WATA MACE CHAPTER 3 BY SANA S MATAZU
WATA MACE CHAPTER 3 BY SANA S MATAZU
Www.bankinhausanovels.com.ng
SAUYI.
Haihuwar Labiba ta kawo sauyi da yawa a rayuwar aurenta da Yusuf. Sossai zahirin hallayarta ta fito kowa ya sani. Muguwar Ζazantar data zame mata jiki ta bayyana. Ζakinta baya zaunuwa saboda zauri ga Ζarnin miyau. Domin tana tashi daga bacci shi take soma tsartarwa a jikin bango. Tun yana kauda kai har ya zamana ya soma tankawa amma babu sauyi ko kaΙan sai ma izgilanci da rainin wayau data tsiri yi masa. Hakan ya asassa musu rabuwar Ιaki kowa ya zamana yana da mallakinsa.
***
Duk abinda ya ke faruwa game da Ζazantar Labiba Amne ta sani sarai, amma bata taΙa kadda baki ta yi mata magana ba hasalima hakan ya yi mata yadda take so ko ba komai Yusuf zai Ζara Ζuntata da baΖin ciki. Watan Ummi goma a duniya Allah Ya sake bata rabon ciki, tabbas samuwarsa ta Ζara asassa komai na rayuwarta. Iskanci kala-kala da an yi magana ta ce cikine. Tun ba ajin kansu har ya zamana iyayensu maza sun soma shiga cikin lamarin domin sassanci. Baba Ιaure dai kodayaushe yana bayan Yusuf saΙanin mahaifinsa.
***
A safiyar wata Asabar Yusuf ya tashi da sassafe. Nazira Ιiyar Yaya Asabe da tazo musu hutu yasa ta kira masa Labiba ta tafi da Ιan gudunta tana tsale. Tana shiga ta sameta a kwance kamar mataciyya. Kauda kai ta yi tana gunguni dan Nazira akwai rashin kunya. Ζ³ar Ζara ta yi, wadda ta haddasawa Labiban farkawa, a tunzure take duban yarinyar da haushin tadata da ta yi. Nazira kuwa baya ta yi tana Ιan turo baki. Tsittt! Kake jin sautin fitar miyan bakinta, bai sauka ko ina ba sai a bangon Ιakinta. Nazira data shigo ta ja baya tana kyaΙe baki. Idanunta Ζur a kan bangon da Addahrta ta zubar da miyan. Ζauke kai ta yi tana yatsuna fuska. Karaf a kan idanun Labiba, ta maka mata harara,
“Dan ubanki ni kike kyaΙewa baki?”
Ja da baya yarinyar ta yi tana zare idanu, domin tasan matuΖar ta shiga hannunta mai Ζwatarta sai ubangiji. Bata sami nasarar guduwa ba ta cafkota.
“Ba dake nake ba?”
Da sauri yarinyar ta toshe hancinta saboda hamammin bakinta daya doketa. Daidai lokacin da take kicin-kicin Ζwacewa Yusuf ya jiyosu ya tako zuwa Ιakin badan ransa ya so. Sai dan sanin zata iya illata masa yarinya kafin zuwansa.
“Laby cikamin yarinya!”
Ya furta da fuskar shanu.
“Idan anka Ζi hwa?”
“Zan Ιauki mataki fiye da tsamaninki!”
Kallon uku kwabo ta watsa masa, ta cuno baki tana karkata kai.
“Da anka yi man wanga tutiya, banda wannan lokaci kajiya”
Wani Ζululu ne ya tokare masa maΖoshi, da Ζyar ya haΙiye miyan daya tattaro, bai san yaushe ne Labiba zata sauya ba? Ba haka ya ga KOWACE MACE na yi wa mijinta ba. Wai shin jarrabta siyanta ake da Labiba ta kwaso duk wasu makaman raini ta zuba akansa? Ba tare da ya tanka mata ba, ya juya ya kama hannun Ummi da Nazira da zumar su bar Ιakin,
“Allah ka rabani da lusarin namiji!”
Saukar kalamanta kamar aradu cikin kansa, a fusace ya juyo ya watsa mata wani kallo muryarsa na rawa,
“Ba ki ji ya daΙin halinki ba, Ιiyan boya kawai”
“Uwa taka ma ai tsattson boya ce..”
