WATA MACE CHAPTER 2 BY SANA S MATAZU
WATA MACE CHAPTER 2 BY SANA S MATAZU
Www.bankinhausanovels.com.ng
Kamar yadda me karatu ya sani a baya, Yusuf Ιa ne ga Baba Ζangaladima, abin soyuwa ga kowa tun yana Ζarami haka har girmansa. Sai dai Yusuf ba shi da nasibi akan komai. Duk Ζaunar Baba Ιaure na Yusuf ya yi zurfin karatu abin ya faskara. Sau biyar yana faΙuwa jarrabawar gama secondary Ζarshe dai sai Jawwad ne ya zana masa. Shi ma ba asami wani abin kirki ba. Hakan yasa Baba Ιaure ya ja shi jikinsa ya Ιorashi harkar kwangilolinsa. To shi ma dai tana kasa tana dabo. Yau riba gobe faΙuwa, babu wani cigaba da aka samu. Daga faΙuwa sai ayi aiki a sami matsala. Gona kuwa ko ya noma ba a samun abin kirki. Akasari ma
Ζwari ne suke cinye shukar tun kafin ta yi nisa. Tun abin baya damunsu har ya soma damunsu. Kowa a zuri’arsu yasan da wannan TAMBARI a tare da Yusuf.
Gori daga shi har mahaifiyarsa suna shan sa, sai dai kasancewarsu mutane masu haΖuri ko Ιaga kai basa yi bare su tanka. Tun ana yi a bayan idanunsu har ya kai ana yi gabansu. Sai ya zamana Yusuf ya soma ja baya da Baba Ιaure sossai. Ya sha ganinsa idan zai fita yana sa yara nemansa haka zai laΙΙe saboda mudun suka fita tare abu ne mawuyaci bai bashi kwangila ba, kuma ba a samun nasara sai faΙuwa shi yasa ya zaΙi nisa da shi fiye da kusancinsu. Ya fi ganewa ya fita ya yi buga-bugarsa kamar ba Ιan cikin Ιan saΙalo estate ba. Bai cika shiga cikin Ζ΄an uwansa samari ba, rayuwarsa ya ke yi shi kaΙai. Kama daga kan dako, aikin gini koyon Ιinki babu wanda ba ya yi, duk kuma abin da ya samu yakan yi ΖoΖarin ya raba ya siyi wani abu ya kai cikin gidan. Wannan na Ζara masa martaba da mutuntaka sossai a idanun masu mutuntakar gida.+
***
Zahidah Ιiya ce a gidan Baba Ιaure. Yarinya ce mai tsanin natsuwa da haΖuri ga sanin yakamata. Akasarin rayuwarta tafi yinta ne Ιangaren Baba Ζangaladima wajen Hajiya Hauwa. Ko kuma gidan surukarta Yaya Amina matar Adam babban Ιanta. Hakan yasa suka shaΖu matuΖa da ita, hakama Yusuf akwai shaΖuwa tsakaninsu. Tana da kaifin ΖwaΖwalwa sossai ga wayau da kuma girmama manya. Hajiya Hauwa ta sha hasashen a haΙa auranta da Yusuf kamar yadda aka saba haΙa auratayya a danginsu. Sai dai da yake yanzu zamani ya ja, sukan bari yaran su haΙa shekaru shatakwas cif lokacin sun kammala karatun gaba da primary. Badomin komai ba sai dan Ιarakar da suka soma samu na shigowa cikin ahalin na dojewar wasu a wajen haΙin. Alla bashi sai yaran su haΙa kawunansu da kansu, su kuma su aurar dasu amma babu batun ka aure wata a waje. Su kuma mazan lokacin ko sun gama karatu ko suna dab da gamawa.
Wannan sauyi da aka samu Ζwarai shi ya daΖilar da burinta na son a haΙata da Yusuf. Zahidah mace ce mai Ζulafuci, idan tasa abu aranta sai Allah. Shiyasa kaf sa’aninta ta rugasu kammala karatunta na gaba da primary. Tsabar ΖoΖarinta, bata isa zana jarrabawa ba, aka yi mata jumping (tsalake). Haka kuma ta haΙa saukarta hadda. Tana da burin cigaba da karatu sossai. Kowa ya son burinta, dan da ya wa agidan sukan yi mata laΖabi da *Ζ³AR BOKO*. Kuma takan amsa kai tsaye ba tare da shakka ba, domin tasan akwai tsarin cigaba da karatu bayan aure acikin zuri’arsu.
