YARIMA MUS'AB CHAPTER 6 KARSHE YARIMA MUS’AB CHAPTER 6 KARSHE Www.bankinhausanovels.com.ng Washegari girke² akeyi tamkar ana biki a gidan Abbu kowa na gidan yazo duka ‘ya’yan Ummy mata guda biyu Aunty Maryama da Adda Khadija hatta Mai martaba sanda yaxo ya gaida Malam tare da masa godia sosai kan rike kanwarsu da yayi shima ya zama kamar dan uwa Inna kuwa suna tare da Mama Muniba an kulla kawancen tsofoffi bayan anci abinci nan aka tarasu kan maganar auren yaran tunda kowa yana nan harda Baffa Auwalu sai a nan Ammi take jin cewa ashe akwai maganar aure tsakanin Yarima da Hafsat taso tayi gardama kan maganar Mami amma Malam ya tsawatar yace “Kul Fatima Allah bai haramta ba”+ Nan Mus’ab ya gabatar da kudirin da ya dade da kudirtawa a ransa ya dubi Abba Sadiq yace “Abba na daman dalilin hada zumunci kuke son hadani aure da Hafsa ko” Suka ce Eh yayi murmushi “to Hafsa dai bata so na amman ta karbi zabinku sbd biyayya amman indai sbd zumunci kuke son hadamu to baza’a fasa ba don wani zumuncin ne zai hadu…