Jifa ya kai mata da takalmin Ζafarsa, ya kuwa yi nasarar samunta a bakinta. Ta Ζwalla Ζara tana riΖe wajen. Take leΙΙen ya fashe kafin ajima ya kumbura ya yi suntum da shi. Ta kuwa shiga surfa masa zagi ta uwa ta uba, ganin idan ya biye mata sai ya iya yi mata dukan da zai nakasata ya sa ya fice da niyyar bar mata gidan gaba Ιaya. Nazira da take riΖe da Ummi tana kuka ta yi sakare tana kallonsu. Farga ya yi da yarinyar ya juya kawai ya fita gudun yin abin kunya.
***
Cikin Labiba na Ζara girma Ζazantarta ta Ζaru fiye da baya. Nazira da take tayata aiki ta tattara kayanta ta gudu saboda masifarta. Cikinta na gab da haihuwa gwamna mai ci ya bawa Baba Ιaure kwangilar gina babbar kasuwar da ta kasance a tsakiyar garin sakwato. Wadda ta haΙa kowane nau’in kaya na kasuwanci. Kasuwa ce da aΖala ba a kasaraba aka yi itifaΖin zata ci naira miliyan Ιari da hamsin da Ιoriya. Sossai wannan kwangila ta fito da martabar duk wani Ιan cikin *ΖAN SAΖALO ESTATE.* Nan da nan Baba Ιaure ya soma gudanar da gwangilar cike da Ζarfin guiwa.
Yusuf na Ιaya daga cikin ma’aikatan da aka Ιauka, kuma yana cikin waΙanda aka ba wa babban matsayi a wajen. Safiyar da zai fita aikin haka suka rabu da Labiba da zagi uwaka ubanka kare baya ci ba. Ji ya yi kamar bazai fita ba saboda Ιarin rai.
Tunda ya bar gidan kansa ya ke ciwo, ga jiri da yake Ιibarsa lokaci-lokaci. Haka ya daure ya tuΖa machine Ιinsa har zuwa inda ya ke san zuwa. Aharabar ma’aikatar da ake gudanar da kwangilar da wan mahaifinsa ya karΙa ta gina babbar kasuwar MARWAKH ya samu ya yi matsuguni. Tun daga nesa ya hango Baba Ιaure yana zagaya wajen, ya zuba masa idanu, tsoho mai karamci da sanin ya kamata. Tarin dukiya bai Ιora masa girman kai ba, kamar yadda Ιiyarsa ta Ιorawa kanta. Sau tari yana jin kamar ya saki Labiba ya huta, sai dai kullum yana tuna karamcin mahaifinta da kuma furucin mahaifinsa,
“Labiba Ιiyatawa ce, ni naka Ιaurama aure da ita. Amanatata naka baka, ni zaka duba ba ita ba!”
Ajiyar zuciya ya saki, ya taka akan duga-dugansa, daf da yayan mahaifin nasa ya Ζarasa tare da rusuna ya gaisheshi. Daga bisani ya cire rigarsa ya saka ta ma’aikata kamar kowa. Cikin hanzari ya shiga sahu, aka soma loda masa suminti a kwano yana Ιauka kamar kowa. Nauyin sumintin ya danΖarar da dogon wuyansa, har ya bada wata Ζara Ζas! Cije laΙΙansa ya yi yana jin Ιaci a Ζasan ransa, sai dai kuma wata zuciyar na tuna masa,
“da haka kowa ke mallakar gumin hallak!”
A haka suka shari awa huΙu suna aikin gini, wasu na Ιaukar bulo, wasu na kwaΙin suminti wasu kuma na Ιaukar kwaΙin suna kaiwa masu dasa harsashin gini. Nan da nan suka ci Ζarfin aikin domin sun kai kimanin su Ιari da hamsin. Sallah da cin abinci kaΙai ya ke tsayar da su. A haka suka kammala. Daga bisani suΖa soma bi layi sahu-sahu ana rarrabamusu haΖΖinsu na ranar. Kowannansu da naira dubu uku ya tashi.
Hannu yasa ya karΙi nasa kason, farin ciki na zaga zuciyarsa. Idannunsa na kan kawun nasa, yana yaba hallayar dattijon har gobe. Tabbas samun irinsa sai an tona. Ba kuma shi kaΙai ba da yawansu sai sun yi godiya bayan sun karΙi kuΙin, ba don komai ba sai don karamcin shugaban nasu. Sau tari idan sun yi aiki irin wannan na kwangila ga su kuma da yawa, maimakon a basu dubu Ιaya da Ιari biyar ko dubu biyu na yini da aka sani ana biyan kowane magini. Wato raba kuΙin biyu da wasu suke yi, suna yi musu tinΖahon suna da suna da yawa shi yasa aka rage farashin. Shi baya yin haka.