Mace ce mai tsanin tsafta da son kwaliya, Ζunshi kafin wani ya disasshe anyi mata wani. Saboda zaryar gidan Ζunshi ta koyi yankan salatif kala-kala wanda har ya zame mata sana’a kuma take samu da shi matuΖa. Dan ko a iya cikin zuri’arsu kuΙin da ta ke samu da salatif Allah Ya yi yawa da su. Wasunsu na ganin kamar wahalar banza take yi, amma ita kaΙai take sanin nishaΙin da take ji a tare da ita idan tana aikinsa. Domin ta haΖiΖance zana shi baiwa ce kuma wanda ubangiji ya so yake bawa. Dan haka tun abin yana damunta har ya bar damunta. Masu manyan sana’ar da yawa sun sha zuwa wajanta rancen kuΙi, takan yi murmushi idan ta tuna su ne gaba wajan kushe hikimarta.
STORY CONTINUES BELOW
***
Jawwad shi ne kaΙai Ιa namiji a gidan Baba Iro. Baba Iro kaf Ζ΄aΖ΄ansa mata ne, ya yi aure-aure ya kai goma domin Allah Ya bashi Ιa namiji amma duk matan da ya aura basa rufe wata goma suke haihuwa. Sai dai kash babu wadda ta haifa masa burinsa sai Ζ΄ar uwarsa Sadiya. Wadda kafin ya karΙi auranta an sha Ζwarbai da shi. Lokacin da ta haifi Jawwad babu irin Ιarnar kuΙin da bai yi ba. Sadiya tana takaicin yadda Ζiri-Ζiri ya ke nuna ya fi son Ιa namiji akan mace. Duk da kasancewar Jawwad ya taso a tsakiyar mata Ζ΄an uwansa hakan bai hanata ΖoΖarin bashi kyakkawar tarbiya ba. Sai dai kuma mahaifinsa ya Ιata komai ta yadda ya dinga fifitashi kan komai a kan Ζ΄an uwansa. Duk wata kaddara da ya mallaka tun Jawwad na Ζarami ya maida sunansa akai.
Duk inda zashi to tare da shi yake tafiya. Ζ³an uwansa sun sha nuna masa kuskuran abinda yake yi amma Ζarshe da faΙa suke rabuwa. A haka yaro ya tashi a sangarce, babu kwaΙa babu harara. Jawwad Matashi ne mai jini a jika kuma Ιan Ζwalisa. Sai dai tun tasowarsa fitinanne ne baya jin magana. Tun yana shekara goma sha takwas ya Ζware a bin mata da kuma tare yara a hanya yana ΖwaΖΖularsu. Wannan kowa ya san shi da wannan TAMBARIN a zuri’arsu. A silarsa iyayansu suka so dawo da al’adar aurar da yaransu suna shekaru goma takwas maza amma hakan bai samu ba. An yi masa aure ya kai sau uku amma kuma baya shafe wata biyu da matan yake sakinsu. Hakan yasa aka haΖura aka zuba masa ido ana binsa da addu’a domin sun haΖiΖance duk zuri a sai a sami wari guda.
***
Kabir ya fito ne daga zuri’ar Baba Muttaka Ιan uwargidansa ne Hajiya Fure. A zuci fir’una a fuska Musa kenan. Kafatanin hallayar Jawwad irin ta Kabir ce sai dai kuma ga wanda ya san baΙinin Kabir kenan ga wanda yasan zahirinsa kuwa ba zaka taΙa cewa yana da wani aibu ba. Yana da suffar kamala sossai, akwai shi da iya taku da nutsuwa ga tausassa kalamai. Idan yana magana da kai dole ka ji ya burgeka, duk wani salo na tausasawa ya sani. Allah ya bashi kaifin fikra da balagar harshe. Shi yasa Ζ΄an mata da yawa suke rubibinsa. Akwai masu kuka akansa.
***
Labiba, Ιiya ce ga Baba Ιaure kuma ita ce Ζarama a gidan cikin mata, sai dai mace ce me ji da kanta. Ζ³ar Ζwalisa ce ta Ζin Ζarawa. Bata da kunya ko kaΙan, bata ragawa na sama da ita haka ma Ζananun dake Ζasanta. Yanzu yaro zai mata abu bako kunyar idon mahaifiyarsa zata kwafΙeshi. Gata gaΙuwa ko kusa bata iya magana ba, duk yadda tazo bakinta haka zata furzota ba tare data taunata ba. Ba namiji ba hatta mace Ζ΄ar uwarta takan jinjina wautarta idan ta yi wata maganar. Bata ganin kowa da gashi musamman yadda take la akari da mahaifinsu ne ginshiΖin *ΖAN SABALO ESTATE*. Sangarta take zubawa son ranta kuma mahaifiyarta na Ιaure mata Ζugu.
Labiba baΖa ce amma kuma ta kwaso kyawun mahaifiyarta wadda ta kasance Ζ΄ar asalin garin sumalia. Tana da kyawu daidai gwargwado. Ga kuma cikar hallita. Duk wata budurwa mai ji da kanta a estate Ιinsu bata kama Ζafarta ba. Duk gayun Labiba bata san idan ta cire kaya ta sauya ta Ιauke ba, mahaifiyarta ko kuma yaran da ake riΖo a Ιakinsu sa’aninta wanda Ιakin kwanansu Ιaya su suka san wannan hidimar. Bata san ta yi kwaliyya ta kwashe kayan data yi amfani da su ba. Bata san ta ci abinci ta Ιauke kwano ba.
