbatar cewar ko yarinyar nan ba zata zage shi ba in ya sake zuwa wajenta to tsaf zata iya yi masa korar kare….
Fulani ta rasu da shekaru biyu bayan faruwar duk wadannan abubuwan, bayan Saifudeen da Madaki sun sha mutuΖar Ιawainiya da ita gurin yawon nema mata sauki a cikin shekarun, wasu shekaru data shafe cikin jinya da kuma tarin nadamar da bata da amfani, irin nadamar da ubangiji baya karΙa, tata Ζaddarar kenan…
Kuma kamar yadda rayuwar kowanne bawa bata taΙa cika goma cif-cif ba, haka ciwon zuciyar Madaki bai taΙa warkewa ba sai dai samun sauΖi, sannan bai taΙa samun iyaye ko danginsa ba, amma ya samu mafi alkhairin arziΖin da kowanne namiji ke bukata a rayuwarsa, ya samu mace ta gari da bata da burin komai illa ganin ta faranta masa, macen da ta CIKE DUKKAN WANI GURBI da ya taΙa kasancewa mai zurfi a rayuwarsa sannan macen da Ζaddara ta mallaka masa ita…4
Don me akace ne?
Ζaddara tana da tarin ma’anoni a duniyar nan, kuma bayan fuskar da aka santa da ita, tana iya Ιaukar siffar alkhairi ma….
Sauran rayuwar MAJID kuma, na barwa tunaninku….!3
Tamat bihamdillah!
Alhamdlilah Alhamdlilah.
Ina fatan Allah ya hada mu a ladan alkhairin dake cikin littafin nan sannan yayi min gafara a kuskuren dake cikinsa.
Post a Comment for "ZANEN DUTSE CHAPTER 7 KARSHE BY AISHA-SHAFIEE"