YAR LEKEN ASIRI CHAPTER 7 BY ANUP JANYAU (_SPY_?) YAR LEKEN ASIRI CHAPTER 7 BY ANUP JANYAU (_SPY_?) Www.bankinhausanovels.com.ng *_RADDAL State_* 9:40am jirgin ya sauka a cikin *S.I* airport, dama tafiyar 40 minutes ne tsakanin FUNADE zuwa RADDAL a jirgi, saboda akwai ‘yar tazara kad’an tsakaninsu. Cikin natsuwa Kuzeem ke saukowa daga kan matakalan jirgin daga ita sai hand bag da wayarta, don tuni aka sauko musu da kayansu a field d’in jirgin, bayan ta sauk’o k’asa ne ta isa wurin kayanta, tayi tsaye tana k’arema airport d’in kallo, saurin mayar da dubonta tayi kan wayarta da kira ya shigo, sai taga Abba ne ke kiran. “Barka da zuwa Ranki shi dad’e, sunana Ahmad Sani, ni ne zan kaiki masaukinki”. Tana k’ok’arin amsa kiran Abba muryar wani mutum ta ratsa kunnuwanta, a hankali ta d’ago ta kallesa na ‘yan seconds, sannan ta d’auke kanta tace; “Okay”. Cikin sauri Mutumin ya d’auki trolley da laptop bag d’inta, sannan yace; “Ranki shi dad’e, Motar tana can gaba”. Yana gama fad’in haka ya fara tafiya, hakan yasa Kuzeem tabi bayansa…