Tun suna kai Ζara har suka haΖura domin Amne bata goyon bayansu. Haka batasan wanke kai ta yi kitso ba, zadai ta kimma acuci akanta yana sumbuΖa wari ba damuwarta bace domin zata buleshi da turare. Babu tazara tsakaninsu da Zahidah sa’anin juna ne. Sai dai kowa hidimarsa yake, idan sun haΙu to anzo taron cikin gida ne ko kuma islamiyya domin Zahidaht bata son raini ko kaΙan. Bayansu akwai Ζ΄an mata shida masu irin shekarunsu. Husnah, Amira da Maryam da MashiΙa da Zuhuriyya sai kuma Kamila.
***
Kwanci tashi babu wuya wajen ubangiji, Ζarshan shekara na gabatowa haka kuma batun shirya-shiryan aurar da Ζ΄an matan *ΖAN SAΖALO ESTATE* ya soma kankama. Ko wace nada zaΙinta in ka Ιauke Zahidaht da Labiba. Haka ma matasan kowa da zaΙinsa idan ka Ιauke Kabir da Yusuf da kuma Jawwad. Wanda Jawwad da Kabir ana dakon fitowar jarrabawarsu ne, da suka zana ta zangon karatunsu na biyu. Awannan lokacin da yawa basa lissafi da Jawwad a auran saboda bama shi da wadda take sauraronsa cikin zuri’arsu. Kasancewar a lokacin ya saki mata guda biyu, Ιaya Ιiyar Baba Khamis Ιaya kuma Ιiyar Baba Muttaka. Wanda abin har ya so taΙa zumuncinsu. Kasancewar duk matan da ya saki na baya sun yi aure amma waΙanan sai auran nasa ya zame musu TAMBARI kwata-kwata babu mai sha’awar auransu cikin zuri’ar.
Kabir kuma yana Ιaya daga cikin waΙanda gwamnan dake ci alokacin, ya nemi alfarmar a barshi ya tafi Ζaro karatu. Baba Ιaure bazai iya karya wa gwamna bille ba, abokinsa ne tun yarinta hakan yasa ya amince da buΖatarsa ya tara sauran Ζ΄an uwansa suka yi shawara aka haΙa da Jawwad aka biya masa suka tafi. Karon farko da wani matashi wanda bai taΙa aure ba a zuri’ar ya tafi Ζaro karatu, kuma ba cikin Sakwwato ba Ζasar waje. Daidai lokacin da ake shirin aurar da Ζ΄an matan gidan su kuma sun zo gida ne hutun jarrabawa. Iyaynsu kuma suka yanke a dakata jiran jin yadda sakkamakon ya yi kyau, alla bashi sai a Ιaura auren su juya da matan.
Wannan fifiko da suka samu ya Ζarawa Jawwad da Kabir girman kai da kuma samun wani fili a zuΖatansu na cewa su Ιin sun kai. A Ιage suke kallon kowa, sun raina da yawa cikin matasan gidan musamman Yusuf. Babu yadda Jawwad da Kabir basu gwada hikimarsu ba, ko Labiba zata amince da buΖatarsu domin suna ganin su suka dace da Ζ΄ar Ζwalisa irinta amma ta shafawa idonta kwalin audi ta nuna bata san suna yi ba. Ζangaren Jawwad dama shi soyayyar zamani yake biΙa, daya ga ba fuska sai ya haΖura. Shi kuwa Kabir zahiri da gaske yake son auranta shi ma dai babu fuska dole ya haΖura.
Daga gefe guda kuma, Zahidaht ta makance akan soyayyar Kabir, ba dan komai ba sai dan tunaninta shi ne daidai da ita. Ζan gayu ga Ζwalisa ga kuma ilmi. Koba komai zai tuntuΙawa mafarkinta tabbata na cigaba da karatu. Sai dai ta kasa tunkararsa koda wasa, domin baya wasa dasu kwata-kwata. Tun ana zunΙenta a gida taΖi fitar da tsayayye, duba da yadda Salihu yake sonta har aka soma yasar musu da habaici a tsakar gida ita da mahaifiyarta. Hankalinta ya tashi matuΖa, musamman da mahaifiyarta ta soma sakata a Ιaki tana nuna mata ta rufa mata asiri ta karΙi tayin Salihu. Sossai ta shiga damuwa, zuciyarta ta soma aminta da karΙar Ζudurin mahaifiyarta kodan sama mata natsuwa.
