WATA MACE CHAPTER 6 BY SANA S MATAZU
WATA MACE CHAPTER 6 BY SANA S MATAZU
Www.bankinhausanovels.com.ng
Look Ramlatu kinsan dai abinda ki ke be dace ba. Ta yaya na kai kuΙi gidanku amma kuma kina tsayawa da samari kuma dan cin fuska a gabana?”
“Dakata Kabir, ni fa allura ce acikin ruwa ta yaya zan tsaya ka yi min sakiyar da ba ruwa. Na sani ko Ζarya ka ke ba aurena zaka yi ba, sai na gama sakankancewa sannan in ji wuf ka fece!”
Wani miyau ya haΙiya yana jin kansa yana yi masa nauyi,
“Be san abinda ya ja shi ga auren Ramlatu ba, duk da zuciyarsa ce ja gaban kwaΙaitar da shi cewa ita ce ta dace da shi amma kuma yana ganin kamar ya yi kuskure”
Kallonta yake idanunsa jajjur, amma kuma wata shakkarta da be san dalilinta ba tana mammayeshi. Kamar wanda aka datsema baki ya kasa tanka mata haka ta juya tana girgije-girgije. Ζasan ransa ya na jin kewar Zahidaht da komai nata.
“Shikenan Ramlatu ki faΙa ma su Baba ji bi za a zo batun saka rana kuma wata Ιaya nake buΖata!”
GuΙa ta yi tare da kai masa hug, “amma ka biyani wallahi”
Janye jikinsa ya yi yana takaicinta, sai dai ya gaza hanata shi gaba Ιaya ma tsoronta yake ji dan wani kwarjini take yi masa.
***
Ζ³an kai amarya sun Ιaukin hanyar Geza. Tafiya suke ba kama hannun yaro. Tun Labiba na ganin abin wasa ne har ta soma gajiya, ita da Tukur ya ce mata nan nan unguwar Maude za a kaita. Tazararta da gida kaΙan ne amma kuma ta ji sai lulawa ake. Gashi an Ζumsheta cikin mayafi ga zafi ana yi, ganin tafiyar ba ta Ζare ba ce yasa ta yayye rufin tana kallon yadda suke wuce hanya. Wani abu ne yake tokare da zuciyarta ganin da gaske Ζauyen Geza za a kaita. Bata manta ba, nan ne garin da Ζawarta Atine ta yi aure. Suka dinga yi mata dariya tun suna yara bare kuma yanzu? Tabbas ya yaudareta amma zata nuna masa kuransa. Sai dai wata zuciyar na gargaΙinta kan kadda fa Ζilu ta jawo bau. Ba wannan ne matsalarta ba, ta ina zata fara rayuwa a Ζauyen nan da ko service me kyau basu da shi. Kennan da gaske Ζ΄an gidansu suke yi na cewar gidan ma da zata zauna na Ζasa ne? Da sauri ta girgiza kanta tana ayyana miliyan guda fa ta bashi ya zai kama mata gidan Ζasa?
Tunaninta ya katse daidai lokacin da suka ajiye motarsu a Ζofar wani gidan Ζasa. Kasancewar akwai sauran rana bata Ζarasa faΙuwaba. Sossai ta ware ido tana kallon Ζofar gidan. Ya sha shafe da farar Ζasa an mana irin tambarin nan na indomie da ake yi wa gidajen Ζasar Ζauyuka. Gabanta ya doka, tana saukewa Hajiya iyyah harara saboda mitar da take na taΖi rufe fuskarta. Bata damu ba, ta soma jan hannunta,
“Labiba fito mun kawo ki gidanki”
Hajiya Mawwadah ta maida dariyarta tana yin gaba, tare da cewa,
“ku sata ta yi basmallah ta saka Ζafar dama!”
“Angama Mamarmu”
Cewar Ade tana rangaΙa guΙa cike da shaΖiyanci. Su Yaya Amina da Maryam da Husnah kuwa sakatotto suka yi dan dama su basu san dawan garin ba tunda basu zo jera ba. Duk surutan da ake a gida sun Ιauka iya shege ne. Labiba kamar mutum-mutumi haka aka dinga janta. Ta dinga binsu kamar raΖumi da akala. Yuuuu! Yara suka yi dafifi a Ζofar gidan suna shafa bango kamar sun ga wani sabon abu. Suka shiga gida sai Ζamshin Ζasa yake da yake anyi yayyafi kafin su Ζaraso.
