YAR LEKEN ASIRI CHAPTER 8 BY ANUP JANYAU (_SPY_?)

YAR LEKEN ASIRI CHAPTER 8 BY ANUP JANYAU (_SPY_?)
YAR LEKEN ASIRI CHAPTER 8 BY ANUP JANYAU (_SPY_?)               Www.bankinhausanovels.com.ng  Wani irin dirowa Saimah tayi daga kan kujerar da take zaune, saboda ba k’aramin tsorata da ganin Binta tayi ba, don tunda ta shigo bata lura da ita ba sai yanzu. Saurin kallonta Kuzeem tayi sannan ta maida dubonta wurin Binta. D’an guntun tsaki taja tare da b’alla ma Saimah wata uwar harara tace; “Tou shugabar matsorata, mutum ce ba aljana ba, tunda kika shigo fa take d’akin nan amma mitar da kike bata baki damar ganinta ba”. Wata nannauyar ajiyar zuciya Saimah ta sauke tare da k’yalk’yalewa da dariya sannan ta koma ta zauna tace; “Yoo ai tsoro halas ne, ya za’ayi inga mutum bansan daga ina ya fito ba in rasa tsorata”. Murmushi kawai Kuzeem tayi bata ce mata komai ba, sai mamakin tsoro irin na Saimah take.  “Aunty fitsari nake ji”. Binta ta fad’a tana isowa wurin Kuzeem, jin hakan yasa Kuzeem ta mik’e tare da rik’a hannunta suka nufi d’akin da ta shiga d’azun, saida ta duba bathroom d’in taga akwai ru…