Ζangaren Yusuf kuwa baya kula kowace mace cikin ahalinsu da sunan so, yana ganin wace ce zata so shi a hakansa? Hakan yasa koda wasa bai Ιorawa kansa kula *WATA MACE* cikin zuri’arsu da sunan soyayya ba, in ka Ιauke gaisuwar mutuntaka. Hakama mahaifiyarsa tana goyon bayansa. Mace Ιaya ce ya ke hango nutsuwarta ta kwanta masa, sai dai koda wasa baya tunanin zata karΙi tayinsa shi yasa ya haΖura.
Gaba Ιaya ya maida hankalinsa ne ga sana’ar hannu da kuma nacin karatun al-Ζur’ani. Kaf zuri’arsu babu mai baiwar karatunsa, shi yasa ya ware aji guda na Ζanannun yara masu rasowa yana koyar dasu Ζira’a. Kuma alhamdullilah, duk wata gasa ta karatu acikin garin Sakwato matuΖar aka Ιauki yaran da yake koyarwa to *ΖAN SABALO* sukan yi nasara. Ya goge a fannin sanin alΖur’ani da Ζa’idojinsa.Safiyar wata Asabar garin Sakwato an tashi da wani irin muku-mukun sanyi. Labiba na Ζunshe cikin lallausan bargonta, gaba Ιaya Ζ΄an Ιakin da suke kwana tare sun farka, wasu na Ιakin girki wasu kuma na cikin gida. Wasu kuma da yawa suna islamiyya. MiΖa ta yi tare da sako Ζafaffunta Ζasa, Ιan turo baki ta yi ta yatsina fuska. Kai tsaye banΙakin Amne ta shiga, cikin mintun ta fesa wankanta tare da wanko baki ta fito tana taku Ιai-Ιaya. Sai da ta shari lokaci wajen shiryawa daga bisani ta fito babban fallo. Bata sami kowa ba hakan kuma bai dameta ba, duk da tasan ta karya dokar zuwa islamiyya haka ta kaΙa kai ta tafi bayan ta karya kumalo.
Tana gab da shiga makarantar gabanta ya yanke ya faΙi, ba dan komai ba sai dan tunawa da yau kowace rana ce. Ilai kuwa tana saka Ζafa cikin makarantar ta haΙa idanu da mahaifinta. Harara ya wurga mata ta sune kai Ζasa domin tasan laifinta. Ita shaf ta manta yau ne Ζ΄an ajin Zahidaht da kuma ajin Yusuf suke gwajin gasar karatu, Ζa’idar islamiyyar ne duk Ζarshan wata sukan shirya gasar karatu daga wannan aji zuwa wannan aji. Ajin da ya yi nasara zai kara da dukkan ajujjuwan idan ya yi nasara shi ne ajin da zai jagoranci estate Ιinsu a gasar da suke fita ta Ζarshen shekara. Da babu abin da zai sa ta shigo makarantar ma, saboda tasan rana irin wannan tana haΙa duk wani uba na cikin zuri’arsu. LallaΙawa ta yi zata zauna sai jin sautin muryar mahaifinta ta yi,
“Yusufa ga Labiba can yi mata bulala!”
Da hanzari ta Ιago kanta, gaba Ιaya sai ta muzanta yadda idanun sa’aninta na yawo a kanta. Har ta hango Husnah Ιiyar Baba Mu’az da Maryam suna Ζunshe dariya. Wani takaici ya kamata, kwata-kwata ta tsani abinda zai muzantata cikin sa’aninta. Ga mamakinta sai ta riski sautinsa cikin sanyin da ya zame masa Ιabi’a,
“Baba ai Labiba bata makara, ayi mata uzuri”
Sai ya Ιauke kai ya cigaba da abinda yake yi, kamar ba shi ya yi furucin ba. Gaba Ιaya kuwa su Husnah suka rakashi da idanu suna mamakinsa. Saboda sun sa yadda take kayawa tsakaninsa da ita matuΖar ya daketa shi yasa ma ya sahalewa kansa dukan nata.
“Bani bulalar!”
Ya furta a fusace, jiki a sanyaye ya miΖa masa, da kansa ya taso har inda take ya yi mata bulala goma, lafiyyayu. Tun tana daurewa har ta soma kuka don ta tsani duka. Ai kuwa filin wajen ya yi Ιif ana jin shassheΖar kukanta. Sai ajiyar zuciya take saki. Daidai lokacin Kabir da Jawwad suka Ζaraso wajen, akan idanunsu aka yi komai har gwalo ya yi mata da suka haΙa idanu da shi.