Ζakuna uku ne a gidan, Ιaya ya Ιauke kujerunta gaba Ιaya da tv da fankar Ζasa Ox babbar sai firij Ιinta. Ζayan kuma ya Ιauki gado da kwaba da mudubi. Sai kayan kicin Ιinta da aka tsubesu a cikin Ιayar kwabar saboda babu kanta. Hasalima turaku uku ne na murhun dutse da aka yi da gini babba da Ζarami kuma ciki babu daΙe. Sai rumbun hatsi a tsakar gidan, daga gefe kuma buΙaΙΙan banΙakine. Tsakar gidan ya sha irin shafa nan me tafiyar mijici da ake yi a Ζauyuka da farar Ζasa. Labiba kasa jurewa ta yi ta warce hannunta tare da lallubar jakarta hannun Yaya Amina tana ΖoΖarin kiran Tukur amma kuma yaΖi Ιagawa. Fashewa ta yi da kuka,
“Wallahi bazan zauna a wannan matsiyacin Ζauyen ba, ai ba haka muka yi da shi ba. Uw…sa ya yi da kuΙin da ya…”
Bakinta Hajiya Mawwadah ta buge tare da turata Ιakin da gado yake, ba dan komai ba sai dan ganin yadda yara suka yi dafifi suna kallonta. Daga bayansu kuma mata ne zuga guda an zo tarar amarya. Suna zama kuwa matan na shigowa. Nan aka gaggaisa suka soma gabatar da kansu, matan kawunansa ne da kannansa sai kuma yayyansa mata uku. Dukkansu anan garin suke wasu ma suna maΖotaka da Labiban. A Ιage take dubansu, tana yatsina duk ta gama Ζaguwa Tukur ya dawo ta sauke masa kwandon masifa na ha’intarta da ya yi ya kawota Ζauye. Lallai mutum mugun ita ce ne. Ζanwar Tukur ce ta kasa haΖuri da duban da take musu, ta ga ko Ζ΄ar kunyar nan ma ta amare babu a gun amaryar tasu ta furta,
“mu dai ance mana matan birni basu da ta ido, naga kuma da alama irinsu aka kwaso masa!”
“Mene ne haka Magajiya”
Cewar matar Ζanin mahaifinsu Lantana tana umartar yara da su ajiye fantekun da suka zo da su. Nan da nan suka miΖe, Addeh ta cikasu da tukuicin dubu goma. Kamar su goyata haka suka fita suna murna. Sai dai da hanzari wasu suka zagaya suna kaiwa mahaifiyar Tukur tsegumin irin surukar da aka Ιauko mata. Sossai ta shiga faΙa tana ba zata lamunta ba kasancewarta mace me zafi. Ana haka Tukur ya Ζaraso, nan ta haushi da faΙa haΖuri ya dinga bata tare da nuna mata zai ja kunnan Labiban. Fita ya yi yana jinjina abinda ya faru duk da ya shiryawa haka domin ya san halinta amma ba zai juri ΖasΖantar da martabar mahaifiyarsa ba. YaΖin nasa ne._Suna da yatsan Ιagawa su yi nuni wa shafin da Ζaddara ta buΙewa Ιayansu abisa kalmar sakaci. Amma kuma nasu yatsan ya kan zauna a Ζwantare wajen nuni wa nasu sakacin zuwa kalmar Ζaddara. Idanunsu na da kaifi wajen hango kuskure duk ΖanΖantarsa. Amma suna zama makafi yayinda suka hango nasu kuskuren koda kuwa kusancinsu da shi ya kai sun shafa sun ji tabbacinsa._+
WAYE TUKUR?
Ita ce tambayar da Labiba taketa nanawata acikin zuciyarta. Domin gaba Ιaya ta rikice. Ζ³an kai amarya kuwa tun suna Ζunshe dariyarsu har wasu suka soma yi a gabanta sai da Hajiya Mawwadah ta tsawatar musu. Ta kira Yaya Khamis ya fi sau shurin masaΖi amma wayarsa bata shiga hakama Amne. Ζarshe ta ajiye girman kanta ta sa Husnah ta bincika mata aka tabbatar mata network Ιin garin baya tafiya sossai sai cikin dare ko kuma ka zaga baya ka hau dutse.