Haka kuma Ιabi’ar sauya ma’aikata a washegari baya yi. Wanda akasari haka Ζ΄an kwangila suke yi, in ma dai waΙanda suke da hanya ko kuma in baka yi sammako ba a Ιauki wasu a yi maka tinΖaho da cewar aikin kwangila babu jira. Akasari maginan da suke aikin kwangila suna fuskantar wannan matsin na ragin haΖΖinsu, ga hantara da kyara daga shugabaninsu. Ga kuma fitar sassafe gudun a sauyasu da wasu. Wsu na jurewa hakan kasancewar rashin aiki da ya yawaita, duk wajen da ake aikin kwangila irin na gini baya rasa matasa masu zuciyar nema a wajen. In ma sun san wani, in ma kuma haka siddan su zo neman dacewa dan samun hasafi.
Sai dai shi nasa fanin ba haka bane, Baba Ιaure akwai karamci, mutanan da ya soma aiki da su, har agama da su yake aiki. Kuma yakan ninka musu kuΙin aikinsu tare da tunatar da su muhimmancin wadata iyali. Shiyasa duk wajan da ake aikinsa zaka ga tururuwar matasa.
Da murna da komai Yusuf ya wuce gida, a hanya ya tsaya ya siyi shinkafa kwano Ιaya ta hausa, sai shinkafar tuwo rabin kwano saboda yasan Labiba na Ζaunar wainar shinkafa. Ummi da Nazira kuma ya siya musu alawa da biscuit da bobo. Wasai ya ke jin ransa ko ba komai ya fi Ζarfin gidansa. Duk da Ζasan ransa yana jin takaicin yadda suminti ya yi masa kanta a hannu tare da maida fatar hannun nasa me kausji da wani irin tauri na ban mamaki. Haka Ζafafunsa tafin Ζafar duk ya tsattsage duk kular da yake bata da man kaΙanya. Duk wannan takaicin be hanashi yin walwala ba saboda ya siyi abinda za su ci. Sai dai tun daga bakin Ζofa gabansa ya soma faΙuwa. Kafe machine Ιinsa ya yi, tare da yin shahadar Ζuda ya shiga. Take idanunsa suka sauka akan yanyyamun Ζudan da suka cika mazubin kashin yara. Da sauri ya Ιauke kai, zuciyarsa kamar ta fito dan takaici. Tana zaune a can gefe, daga ita sai Ιaurin Ζirji, ga mangwaro take sha. Ummi na kwance a Ζasa bako riga Ζuda na binta. Ga hannunta a baki tana sha, bisa dukkan alamu yunwa ta ci ta cinyeta. Da gudu ya nufoshi,
“Abba sannu da zuwa!” Sauban yaron Yaya Adamu ya faΙa yana Ιaneshi. Shafa kansa ya yi, yana jin Ζuncinsa na raguwa. Babu suturar kirki a jikinta bare kuma yasa ran za ta sakawa Ummi. Ya sake kallon Sauban yaron ya bashi sha’awa tsaf da shi. Hannunsa ya riΖe sossai cikin nasa.
“Saubahn ina Mamanka?”
Mtsss! Tsakin Labiba ya shiga kunnuwansa, ta miΖe yuu! Ζudaje kuwa suka ce sallamu alaikum. Ζauke kai ya yi. Ya soma Ζarewa tsakar gidan kallo. Ya ma rasa ta ina ne zai soma. Allah Ya yi shi da mugun tsafta. Dan haka ya zage ya gyara ko’ina tsaf duk da gajiyar daya kwaso. Bai nufi Ιakin girki ba, gudun ganin abinda zai iya sa shi amai. Ummi ya kama ya yi mata wanka, ya kaita Ιakinsa wanda yake fitar da Ζamshi mai daΙi. Daga bisani ya yi dabarar dafa musu indomie suka ci tare da ita, nan da nan ta ware tana Ιangala dariya sai ta Ιingire ta kama bacci. Sai da ya mula sannan ya nufi Ιakinta. Tana zaune kai babu Ιankwali ga tulin kayan wanki, zauri kuwa ba a magana kamar banΙakin Ζ΄an makaranta. Shinkafar ya miΖa mata da sauran canjin, ta karΙa a lallace.