Iyayyen suka shiga gaisarwa Ιaya bayan Ιaya, har suka zo kan Baba Ιaure idanunsa akan Jawwad ya sha aski irin wanda ake kira hana sallah. Ga uban zanzaro da Ζaramar riga iya Ζugu. Kabir kuwa shigar shadda ya yi da hula zanna bukar suna taku ΙaiΙai. Yana shirin tanka musu ne daga gefe kuma cikin taro, aka gabatar da Zahidaht domin gabatar da buΙe taro da karatun alΖur’ani. Wannan dalili ya dakatar da Baba Ιaure daga Ζudurinsa na hukunta kowannansu, sai dai ya Ζuresu da idanu yana ajiye kowanensu a hukuncin da ya ke hangen ya dace da shi ciki kuwa hadda Zahidaht da sautin karatunta ya dira a kunnunwansa cikin taushi da nutsuwar murya.
Ζangaren Labiba kuwa, bayan ta gama shan kukanta duk fuska ta dame da kwaliya. Da mamaki ta dinga satar ajiye kallonta a saitin Yusufa, ba yau ba ya saba tareta a makara ya yi mata alfarma ba wai saboda wani abu ba. A rayuwar Yusuf ya tsani ya daki yarinya ta tafi tana yi masa ΖunΖuni. Ita kuma Ιabi’arta kenan, duk da cewa bashi da zafi kan sauran Malam amma ya salaΙewa kansa dukan Labiba tunda ya fahimci bata da kunya. Amma bata taΙa kawo zai tsallake umarnin mahaifinta a kanta ba. Kanta a Ζasa har aka gama taron baki Ιaya, Ζ΄an ajin Yusuf ne a kan gaba sai kuma na Zahidaht da suke bi musu baya.
Ba a tashi taro ba, sai da Baba Ιaure ya sami matsaya kan hukuncinsa. Ya kuma yi na’am da hakan, karon farko da yake ji aransa zai karya dokar da suka gindaya a zuri’artasu. Iyaye da dama sun yi jawabi mai Ζayatarwa, tare da nuna jin daΙi da kuma godiyarsu ga Yusuf. Daga bisani aka sallami kowa tare da kyaututtuka ga Ιaliban da suka yi nasara. Sai kuma sanarwar Ζarshe ta taron family da za a gudanar bayan azahar.
Jiki a sanyaye Labiba ta miΖe zuwa cikin gida, bata yadda ta jera da sa aninta ba, tunda yau sun sami abinda suke so kanta. Da Kabir ta soma karo,
“Su Laby manyan mata!”
Ya furta yana dariyar shaΖiyanci, sunan da yake kiranta da shi kennan, kuma yara da manya sun kama, wasu kan ce Yaya Laby, wasu Anti Laby wasu kuma Laby Ιin kai tsaye. To ita ma dake uwar iyayi ce sai take amsawa duk da Amne na masifar sunan. Bata biye masa ba ta yi gaba abinta. Sai dai kuma tana shiga babbar mahaΙar shiga gidan ta sami su Husna ana hira da shewa, ana ganinta kuma aka yi Ζusu! Bata raba Ιayan biyu da ita suke, Ιauke idanu ta yi ta hangi Zahidah na sawa Yaya Amina Ζunshi ta Ζarasa,
“Kai ya yi kyau! Zeedat zaki yi min ni ma?”
Ta furta tana tsaresu da idanu,
“Laby baki da kunya wallahi, ko ki gaishe ni kin wani tsayamana akai”
Ade ta furta tana zare idanu, yaya Asabe ta yi murmushi tana auna gajen haΖuri irin na matan yayyun nasu. Shiyasa duk Labiban ta bi ta rainasu bare kuma Amne na Ιaure mata Ζugu. Ilai kuwa, yaya Asaben kaΙai ta gaisar, don duk tsaurin idonta tana raga mata, bata wasa da yaro gata da kyauta abin da bai rufe mata ido ba. Sai ma juyawa da ta yi, tana Ζara nanatawa Zahidaht zata yi mata Ζunshi, ita ma dake Ζ΄an miskilancin na kanta kai kawai ta Ιaga mata. Be dameta ba, ta wuce tana jin yadda suke mata cari. Tana shiga ta sami Hajiya Muwaddah da Amne na haΙe kayan da za a raba wajen taro na ci.
Zama ta yi ta jefa hannu a robar cake ta hau tauna tana lumshe idanu, bata tantama wannan aikin Mamarsu Yusuf ne, shi yasa kullum take dakon zuwa gaisheta da safe ko ba komai takan fito da tsabarsu tunda sana’arta kenan kuma ta Ζware sossai. Kamar an mintsineta ta turo baki, ta hau bawa Amne labarin abin da Babansu ya yi mata. Ai kuwa Amnen ta shaΖa, amma tasan ko giyar wake ta sha ba zata ce don me ba. Sabida ita kanta ya sha jan kunnanta kan makarar Labiba, duk cikin sa aninta ita kaΙai ce bata yi sauka ba, saboda fashi da latin islamiyya. KaΙa kai kawai ta yi, Hajiya Muwwadah ta yi Ζwafa,
“Ina ma Yusufan ya bugeki da yagane!”