Abin ya bata mamaki dama akwai irin waΙanna Ζauyukan a cikin garinsu? Ta dai ji ana faΙar garin geza amma bata taΙa zuwa ba, hasalima akwai gonakin mahaifinsu a garin waΙanda bayan rasuwarsa duk aka saidasu. Amma bata taΙa tunanin haka Ζauyen yake ba. Tana yawan ganin Ζ΄an garin sun kawo tallan gyaΙa me gishiri cikin Sakwato. Yanayin yadda suke wajen rashin tsafta ga rashin kunya da raina mutane, uwa uba rashin wayewa. Duk bata Ιauki lamarinsu da zafi ba, ta Ιauka kawai abu ne irin na Ζ΄an tallah musamman a shigarsu.
***
Tukur shi ne cikakken sunansa. Matashi ne me kimanin shekaru talatin cif, amma matsi da Ζuncin rayuwa ya takureshi waje Ιaya Ιan firit da shi kamar Ιan shekara ashirin da Ιoriya. Yana da faΙin Ζirji da kuma Ζaton kai ga tagomashin tsagun magge a gefan bakinsa.
Su takwas mahaifinsu ya mutu ya bari, babu wanda ya sami tagomashin karatun boko saboda rayuwar yau da gobe. Yayarsu Hajara sai Katume da Tsahare da kuma Indo. Duk suna aure anan Geza da Ζ΄aΖ΄ansu. Tukur shi ne na biyar sai Auwala da Isuhule daga nan sai autarsu Mero data rage ba ayi mata aure ba.
Auwala direba ne Lagos yake zuwa. Isuhule kuwa manomine. Sai Tukur da ubangiji ya taimakeshi aka turashi garin Sakwato almajiranci. Anan ya sami karatu na izzuf talatin cif daga nan ya faΙa buga-bugar rayuwa. Allah ya bashi nasibi kan gyaran takalma da kuma facinsu.
Kasancewarshi babba cikin maza Ζ΄an uwansa be bashi damar yin aure da wuri ba, duk kuwa da gorin da ake masa na Ζannansa duk sunyi aure har ma da yara biy-biyu Isuhule da Auwala. Badan komai ba sai dan yadda yake tunanin sana’arsa ba zata Ιaukeshi da iyalinsa ba amma a ransa yana son ya raya suna.
Haka abokansa babu wanda be aure ba. Lokacin da ya riski dami a kala game da Labiba ba Ζaramin farin ciki ya yi ba, koba komai lokaci ya yi da shi ma zai raya gori. Ya kuma ci alwashin ko zata yi hauka ba zai saketa ba. Musamman da ya ga gidan data fito.
Ya godewa Allah da ya sa duk dabarar da ya haΙa babu wanda ya fuskanceshi ita Labiba na Ιaukar Khamis ne ya turoshi shi kuma Khamis na Ιauka Labiba ce ta aikoshi. Ko Jawwad sai ranar Ιaurin aure suka haΙu shi ma sama-sama kuma be wani tsaurara bincike ba da jin cewar Labiba ya aura. Hasalima shi ta kansa yake sakammakon kamuwa da cuta me karya karguwar jiki.
Mahaifiyarsu Baba Harira mace ce me faΙan gaske, bata son raini. Tana sana’ar gasarar koko da wainar gero da safe. Da rana kuma tana taliyar hausa da manja da awara. Haka kuma tana sana ar saida mai da Ζuli-Ζuli. Tun suna yara sana’arta kenan.
Baba Harira tafi kowa takaicin rashin auren Tukur, da kanta ta sha nema masa auren Ζ΄aΖ΄an abokanta sai ya doje. Hakan yasa ya daina zuwa gidama gaba Ιaya sai dai ya yi musu aike. Gidansu Tukur babban gidane me wadatar Ιakuna, matan Ζannansa da Ζ΄aΖ΄ansu duka a haΙe suke da mahaifiyarsu. Sai dai katanga da ke nuna Ιangaren wancan da wannan amma Ζofa Ιaya ce ta shiga gidan.