“Ka fanshi kanka da…”
Kafin ta Ζarasa idanunta suka nuna mata shinkafar gida, Ζ΄ar hausa. Wata ashariya ta Ζundumo ta maka masa tare da tattara shinkafar ta jefa masa. Bata sauka ko’ina ba sai kan fuskarsa. Ta tarwatse a tsakar Ιakin. Take ya soma bin shinkafar da idanu, kwanyarsa na lissafomasa tarin wahalhalun da ya sha wajan samar da ita. Komai ya shiga zuwar masa daki-daki kamar a lokacin ya ke aikin. Zuciyarsa ta Ζuntata matuΖa karon farko ya ji yana muradin sauke fushinsa akan Labiba tun auransu. Kyawawwan maruka guda uku ya shimfiΙa mata akan fuska, yana huci ya nunata da yatsa,
“Zan juri komai Laby amma banda wulaΖanta Ζumajina!”
Daga haka ya fice ya bar mata Ιakin tana kuka da Ιura masa ashariya kamar Ιiyar maguzawa. Ashariya ta shiga auna masa kwano-kwano. Hajiya Hauwa dake kwance a kabari, ta dinga ambata tana Ιurawa zagi. Gani ya yi ba zai iya juraba ya zage kwanji ya jibgeta son ransa. Ai kuwa da himma ta tattara ta nufi gida. Amne ta dinga surfa ruwan bala’i ta kuma yi rantsuwa duk ranar da ya kuma dukkan mata Ιiya to yayyunta zasu rama mata.
Baba Ιaure ne ya nuna mata bata isa ba, ya kuma ja kunnan Labiba da kakkausar murya kan zagar masa iyaye. Tare da yi wa Yusuf Ιin nasiha mai ratsa jiki kan haΖuri da iyali. Nauyinsa ya koma ji sossai, saboda me doki ne ya koma kuturi shi da ya kamata ace ya tsayawa Labiba amma shi yake goyon bayan Yusuf. Ζima da mutuntakarsa sai ta kuma Ζaruwa a idsnunsa dama dangi baki Ιaya. Tun daga lokacin Labiba ta shiga fefan dangi, aka watsata. Da anga kina Ζ΄ar rashin kunya ga miji za a soma dangantaki da ita, har abin ya soma zama abin fitina cikin ahalin.Baba Ιaure ya tashi haiΖan, wajen gudanar da aikin kwangilarsa. Ba’a Ιauki wata biyu ba gaba Ιaya birni da kewayen garin suka san da mashahuriyar kasuwar. Saboda yadda ginninta ya soma fantsama ko’ina ka zauna batun ake yi. Wani abin burgewaa sisi bai karΙa ba na aikin ya ce sai ya kammala. Wannan ya Ζara masa Ζima da martaba a idan gwamna sossai.
A Ιangare guda kuma Ζ΄an adawa nata ΖoΖarin dakusar da hoΙasarsa, amma kuma Allah bai basu ikon yin nasaraba. Cikin watanni Ζalilan aka kammala ginin kasuwar, gwamna ya haΙa gagarumin taro tare da karrama shi da wasu cikin makusantansa. Aka bashi lambar girmamawa tare da yabawa aikinsa. Sai dai kuma kamar yadda gwamna ya buΖata shi ne, ya zo gida ya amshi kuΙin aikin kwangilarsa ba za a bashi su gaban bainar jama’a ba.
Haka taro ya tashi farin ciki cike da zuΖatan makusanta. Yusuf kansa yana cikin masu farin ciki, domin ba kaΙan ba ya dama a wannan kwangila ya samu daidai gwargwado haka duk wani matashi dake kewayen unguwar dama cikin estate Ιinsu.
Bayan sati biyu a safiyar Littinin Baba Ιaure ya yi wa iyalansa sallama. Ya shirya ya tafi karΙo haΖΖinsa kamar yadda aka buΖata. Sai dai tun safe har zuwa magarba babu shi babu labarinsa, hakama wayoyinsa basa shiga. Amne ce ta soma ankarar da mutanan gidan halin da ake ciki, domin ita Ιin mace ce mai kulawa da lamarin mijinta. Tunda ya tafi take bibbininsa a waya, balantana kuma da take tunanin kuΙi zai amso ko banza tana da kaso mai tsoka. Saidai bata samun wayar, tun abin yana cinta ita kaΙai har ta fito ta nunawa mutanan gidan wayarsa fa bata shiga. Nan fa hankula suka soma Ιagawa aka shiga cuku-cukun neman ina ya tsaya. Sai dai kash duk iya ΖoΖarinsu babu labarinsa. Kafin wayewar gari labarin Ιatan Baba Ιaure ya kewaye cikin ahalin baki Ιaya.