“Mama ai shi yana da kirki, ni ba ya dukana ba fa ko makara na yi a islamiyya. Shi kam matarsa ta huta wallahi yana da sanyin hali”
Karaf! Sautin maganar ya sauka akan kunnuwan Baba Ιaure. Ita kuwa Laby tana furta hakan ta miΖe tana ΖoΖarin shigewa cikin Ιakinsu, duk suka rakata da idanu.+
***
Gaba Ιaya Ιakin taron cike yake da ahalin gidan, Husnah da Maryam da Zahidah su ne suketa kujuba-kujubar gyara yaran da suka Ζi zama. Can Maryam da ta fisu rashin haΖuri ta ja Ζwafa tare da taune gefan bakinta,
“Wai ku mu kaΙai zamu yi aikin nan ne, ina ce hadda Laby Baba ya haΙamu. Ita wata fi ne da duk lokacin da aka samu aiki sai ta noΖe?”
Zahidaht ta murmusa, tare da dafa kafaΙarta,
“DaΙina da Maryam ragon azanci. Shin idan mun yi faΙuwa muka yi? Ita fa taga zata iya kowa da kiwon da ya karΙeshi. So hurry up mu yi abin da yake gabanmu”
Bata da yadda zata yi tunda Zahidah ta furta hakan, koba komai gaba take da ita. Kuma basu da tsarin raina nagaba cikin ahalinsu. Dan haka ta cigaba da aikin amma tana yi tana ΖunΖuni. A haka wajen ya kammala kowa ya hallara. Iyayye da jikoki da Ζ΄aΖ΄a babu wanda babu. Duk wurin da ka wulga hayaniya ce tare da tashin muryoyi ana hirar zumunci. Baba Ιaure ne ya Ιauki abin magana tare da yin gyaran murya, gaba Ιaya wurin ya yi tsit!
Godiya ya soma yi ga ubangiji, daga bisani ya faΙi irin nasarorin da ahalin ya samu daga kowane Ιangare. A hankali har ya gangaro kan maΖasudin taruwarsu, wato batun aure. Kowa ya nutsu ya kasa kunne yana sauraron bayaninsa, masu murna na yi akasin hakan kuma dai yana cikin ransu. Maganar daya furta ce ta Ιauke jin wasu daga cikin mazauna wajen na Ιan lokaci,
“Mun yanke zamu haΙa Yusuf da Labiba aure, Jawwad da Khamisa, da kuma Zahidaht da Kabir”
Dum! Sautin ya sauka a kunnuwansu, da fari kalon-kalo aka soma yi tsakanin, Amne da Hajiya Muwwadah. Haka ma tsakanin Yusuf da Ummunsa sai Labiba da take ji kamar almara. Wani irin yanayi ta sami kanta, ita ba farin ciki ba ita ba takaici ba. Haka dai tsaka tsaki, kafin daga bisani zuciyarta ta soma wassafo mata wasu cikin kamalolin Yusuf Ιin. Sai ta sami kanta da sakin murmushin da ita kaΙai ta san manufarsa. Ζangaren Zahidaht kuwa, farin ciki ne ya mammateyeta tako’ina jinta take a duniyar sama. Gaba Ιaya wajen ya Ιauki kaburburi ana nuna jin daΙi,
“Alhaji ina da magana!”
Cewar Amne tana haΙe girar sama da Ζasa, ba ta saurareshi ba ta ci gaba,
“A tarihin wannan zuri’a kowa ya santa da auren zumunci amma kuma kowa ya san cewa auran na Ζuluwa ne bisa ra’ayin ma’auratan. Ta ya ya lokaci guda zaka dawo mana da shuΙaΙΙan tsarin da mun riga mun kawar da wanzuwarsa”
“Ζwarai kuwa Hajiya Amne wannan abu dubawa ne, an tambayi yaran?”
Cewar Hajiya Muwaddah tana murmushin mugunta, duba da yadda taga kowa na bin Amnen da idanu. Dama haka ta saba ta hankaΙata ta magantu akan kowace muΖala ta gidan ita kuma tana daga gefe tana rura wuta. Baba Ιaure kansa ya Ιaure, a zuciyarsa ayyana ya aka yi rainin da matarsa ta yi masa ya kai haka? Har ya gindaya hukunci ta fito tana addawa da hakan. Lallai a wannan karon zai nuna mata so ba ya hana hukunta masoyi.
Ζanannun maganganu ne suka soma tashi, Ζus-Ζus musamman Ιangaren Kabir fiffiΖa ya soma yi yana baya son Zahidaht. Abin da ya haifar mata da faΙuwar gaba mai tsanani, tare da soma tunanin wace irin rayuwa zasu yi tare. Domin ta san tunda Baba Ιaure ya furta, to fa ba fashi sai wani hukunci na ubangiji.