Girki a cikin gidan ake basa raba tukunya, sai dai idan an gama Baba Harira ta rarraba. Idan kana san ganin fushin Baba Harira ka taΙa Mero auta, tabbas ranar zaka ga fushi da sababi dan haka surukanta suke shakarta kuma suna taka tsantsan da ita. Ζiri-Ζiri mijinki zai siyo miki abu, koda ya bata nata ta taka Ιakinki ta Ιauki naki ta haΙa biyu. Idan kinyi magana ta ce yayanta ne ya siya kuma Baba ta goya mata baya.
Kwatsam Tukur ya zo mata da batun zai auro Ζ΄ar birni ya kawota nan, abin ya Ιaure mata kai amma bata hanashi ba a saninta Ζ΄ar birni da hankalinta bata zama a garin nan. Domin su kansu suna fatan yaransu in sun fita talla su samo na cikin gari su aura dan har murna ake zo ma uwa idan Ζ΄arta ta samo Ιan cikin Sakwato.
Amma ba a Ζwacewa yaro garma dan haka ta yi masa fatan alkhairi. Tun a wajen haΙa lefe suka soma haurawa, a cewarta ya tsawala amma sai ya nuna mata Ζ΄ar babban gida ce. Data turkeshi kan ina ya sami kuΙi be Ιoye mata komai ba amma ya nuna mata shi fa ba AUREN MANUFA zai yi ba in ya aureta ya aura kenan. Sossai ta goya masa baya, domin ta tsani masu yin irin auren da ya faΙa mata tana danganta hakan da yi wa ubangiji shisshigi a lamuransa.
A wajen fitarwa da Labiba sashi ma sai da suka haura, domin kaf surukanta Ζofarsu na ciki amma ya nuna mata na kwana biyu ne. Dan haka Ζofa biyu aka yi Ιaya tana cikin gida Ιaya na waje.
***
Washegari Baba Harira ta sa aka damawa Ζ΄an kawo amarya koko, ya ji gasara ya yi kirtif ga kuma wainar gero da tasha Ζuli da man Ζuli ziryan aka yanka albasa akai. Sai aka Ιora musu farar alawa akai madadin sakari. Biredin da ya siyo musu kuwa ta rabawa jikokinta acewarta Labiba ta ja musu. Sai dai ga mamakinsu tsaf Ζ΄an kai amarya suka lamushe waina da koko suna santi. Hakan ya ragewa Baba Harira haushin Labiba koba komai ta ci albarkacin danginta. Sai dai Labiba ΖirΖiri taΖi ci taΖi sha sai da Hajiya Mawwadah ta aika ango ya samo mata tea da biredi da Ζosai. Haka ta ci tana yatsina, su dai da ido suke binta suna ganin dole ta sauko.
Da zasu tafi har gida suka shiga suka yi wa Baba Harira godiya suka rabu kowa ransa wasai. Sai lokacin Labiba ta Ζara raina kanta. Kuka take wiwi tana riΖe Husnah ita ma Husnahr Ζwallar tausayinta take sharewa Yaya Amina kuwa ta kasa cewa komai. Da Ζyar da siΙin goshi suka ΙamΙare suka shiga motocin Ζan saΙalo estate suka nufo cikin Sakwato.
A mota gaba Ιaya sunyi Ιif suna jimamin wace rayuwa Labiba zata yi?
***
Lokacin da labari ya je kunnan Amne game da garin da aka kai Labiba kamar zata yi hauka. Tasa Khamis ta yi agaba ta dinga surfa masa zagi ta uwa ta uba. Abokan zamanta kuwa banda dariya babu abinda suke yi mata. Su Yaya Amina ne kaΙai masu tausarta hatta Hajiya Mawwadah ta kware mata baya. Khamis kansa ya shiga tashin hankali sai yanzu ya soma tunanin yadda auran ya kasance, yana tunanin duk da zaman Ζarantace ne amma wace rayuwa zata yi?
***
Labiba amarya kuwa, bayan tafiyar danginta ta fito ta zazzaga gidan, babu laifi kayanta sun haska gidan dan tana kallon yadda Ζ΄an Ζauyen suke shasshafasu suna kallon fuskarsu a jikin mudubi.
Abu Ιaya ya burgeta da garin ba a cika Ιauka wuta ba. Koba komai ta samu ta cajin yin karatun novel da yin game. Sai da ta gama zaga gidan tsaf sannan ta lura da Ζofar da ta zamo mahaΙarsu. Jim ta yi kamar zata buΙe sai kuma ta Ζyale.
