YAR LEKEN ASIRI CHAPTER 9 BY ANUP JANYAU (_SPY_?)

YAR LEKEN ASIRI CHAPTER 9 BY ANUP JANYAU (_SPY_?)
YAR LEKEN ASIRI CHAPTER 9 BY ANUP JANYAU (_SPY_?)                  Www.bankinhausanovels.com.ng  Tun bayan kammala sallar asubah Kuzeem bata koma bacci ba, ta duk’ufa aiki a system d’inta wanda ya d’auketa tsawon wani lokaci, daga baya ta buge da online shopping inda tayi siyayya me yawan gaske, don dama ita tana daga cikin mutanen da suka yarda da online shopping saboda yafi musu sauk’i, musamman ma ita da batada wani lokacin kanta, saida ta kammala komai kana taje tayi wanka ta shirya cikin wata blue gown, mai masifar kyau da tsada, tare da feshe jikinta da tsadadden turarenta mai shegen dad’i da k’amshi wanda ke narkar da zuciyar duk wani wanda ya shak’i k’amshinsa. Wurin Binta dake baje kan gado tana sharar bacci ta isa ta tayar da ita tare da bata umurnin ta tashi tayo alwala ta gabatar da sallah, daga haka ta fice daga d’akin, kai tsaye gaban k’atuwar Tv plasma dake palorn ta nufa ta kunna, kana ta d’au remote ta dawo kan kujera ta zauna, sanja cannel tayi tare da d’an lafewa a jiki…