“Yusuf!”
Baba Ιaure ya kira sunansa, murya a kausashe ga kuma Ιarin ran daya gaza Ιoyuwa a muryar tasa. Hakan yasa kowa ya shiga taitayinsa,
“Na’am Baba”
“Zaka iya auren Ιiyata labiba?
Ya furta yana kafeshi da idanu take jikinsa ya yi sanyi, yana jin wani irin rauni yana kewayashi. A karon farko mutumin dake Ζumaji kullum wajen taimakon rayuwarsa yana neman alfarma mai matuΖar wuya gareshi. Ya sani bashi da matsala da mahaifansa, haka karan kanshi zai iya karΙar komai daga baban nasa amma kuma zuciyarsa ta fi tafiya kan tunanin Labiba da Amne fa?
“Idan baka ra’ayinta babu tursassawa tsakaninmu. Kaima Ιana ne kuma mafi soyu ba gareni. Zan iya jurar kowane sauyi daga gareka…”
Ya Ζarasa murya a raunane, domin ya gama karantar saΖon dake cikin zuciyar Yusuf Ιin, yadda yake ganin kaf ahalinsu babu mai iya Ιaukar tarangahomar Ιiyar tashi guiwarsa a sanyaye take da gazawar wanda ya ta’alaΖa da burinsa gareshi.
“Baba ka yi haΖuri bazan iya…!”
Ζas! Ζas!! Ζas!!! Gabansa ya tsananta faΙuwa sakammakon haΙa idanu da mahaifiyarsa.Baba ka yi haΖuri, ba zan iya musu bisa umarninka ba. Ko da baka bani umarni ba Labiba Ζ΄ar uwata ce!”
Gaba Ιaya wajen ya Ιauki kabbara, jikin Baba Ιaure har tsuma yake tsabar farinciki. Labiba kuwa ji ta yi kamar an Ιaureta da sassari, me kalaman Yusuf suke nufi, yana nufin sonta yake yi ko kuma manna masa aka yi?”
“Labiba kina son Ιan uwanki?”
Muryar Baba Ζangaladima ta ratsa cikin tunaninta, kanta a Ζasa bakinta ya yi nauyi. Ba zata taΙa iya kunyata mahaifinta ba duk rashin kunyarta. Sai kawai ta gyaΙa kai, wata irin ajiyar zuciya mahaifin nata ya sauke. Haka ma Zahidaht dai ta amince duk da tana tararrabin amsawar Kabir. Amma ga mamakinta koda aka tambayeshi kai tsaye ya amsa da yana sonta. Ta yi mamaki Ζwarai da gaske. Shi kuwa Kabir ya amsane, ganin Laby ta kuΙce masa kadda ya yi biyu babu kuma Zahidaht dai ba baya ba. Haka taro ya tashi rayukan wasu a daΙaΙΙe wasu kuwa sai ikon Allah.
Ba Ζaramin Ιaci ran mahaifiyar Labiba ya yi ba, ga kuma Ζawarta na Ζara ingizata. Tunda ta shiga gida take kai kawo tsakanin falo da cikin Ιaki. A haka Labiba ta risketa, idanunta Ζur a kanta tanata huci. A zuciye ta kai hannu ta damΖeta,
“Me yasa kika amince Labiba? Kinsan kuwa me ki ka aikata? Ki rasa wanda zaki aura duk taron samarin gidan nan sai wanda bai san ya tsinanawa kansa komai ba?”
“Amne ba zan iya kunyata mahaifina ba gaskiya, shi ma Yusuf Ιin ai baya ra’ayina daga dukkan alamu, amma kuma ya kasa kunyata Abbana sai ni da ya haifa?
“Allah Ya yi miki albarka Labiba”
Muryar mahaifinta ta ratso kunnuwanta, dukkansu suka juya domin basu san shigowarsa ba sai sautin muryarsa. Ya ci gaba,
“Sa’adatu wallahi baki isa ki Ιatamin rai akan auran nan ba, kin ji na rantse zan iya sahale naki auren da shikka uku Ζwarara matuΖar wata Ιaraka ta taso. A yanzu dai na gamsu Labiba ta haifu, dan haka duk wata Ιaraka da zata taso a nan gaba dake zan koka!”
Ficewa ya yi ba tare da ya tanka mata ba. Jiki a sanyaye suka wuce Ιakunansu. Kwana Amne ta yi tana tunanin mafita, sai dai kuma furucin mijin nata ya Ιaga mata hankali. Basu taΙa irin haka da shi ba, dan haka ta haΖure zata bishi yadda yake so kafin ta sami mafita.