Da rana aka aiko Mairo ta kawo mata gero da wake, Ζerere ta tsaya mata aka kamar wata sa’arta bayan ta dire kwano. Bayanta kuma Ζawayenta ne da suke dafifin leΖa Ιakin Labiba suna kallon firij. TaΖaici ya kamata, ta tsaya kawai tana kallonsu kafin ta gama yanke abin yi Mairo ta buΙe firij ta rarraba musu pure water. Ta zarce ta Ιauki kwalbar turaren data gani gefan kujera.
“Ina so!”
Ta furta cike da ko in kula, daga bisani ta ba wa abokanta umarnin su tafi. Fuu! Labiba ta miΖe ta bi bayansu. Janyo kwalar rigar Mairo ta yi tana huci,
“Bani kayana!”
“Na hana ai yayanmu ne ya siyo..”
“Da kuΙin uwarki ya siy…”
Wani wawwan ihu Mairo ta tsalla, wanda ya janyo hankalin mutan gidan suka shiga rige-rigen nufo sashin. Kafin Labiba ta yi aune sun soma tuttuΙowa ta Ζofar da ta dinga tunanin ta me ce ce.
“Wallahi baki isa ki zagarmun Innarmu ba. Ζarya nayi ba shi ya siya ba?”
Ta faΙa tana cakumar wuyan Labiban wadda mamaki da takaici sun hanata kataΙus. Daidai Ζasawowar Baba Harira tana tambayar ba asi, caraf sai Mairo ta Ζara kukanta tana faΙin,
“Innarmu zaginki ta yi…”
“Zagi?”
Sauran matan suka haΙa baki wajen faΙa,
“ke kuma taki tarbiyar kenan daga zuwanki jiya?”
Wata Ζ΄ar tsamurmura ta faΙa, kafin su farga sai ga Tukur kamar anjehoshi.
“Lafiya Inna? Ke dalla malama sakar mata wuya!”
Ya faΙa yana watsawa Mairo harara. Da hanzari ta saketa. Matan kuwa da Ιai Ιaya suka soma zare jiki saboda sun san halinsa.
“Ke Ladiyo me ya faru..”
Mairo ta yi caraf,
“Innarmu amaryarka ta zaga..”
“ban tambayeki ba suda!”
Tiryan-tiryan Ladiyo ta faΙi gaskiyar abinda ya faru, duk da hararar da Mairo ta ke antaya mata. Juyowa ya yi tare da nunata da yatsa ya shiga watsa mata kashedi. Sum-sum ta ja tawagar Ζawayenta suka fita. Sai lokacin ya dubi Inna yana sassauta murya kansa a Ζasa,
“Dan Allah Inna kadda ki biye zancen yaran nan su hanaku zama lafiya. Labiba dai Ζ΄ar ki ce kamar ni…
“Dakata min Tukur ni ma a gabanta zamu yi magana da kai?”
Ta faΙa tana tsattsareshi da idanu. Kai ya girgiza jiki a sanyyae baya san fitina ta soma tashi tsakaninsu, yasan Innarsa kuma ya san labarin Labiba tabbas ya kamata ya yi wani abu..Fuu! Ta juya ta nufi sashinta. Labiba ta bi su da idanu kawai tana jinjina lamarin.
***
Sati uku da kai Labiba Ζauyen geza, gaba Ιaya hankalinta ya tashi. Tukur ya rantse mata ya maya babu saki tsakaninsu. Kuma ya gayamata dalilinsa na auranta da hanyoyin da ya bi. A ranar ta kira Yayanta ta faΙa masa komai. Shi kansa ya girgiza amma babu yadda zai yi, in ya yi wani yunΖuri tabbas iyayansu zasu fahimci manufarsu ba kuma ya san ta Ζara wani laifin kan na baya. Dan haka hankali ya kwantar mata tare da nuna ta yi haΖuri kawai ta rungumi Ζaddara.
Ζangaren Amne ma dai hakane, amma zuciyarta na cike da danasani da takaicin yaudarar da aka yi musu.
Labiba fa ta shiga tsaka me wuya, da fari ta soma zuba rashin mutunci sai dai mutanan gidan suka nuna mata sun fita gogewa. Mairo kaΙai ta isheta ciwon kai. Haka zata jawo yara ta kunna kallo, ta Ιaura ΖanΖara ta saka a firij dinta wai ta saidawa idan kuma ta hana Baba Harira ta tsefet tsaf ta uwa ta uba.
