WATA MACE CHAPTER 3 BY SANA S MATAZU WATA MACE CHAPTER 3 BY SANA S MATAZU Www.bankinhausanovels.com.ng SAUYI. Haihuwar Labiba ta kawo sauyi da yawa a rayuwar aurenta da Yusuf. Sossai zahirin hallayarta ta fito kowa ya sani. Muguwar ƙazantar data zame mata jiki ta bayyana. Ɗakinta baya zaunuwa saboda zauri ga ƙarnin miyau. Domin tana tashi daga bacci shi take soma tsartarwa a jikin bango. Tun yana kauda kai har ya zamana ya soma tankawa amma babu sauyi ko kaɗan sai ma izgilanci da rainin wayau data tsiri yi masa. Hakan ya asassa musu rabuwar ɗaki kowa ya zamana yana da mallakinsa. *** Duk abinda ya ke faruwa game da ƙazantar Labiba Amne ta sani sarai, amma bata taɓa kadda baki ta yi mata magana ba hasalima hakan ya yi mata yadda take so ko ba komai Yusuf zai ƙara ƙuntata da baƙin ciki. Watan Ummi goma a duniya Allah Ya sake bata rabon ciki, tabbas samuwarsa ta ƙara asassa komai na rayuwarta. Iskanci kala-kala da an yi magana ta ce cikine. Tun ba ajin kansu har ya zamana iyayensu maza sun soma shiga cikin la…