Baba Ζangaladima ya fi kowa shiga tashin hankali, sai dai ya fi kowa nuna musu dauriya domin shi mutum ne mai kawaici. Sai yamma suka sami zuwa wajen gwamna sai dai abin tashin hankalin an basu tabbacin bai zo ba. Tashin hankali wanda ba a samasa rana. Wannan ahali sun ga tashin hankali koke-koke kuwa babu yara babu manya. Haka suka dawo guiwa a sage duk da kwantar musu da hankali da gwamnan ya yi tare da alΖawarin sa wa a bincika. Kwana Ιaya biyu uku, babu wani sauyi, ba bu shi babu dalilinsa.
Ta Ιangaren gwamna ma kuma duk ΖoΖarinsu babu wani cigaba sai ban haΖuri da yake wa iyalan. Addu’a kuwa basu san iyakar wadda suka yi ba, suka saka aka yi. Hakama mutanan gari kowa yana nuna alhininsa. Kwanansa biyu da yini aka kira wayar Baba Ζangaladima tare da buΖatar maΖudan kuΙi kan za a badashi ko kuma zuwa washegari a sami gawarsa. Sossai hankalinsu ya tashi, domin bada kuΙin da aka buΖata tamkar durΖushewar ahalinsu ne domin gaba Ιaya dukiyarsu bata gaza hakan ba. Haka suka shiga cuku-cukun samun kuΙin amma abu ya faskara. Koda labari ya isa ga kunnan gwamna sai ya buΖaci su barshi da alhakin hakan. Sun ji daΙi karamcinsa sossai da sossai. Abinka da aikin gwamnati, ba zasu ce ga yadda aka yi ba, su dai sun wayi gari suni ganshi an kawoshi har Ζofar gida da asuba a wata baΖar mota aka tafi.
Ζ³an uwa sun cika da murna da farin ciki musamman da ya kasance lafiyarsa Ζalau, babu wani rauni tare da shi. Kwana biyu Ζ΄an uwa na jelar zuwa ganinsa, aranar kwana na uku ne suka tashi da tashin hankali sakammakon jikinsa da ya rufe da zazzaΙi sai kuma Ζafaffunsa da ya zamana basa motsawa ko kaΙan. Babu jinkiri aka wuce asibiti da shi, binciken farko likitoci suka tabbatar da an yi masa allurane mai nakasa gaΙoΙin jiki daga nan kuma sai kisa. A bayanin nasu sun tabbatar da zasu yi iya ΖoΖarinsu wajen dakatar da allurar, gwamna kansa ya shiga tashin hankali domin yana da yaΖinin don a Ιata sunansa a ka yi.
A ranar ya soma cuku-cukun nema masa visa domin tafiya egypt, cikin kwana biyu zuwa uku aka kammala komai. Tare da Baba Ζangaladima aka tafi, kwanansu biyu dai jiki ya Ζi daΙi aranar kwana na uku ya amsa kiran mahallicinsa.
Iya tashin hankali ahalin sun shiga, haka aka yi cuku-cukun Ιauko gawarsa zuwa gida nijeriya wadda ta shari tsawon kwana biyar da clearing da komai suka iso tare da rakiyar tawagar amintattun gwamnati. Cincirindon mutane ba a cewa komai saboda tsabar yawansu. Da Ζyar motocinsu da ambulance Ιin da aka turo daga wani asibitin gwamnati wadda ta Ιauko shi suka iya wucewa. Bawan Allah mai halin gaskiya da amana ko da rai ko babu yana cikin zuΖatan mutane. Koke-koke kawai ake ji yayin da Ζ΄aΖ΄ansa da kansu suka Ιauki gawar mahaifinsu zuwa cikin gidan domin haΙa shi. ZuΖata sun raunana matuΖa a wannan rana. Hajiya Amne da abokan zamanta sun zabge lokaci guda. Surukan gidan da jikoki ne ke iya taΙuka wani abu, suma Ιin a sanyaye. An shirya yin jana’izar ana idar da sallar azahar saboda Ζ΄an uwa da abokan arziΖi na nesa da suka roΖi alfarma.
Baba Ζangaladima baya iya ko magana, haka ma Yusuf Labiba kuwa sumanta uku tana farfaΙowa. Hakan ya jaza mata naΖuda gadan-gadan a ranar ta haifi cikin jikinta, yaro Ιan firit da shi bakwaini. Haka aka yi masa sutura aka sadashi da makwancinsa na gaskiya. Ba wani zama aka sake yi ba, tunda anyi na baya. Har zuwa lokacin Labiba na sashin mahaifiyarta bata koma gidanta ba. Ζ³usuf kuwa bai bi ta batunba, ganin har lokacin mutuwar bata gama sakin ahalinsu ba.