Ranar girkinta kuwa babu me taimaka mata, saboda ita ma bata taya kowa. Inda Allah ya taimaketa kwana biy-biyu ne zagayowar girki dan haka tana samun hutu na kwana huΙu. Tuwon dare sunayin kwano uku, saboda dumammen safe kuma shi za a kuma ci da rana wata rana sai dai idan muguntar Baba Harira bata tashi ba. Tukur ya so nuna mata gata Ζwarai amma mahaifiyarsa na hanawa, amma duk da haka yana yi a sace. Duk yadda taso ta yi masa rashin kunya tana shakkar mahaifiyarsa don bata Ζyalewa. Tun a satin farko da ta nuna masa Ιanyen kai ta yo waje kan karΙar haΖΖinsa ta gane wacece surukarta. Dan sunkutukum ta Ιauketa ta a kafaΙa ta maida ita Ιakin tare da saka kwaΙo ta yi tafiyarta.
Da safe sai goma da rabi ta buΙeta, bayan tun asuba ta buΙewa Ιanta Ιaki. Lokacin data fito kuma ta sa facalolinta suka dinga yi mata dariya da habaici tana gudun miji. Tun daga lokacin ta kiyayi matar dan bata son raini. Ita kuma a duniya ta tsani ΖasΖanci. Yanzu gaba Ιaya tunaninta ya tafi ne kan yadda Ιale auran cikin ruwan sanyi.
Amma kuma Khamis ya tabbatar mata badai gidansa ba matuΖar ta kaso auranta. Wajen Amne kuma bata ga fuskar hakan ba. Babban takaicinta duk wasu kuΙi nata ta wasarairai da su. Kaya ta yi masu mugun tsada ga shi ta Ζare a Ζauye. Ko kayan kicin kuΙin da ta kashe suna da ya wa, da fari ta soma tunanin ta fitar da su ta siyar amma kuma tasan karya mata su za ayi. Duk wata kaddara tata ta rasa inda suka yi dan sai yanzu ta farga da cewa ta yi Ιarnar kuΙi ba kaΙan ba. Gidan da Yusuf yake ciki kawai ya rage mata sai tsirarun kuΙi wajen Khamis.Tun auransu da wata biyu ya fuskanci ta soma tu’amli da maganin hana Ιaukar ciki, da fari ya maida abin na marmari amma dag bisani sai ya fuskanci da gaske take bata buΖatar haΙa zuri’a da shi. Duk yadda ya fahimtar da ita hakan ta gaza fuskantarsa, hasalima dalilin hakan suka shafe sati uku suna gaba. Ζwarai yana buΖatar haihuwa amma babu yadda zai yi ya turasasa Ramlatu. Da farko bambami ya soma, daga bisani ya ga ba ci ya koma lallashi. Ζarshe dai tsada suka yi kan zai dinga biyanta dubu goma duk wata domin kadda ta sha maganin . Babu ja ya amince saboda haihuwar ce muradinsa a yanzu. Sun yi wannan yarjejeniya da wata Ιaya kwatsam safiyar yau yana shirin fita aiki Allah ya nuna masa kwalin maganin da ta sha ta bari kan mudubi. Ζwarai ransa ya Ιaci har wani Ιaci ya ke ji. Kai tsaye fallo ya nufo yana Ζwalla mata kira.
Zaune take tana dana wayarta, bata amsa ba har ya Ζaraso inda take. Wayar ya warce tare da wurgata kan kujera.
“Ni zaki munafunta Ramlatu, ba tsada muka yi dake ba?”
Ya furta yana kanga mata kwalin maganin a fuska. Ta razana amma da yake Ζ΄ar duniya ce sai ta maze. Jijjigata ya yi yana huci kamar mahaukacin kare. A zuciye ta ingijeshi, abinda da Ζarashen maye sai ya yi taga-taga zai faΙi ya cize. Wannan dmaar ta samu ta nufoshi da dukkan Ζumajinta. Masifa ta shiga surfa masa kamar ta ci babu duk da tana jin Ιar a Ζasan ranta. Ganin ya nufota kamar zai daketa ya sa ta gyara tsayuwarta. Yana Ζarasowa ta tattara duk wani Ζarfi nata ta cakumi kwalarsa.
