WATA MACE CHAPTER 2 BY SANA S MATAZU WATA MACE CHAPTER 2 BY SANA S MATAZU Www.bankinhausanovels.com.ng Kamar yadda me karatu ya sani a baya, Yusuf ɗa ne ga Baba Ɗangaladima, abin soyuwa ga kowa tun yana ƙarami haka har girmansa. Sai dai Yusuf ba shi da nasibi akan komai. Duk ƙaunar Baba ɓaure na Yusuf ya yi zurfin karatu abin ya faskara. Sau biyar yana faɗuwa jarrabawar gama secondary ƙarshe dai sai Jawwad ne ya zana masa. Shi ma ba asami wani abin kirki ba. Hakan yasa Baba ɓaure ya ja shi jikinsa ya ɗorashi harkar kwangilolinsa. To shi ma dai tana kasa tana dabo. Yau riba gobe faɗuwa, babu wani cigaba da aka samu. Daga faɗuwa sai ayi aiki a sami matsala. Gona kuwa ko ya noma ba a samun abin kirki. Akasari ma ƙwari ne suke cinye shukar tun kafin ta yi nisa. Tun abin baya damunsu har ya soma damunsu. Kowa a zuri’arsu yasan da wannan TAMBARI a tare da Yusuf. Gori daga shi har mahaifiyarsa suna shan sa, sai dai kasancewarsu mutane masu haƙuri ko ɗaga kai basa yi bare su tanka. Tun ana yi a bayan idanunsu ha…