Mutuwarsa ta sanyaya jikin ahalinsu da dama. A kuma lokacin ne Zahidaht ta zo ita da Kabir da Jawwad kuma a wannan zuwane ta tubure kan bazata koma ba. Duk da cewar iyayan nasu basu tambayeta dalili ba, amma kuma ramarta ta matuΖar tsoratasu. Ta Ζanjame kamar ba wace ta bar nijeriya ba. Kowa ya goyi bayanta, da aka matsa mata da san sanin dalili sai ta nuna musu ta fison kusanci da ahalinta ne. Mahaifiyarta kam bata yadda ba, binta kawai take da ido tana fatan ta sami sararin keΙewa da ita.
Dole Kabir yana ji yana gani ya haΖura ya barta, sai dai bisa turasassawar mahaifansu ya soma neman transper domin fara aiki a Ζasarsa sakammakon ya kammala karatunsa har ya soma aiki. An yi cuku-cukun karΙar transper zuwa Ζarshan shekara ya tattara ya dawo. Dawowarsa yasa ya rage yi mata abubuwa da yawa saboda idanun yan uwa. Sai dai kuma ta yi nadamar dawowawarsu gaba Ιaya, domin sai da ta zama Ζofar data bashi lasisin Ζuntata rayuwarta. Ta hanyar kisan mummuΖen da yake yi mata.Yusuf ya yi wa Labiba abin da bata taΙa zato ba, ranar data cika sati aranar ya yanka Ζaton ragonsa ya kuma shaidawa duniya ya maidawa Ιansa sunan Baba Ιaure. Kowa ya yi matuΖar farinciki musamman Amne, nan da nan wasu suka soma kiran yaron da suna Khalifa. Wasu kuma Yusuf takwaran Yusuf Ιan Yusuf jikan Yusuf, amma kuma masu kiransa Baba baure sun fi yawa. Sai dai Labiba ta fututtuke tace Khalifa sak za a kira mata Ιa.
Kwanci tashi mutuwar ta bi jikinsu gaba Ιaya, sai dai alhini irin na sabo. Amma banda Baba Ζangaladima dan shi kamar zuΖarsama ake kullum cikin rama. Haka su Yusuf zasu tasashi gaba su yi ta bashi baki.
Lokacin da Labiba ta koma gidanta sai ya zamana Ζazanta ta Ζaru, da an yi magana ta hau zuba rashin kunya tana faΙin ba a tausayinta ba a ganin gwarnai ta yi. Tun Yusuf na kauda kai har ya soma kai Ζararta wajan mahaifinsa. Saidai kullum bayan Labiba yake bi, bawai dan wani abu ba, sai dan tuna cewa kadda dangi su ce Ζasa ta rufewa mahaifinta idanu ana yi mata badaidai ba.
Shi kuma duk ΖanΖantar laifi idan ya aikata mata, zata kira Amne da Khamis ta shirya Ζarya da gaskiya su kirashi ba tare da jin ta bakinsa ba su ci mutuncinsa son ransu. Yusuf sarkin haΖuri sai dai ya bada haΖuri, amma kuma abin na cin ransa gaba Ιaya ya zabge ya rame. Ga wata uwar Ζasumba da ya ajiye, haka kuma fatarsa ta Ζara duhu idanunsa sun zurma ciki sossai sun fidda wani kogo daya Ζara fito da aihinin sirrintakar hancinsa.
Cikin ΖanΖanin lokaci raini mai Ζarfi ya shiga tsakaninsa da Labiba, bata shakkar ta zageshi a gabansa hakama gaban abokansa da Ζawayenta. Har abin tinΖaho ya zamo mata sai yadda ta ke so ake yi agidan. Abinci idan ya kawo mata Ζ΄ar hausa ba zata dafa ba, idan kuma Ζ΄ar gwamnati ce to ba zata girka mai daΙi yadda zata yi armashi ba. Hasalima abinci Ζarshansa babbakewa cikin tukunya musamman data soma chats ya zamana yana Ζara Ιauke mata hankali. Sangarta kala-kala, wandunan kashin yaro kuwa bata wankewa sai sun taru ta kule a leda ta watsar a bola. A haka Khalifa ya shekara Ιaya da watanni Ummi kuma nada shekaru biyu da watanni.
***
MUSABABI.