ShaΖar data kaiwa wuyansa ita tafi komai bashi mamaki, zuciyarsa ta zo iya wuya. Ya Ιaga hannu zai kwaΙa mata mari, kamar wanda aka jonawa shocking sai ya janye. Ya yi wa kansa alΖawarin ba shi ba dukkan mace. Yana tuna silar rasuwar Zahidaht ya kan ji ya tsani kansa, tabbas ba zai sake wannan gangancin ba. Kallonsa ta yi sheΖeΖe,
“Wai Kabir da dukana zaka yi, to me ya hanaka ka dakeni?”
Shiru ya yi mata yana huci, ga hannuwanta _still_ a wuyansa ta gaza sakinsa. Jijjiga jiki ta soma yi,
“haihuwa ce da kai na ce ba yanzu ba,ka barni in yi sha’anin rayuwata. Ko zan haihu sai na mori Ζuruciyata ballantana kuma ni ba sakarya ba ce da zan yadda in haihu da mutum irinka. Wallahi ba zan haifi ‘ya’ya a dinga kawomunsu an bi su an ΖwaΖwaleba!”
Kamar saukar aradu ya ji shigar kalamanta, jikinsa ya yi mugun sanyi. Zuciyarsa ta matse da wani irin yanayi. Tabbas sai yanzu ya ke Ζara danasani da takaicin rayuwarsa ta baya, be taΙa hango abinda Ramlatu ta faΙa ba duk da yasan ta faΙa ne domin kare kanta. Murya a raunane ya furta,
“sakarmun wuya!”
Ita kanta ya bata tausayi ganin yadda kalamanta suka illatashi lokaci guda. Amma Ζasan ranta tana jin wannan shi ne makamin yaΖarsa ta huta kawai. In ya ga ba zai iya ba ya sauwaΖe mata. Wayarta ta Ιaga ta dana kira, ta bishi da idanu ganin ya dafa bango yana bi har ya kai Ζarshan fallon ya fice. Tsuka ta ja tare da furta,
“Adijee na gama da batun Man fa, na samo hanyar hukuntashi”
Daga can Ιangaren aka furta”ke fa kwalba ce wallahi”
Ba ta bata amsa ba, suka koma wata hirar da ban.+
***
Labiba ganin babu sarki sai Allah ya sa ta saki jikinta ta soma fuskantar rayuwar da ta riska. Ta karΙi duk wani sauyi da ta samu acikin rayuwarta illa abu biyu zuwa uku. Baba Harira dai tsakaninta da ita mutuntawa ce, haka ma facalolinta tuni ta taka musu birki kan izgilanci da suke yi mata kuma Tukur ya mara mata baya. Hakan ya sama mata sauΖi sossai. Tsakaninta da su gaisuwa sai in ta fito girki sun haΙu wanda babu wanda yake taimaka mata. Hakan kuwa ba Ζaramin naΖasu ya ja mata ba, duk ranar girkinta sai ta yi zazzaΙi sabida bata da mataimaki.
Mairo ma tuni ta dakatar da ita, duk masifarta da ta Baba Harira sun haΖura sun sa mata ido domin ta ΖeΖashe Ζasa ta hana Mairo Ιaukar mata ko tsinke. Idan sun yi magana amsarsu ita ce guminta ne bana Ιan uwansu ba. Jin hakan ya kan sa guiwoyin Baba Harira yin sanyi domin tana gudin asan AUREN MANUFA Ιanta ya yi a saka shi a bakin duniya. Dan ta lura Ζwarai Labiban tere take san yi musu. Wnda tana da yaΖinin matuΖar Ζaddara ta ratso ya saki Labiban babu me bashi auren Ιiya a garin dan haka suka shafa mata lafiya.