A haka zamansu ya miΖa, sai dai yau da gobe taΖi gaban wasa. Duk Ζumbiya-Ζumbiyar Yusuf sai da dangi suka fahimci baya jin daΙin zama da mstarsa. Saida ya zamana babu wanda bai san matsalarsu ba. Duk inda aka zauna taro manya ciki kan ΖoΖarin bata shawara, musamman kan Ζazanta amma Ζarshe sai dai ta zagesu tas ta Ζara gaba abinta. Cikin tsakanin aka yi musu rabon gadonsu, dukiyar da aka samu ta girgiza mutane da dama, basu taΙa tsamanin dukiyar mahaifin nasu takai hakanba.
Kowace Ιiya mace saida ta tashi da naira miliyar arba’in da gida guda Ιaya banda kadarori. Shi kansa Baba Ζangaladima abin ya shallake tunaninsa, bai taΙa kawo Ιan uwansa ya kai haka ba. Su Khamis nan da nan aka shiga faccaka da kuΙi, masu wayau ciki suka kafa sana’a wasu kuma suka shiga sharholiyarsu yadda suka ga dama.
Zahidaht na Ιaya daga cikin waΙanda suka bada dukiyarsu a juya musu, Ζwarai taso bawa Yusuf ya juya mata domin shi ne koma baya acikin ahalinsu amma mahaifiyarta ta fututtuke ta nuna bata lamunta ba. Sai dai hakan baisa ta fasa niyyarta ba, a Ιoye ta siya masa sababbin kekuna aka gyara shagon dayake haya aka zuba masa su. Tare da bashi naira dubu hamsin ya kafa jarin kayan Ιinki a shagon. Ranar ya yi kuka irin wanda bai taΙa yi ba, ta kuma roΖi alfarmar ya zama sirri daga ita sai shi da mahaifinsa da yaya Asabe suka sani. Sauran kuΙin kuma ta dunΖule ta miΖasu ga mijin Yaya Asaben ta ce ya juya mata, anyi takarda da shaidu da komai kuma gaban jagororin gidan.
Wannan abu data yi ya Ζuntata ran Kabir kamar ya yi hauka, domin shi ya baje sai lallaΙata yake yi, salon kulawa kala-kala yana tsarin ta gama zuwa hannu har mota sai ta siya masa. Aikuwa ranar data miΖa dukiyarta ga Yaya Adam kaΙan ne bai yi hauka ba, ga Jawwad na Ζara tunzurashi. Ranar yini suka yi a club ya sha syrup ya yi tattul ya nufo gida, duka ya yi mata na fitar hankali tare kyakkyawan gargaΙi kan ta amso kuΙin amma ko a Ζafar silifas Ιinta kuma ba wanda ta kai wa Ζara. Ta yi alΖawarin tunda Yaya Asabe bata goyi bayanta ba, ba zata taΙa buΙe baki takaiwa wani Ζararsa ba. Duk ranar da ubangiji ya nufa zasu fuskanci wa suka bata matsayin miji to zasu fuskanta ba tare da takai Ζara ba. Ζila hakan ya ankarar da su KUSKURAN da suka tafka daga su har ita. Musamman data ga yadda lamarin Labiba da Yusuf yake tafiya sai ya Ζara mata Ζarfin guiwar cewa, ko ta kai Ζara dai bayan Kabir za a bi.
Ζangaren Labiba kuwa, duniya sabuwa dal gareta, gidan da suke zaune ciki nan ne ya zama gadonta. A ranar da aka mallakamata shi a ranar ta tsira Yusuf ya bata takardunsa domin suna hannunsa. Fes ta ke jin ranta. Cikin ΖanΖanin lokaci ta dinga wasa da dukiya. Gwala-gwalai ta siya, a je gidan biki a yi ta iyayi ana Ιaga kai. Ta sake kayan Ιaki biy biyu, wato ya zamana two bedroom. Sai dai kayan basu je ko’ina Ζazanta ta nakasusu, musamnan da ya kasance na dubai ta saka. Su kuwa suna buΖatar kulawa. Haka kayan kallo da duk wasu nau’in kayan amfanin gida ta sauyasu kamar wata amarya ga danΖareriyar waya.
Ζawaye kansu sababbi ta sake Ζ΄an yayi. Ganin tana Ιarnar kuΙi ne, Amne ta Ζwace kuΙinta ta damΖawa Khamis yayanta aka soma juya mata da yake harkar gwala-gwalai yake yi. Kwatsam Zahidaht ta je mata da shawara kan me zai hana ta ba wa Yusuf kuΙinta ya juya mata, ranar da uwaka ubanka suka rabu. Har tana goranta mata me ya hana ita ta ba nata mijin tata dukiyar? Wannan abu ya ba ta mamaki Ζwarai da gaske, domin me Ιaki shi ya san inda yake masa zuba. Ta sha alwashin badan alΖawarin da ta yi wa zuciyarta ba, da sai ta bambancewa Labiba tazarar dake tsakanin Kabir da Yusuf.
A taΖaice dai Labiba sai ta miΖe Ζafa ta sake sabon zubin rashin mutunci. Girki bata yi saita ga dama, take away take yi ita da yaranta. Hidimar dangi kuwa idan ana yi matuΖar bata Ζ΄an Ιakinsu bace sai ta mula take zuwa. Yusuf ya zame mata hoto bashi da Ζ΄ancin tsawatar mata zata ci zarafinsa, agaban Ζ΄aΖ΄ansa. Tun Ummi bata fuskanta har ta soma fuskanta domin ta yi wayau ta shiga shekara ta biyar Khalifa kuma huΙu. Idan ta zauna a waje sai ka ji tana,
“Ummunmu tana sa babanmu kuka!”
Idan yaro ta samu suke wasa sai dai ka ji tana tambayarsa,
“Mamanka tana sa babanka kuka?”
Haka ma idan babbane ba take masa wannan tambayar. Ranar data yi wa Nazira tambayar a gaban Yaya Asabe ba Ζaramin kaΙuwa Yaya Asaben ta yi ba. Ta ja Labiba ta dinga yi mata faΙa tare da nusar da ita KUSKURAN da take aikatawa na yin komai gaban yara. Ta nuna kamar ta ji, amma koda suka dawo gida mugun duka ta yi wa Ummin wanda ya fusata mahaifinta ya zage Ζarfinsa ya naΙa mata nasa dukan. Ai kuwa ta ji jiki matuΖa.
***
Kamar yadda muka sani a al’ada Ζaratowar azumi kowane magidanci yana hoΙΙasa a gidansa. Hakama Yusuf ya kasance mai tsayuwa tsayin daka wajen ganin ya wadata gidansa, sai dai wai a banza man kare in ji Ζ΄an magana. Ko kaΙan bai ΙaΙa Labiba da Ζasaba hasalima a raine ta karΙi kayan. Har aka yi azumi huΙu biyar zuwa goma bai san samun abin buΙa baki daga gidansa ba, sai dai Asiya yarinyar da yake haya a shagon gidansu tana ΖoΖarin kawo masa kunu Alla bashi shi kuma yana siyen Ζosai da dabino. Sossai yake mutunta Asiya da mahaifiyarta bisa karamcinsu.
Lokacin da aka shiga hidimar sallah sai ya zamana aiki ya soma rincaΙewa Yusuf, Ιinkuna sun soma yi masa yawa baya samun dawowa da wuri, amma abin takaici duk lokacin da zai dawo sai ya samu ta garΖame gida da sakata. Idan ya yi magana kai tsaye zata ce,
“Gidanka ko nawa?”
Tun ba ajin kansu game da hakan har ya kai ga ya kai Ζararta, sai dai ga mamakinsa kadda baki Baban nasa ya yi ya tambayeshi,
“Yusuf tun nawa ka ke fita?”
Ya bashi amsa da cewar,
“Baba asuba ne”
“Ka dawo nawa”
Sai da ya yi jim, sannan ya amsa,
“Ina kai biyu saboda yanayin aikin namu!”
Kai tsaye mahaifin nasa ya maida dubansa kanta,
“Labiba Ζarfe nawa ki ke so ya dawo?”
Babu kunya ta amsa,
“ko bai sha ruwa gida ba Baba kadda dai ya wuce tara!”
“Yusuf”
Mahaifinsa ya kirashi da kaushin murya, ya amsa kansa a Ζasa yana jin wani irin raΙaΙi da Ιaci tun daga Ζasan zuciyarsa,
“daga yau idan ka wuce tara a waje Labiba zata rufe gidanta!”
Ζas! Gabansu ya faΙi su duka, Labiba maimaita kalmar take cin ranta,
‘Gidanta! Gidanta!! Gidanta!!!’
Tana ji kamar Baban magana ya faΙa mata, amma suita dake tare da yi masa godiya suka nufi gida. Tun daga wannan rana Labiba ta sake samun lasisin cin fuskar Yusuf son ranta. Haka aka kusa gama azumi gaba Ιaya yana kwannan shago, ya zamana tun kafin maΙinka su soma kwanan shago shi ya soma. Saboda idan ya dawo, sai ya shefe mintuna sittin yana bugu da kiran waya amma ba zata ko Ιaga ba. Kuma ba zata buΙe masa ba.
Post a Comment for "WATA MACE CHAPTER 3 BY SANA S MATAZU"