Babbar damuwarta yanzu shi ne muguwar kazantar Tukur, tun lokacin da ta yi karatun ta nutsu kan rayuwarta ta baya ta fuskancu Ζazanta da wasu Ιabi’unta suka ja mata barin gidan Yusuf ta Ιauki Ιamarar gyara kuskuranta. Komai nata tsaf yake abin sha’awa. Sai dai ga Tukur abin ba haka bane. Tukur cikakken Ζazami ne na bugawa a jarida. Ya kan shafe kwana biyar be yi wanka be yi brush ba. Hakan yasa haΖoransa suke yalaye shar da su babu kyan gani. Har mamaki take yi me yasa bata kula da duk wannan ba KAFIN AURE amma Ζaddara ta tiga fata. Kaya kuwa sai ya yi sati yana maimaita saka m
su kuma ya zo ya cusa mata cikin kwaba, kusa da wankaku su yi ta tashin tsami. Fason Ζafarsa kuwa kullum cikin janye mata zanin gado yake yi. Ta yi masifar ta yi lalashin ya kan rage akan da amma har lokacin be gamsheta ba.
***
Yusuf kam sai sambarka, arziki ya ninka na da. Allah ya sa masa albarka, bayan gidan youghurt da ya buΙe yanzu yana da wajen kiwon kaji da kuma raguna. Shi kansa har mamaki yake yi. Haka kuma be yi Ζasa a guiwa ba wajen tallawa dangi da Ζ΄an uwa. Kowa nasane be ware ba, hidimar abinci da sutura duka ya Ιaukewa mahaifansa. Su Khamis duk sai suka raina kansu, Ιaga kai da Ιagawar da sukewa dangi sai ta tashi a babu. Babu wanda zai buΙe baki be kira mutuntakar Yusuf a dangi ba. Ya zamo wani tauraro me haskawa. Matarsa kuwa ta zamo abar kwatance domin ita take Ζara goya masa baya kan dukkan hidimar danginsa. Da jiki da zuciyarta tana tare da shi. A yanzu haka tana Ιauke da ciki wanda suke sa ran haihuwarsa yau ko gobe. Duk wata siyayya ya gamata. Wasu lokutan tasa kayan babyn yake a gaba yana kallo, wani lokacin ya yi kuka wani lokacin ya yi dariya. Yana tuna Ιiban albarkar Labiba a lokutan haihuwarta da bashi da karfin siyan komai.
***
Da gudu yaran suka shigo, tana zaune ta miΖe Ζafa saboda nauyin da cikinta ya yi mata tana dubansu. Murmushi ya suΙuce mata ganin yadda suke zaga fallon suna dariya. Da alama Khalifa na san karΙar teddyn Ιin hannun Ummi ne. Daidai lokacin mahaifinsu ya yi sallama bayansa yaya Amina ce da nata yaran. Da gudu Ummi ta tafi ta rungumeshi,
“Abba ka ga Khalifan Mommah ko”
“A’a fa Ιiyar Abba ke kika taΙamun yarona”
Cewar Shukura tana murmushi, Ζarasawa suka yi gaba Ιayansu ta yunΖura tana gaishe da yaya Amina. FaΙa ta soma yi mata kan mene zata takura kanta ta ce sai ta sunkuya bayan ta yi nauyi. A kunyace ta Ιauke kai tana murmushi, ita ma murmushin ta yi Ζwarai halin yarinyar na burgeta. Sai yanzu ta sake gasgata cewar Yusuf ya yi mata.
Hirar zumunci suka shiga yi, Shukura ta miΖe ta kawo mata abin motsa baki sannan ta basu guri su gana da Ιan uwanta bayan ta yi dabarar janye yaran. Wannan Ιabi’a tata ta Ζara mata Ζima a idanun dangi da yawa. Duk yadda kuka saba da ita matuΖar ta kula wajen Yuauf suka zo to kuwa zata basu waje su yi uzurinsu. Musamman yanzu da ya kasance Yusuf Ιin ya zama babban Ζarami a cikinsu. BuΙi da wadata sai Ζaruwa suke yi a harkokinsa. Mutane da ya wa na ganin shi ya maye gurbin mahaifin Labiba acikin zuri’arsu saboda yadda harkokin kuΙi suke zuwar masa da nasara.
Amne kanta ta shiga nadama da danasani, duk wata hidima ta gidan shi ne kama daga kan cimma zuwa sutura. Sau tari idan aka shiga taro har shaguΙe ake yi mata cewar Ιiyarta me Ζashin tsiya ce gashi nan daga rabuwarsu Yusuf ya zama wani abu. Ira-iran wannan kalaman kansa mata jin Ζyamar shiga dangi, sossai take dana sanin raba Labiba da gidan auranta.
Post a Comment for "WATA MACE CHAPTER 6 BY SANA S MATAZU"