Furucinsa ya zauna mata a zuciya Ζwarai. Bisa wannan dalili ne ya sa gaba Ιaya ta Ιauki Ιamarar saki jiki a gudanar da sha’anin bikin ba tare da ta nuna bata so ba. Sai dai a Ζasan ranta bata da maΖiyi sama da Yusuf Ιin. A gefe guda kuma Hajiya Muwaddah na ΖoΖarin zugata amma taΖi bata fuska kwata-kwata. Shi ma Ιangaren Kabir duk tunaninsa ya gaza gano makusar Zahidaht, tako’ina mace ce ta tserewa sa a. Dan haka ya tattara ya haΖura ya rungumi auren gadan-gadan, tare da nuna mata tsantsar kulawar data mantar da ita AUREN HAΖI za’ayi musu.
Yusuf ne dai kadaran-kadahan baya shigewa Labiba, ba kuma ya wasarerre da ita. Sossai Labiba ta saki jiki ta Ζara fuskantar Yusuf Ιin, sai ta ga ya yi dai-dai da ra’ayinta. Haka aka gudanar da biki hankali kwance, Kabir ya cale da amaryarsa ya cigaba da karatunsa haka ma Jawwad.
***
Zaman Labiba da Yusuf zamane me armashi, domin dai ta sameshi yadda take buΖata fiye ma da tsamaninta. Duk wata hidima ta gida tare suke yinta, haka zai gama ya fita buga-bugarsa ya samo kuΙinsa. Babu Ζyashi ko nawa zai samo to zasu Ζare ne a hidimar Labiba.+
Labiba ta sami yadda take so, tana burin auren miji bawan mace. Uwa uba kuma Yusuf mutum mai haΖuri, ga kawaici da kuma tsanin tsafta komai take so yana koΖarin yi mata shi koda kuwa ransa baya so. Ita ma kuma ta ajiye son jikinta, gidanta Ζwas-Ζwas irin na amare musamman idan yamma ta yi haka zata kunna tsintsiyar Ζamshi ya yi ta tashi. Kwanakin amarcinsu sun kafa tarihi mai girma a rayuwarsu, tare da alΖawarurruka wanda suka fi yawa sune yadda zasu kula da yara idan Allah ya basu.
Wata Ιaya biyu uku, a hankali ya soma fuskantarta. Gaba Ιaya malalaciya ce bata san aiki, ga shi kowace magana ta faΙo bakinta to zata yaΙa masa ba tare da la’akari da yanayinsa ba. Cikin wata biyar da auransu kayan Ιakinta sun fita daga hayyacinsu. Ζan wanka da kwaliya da Ζamsassa gidan da take yi duk ta watsar dama na marmarine. Haka Yusuf ya dinga ΖoΖarin gwada mata kuskuranta, abin da ya soma haifar musu da saΙani kenan.
***
Kwanci tashi babu wuya wajen ubangiji. Suna shekararsu ta farko da aure ne al’amura suka soma ja baya. Bikinsu dama kafin azumine aka yi, basu da matsalar abinci sakammakon kayan gararta ga kuma kayan azumi da aka rarraba a ahalin nasu. Haka suka yi sallah kashirΙan cikin wadata ga Ιinkuna da Yusuf ya zuba a sallar ya samu kuΙi sossai. A haka suka gangara babbar sallah ma ya yi Ιinkuna babu laifi. Bayan sallah ne al’amuran suka soma ja baya, samunsa ya ragu sossai babu Ιinki sai ya koma harkarsa ta leburanci. Kwatsam ciki ya bayyana a jikin Labiba, ita da shi gaba Ιaya sun yi murna, haka suka dinga rainon abinsu. Da daΙi babu daΙi Yusuf yana ΖoΖarin faranta mata.
Tunda ta sami ciki ya hanata wanki, shi yake wanke musu kaya duka ya share gida ita kuma ta ji da hidimar girki duk da cewa idan ta dafa ba samun ciyuwa yake wajantaba. Matsalar da suka soma fuskanta gaba Ιaya Labiba ta Ζara Ζazancewa, ko ina zubar da miyau take yi, sai ya zamana Ιakinta baya zaunuwa saboda Ζarni. Ga rainuwa ta masifa, komai ya kawo a wulaΖance take karΙa tana mita. Baya ko Ιaga kai ballantana ya nuna mata ya damu. Musamman da ya lura da yanayin da take ciki. Duk wata kulawa data dace da mai irin lallurarta yana ΖoΖari sossai a kanta.
Ζazantarta na damunsa musamman shi gwanin tsafta, haka zai zage ya gyara ko’ina. Ya sa turare amma kafin sati komai wajen zamansa daban. Ba ruwanta da idan ta cire kaya ta Ιauke. Wasu lokutan hadda masu lema, sai Ιakin ya dinga warin ruma. Haka ya yi ta yi mata uzuri, la’akari da masu juna biyu kan tsinci kansu a yanayin da ya fi natama. Dan haka ta miΖe Ζafa tana zuba taΙara son ranta.
Cikin ikon Allah cikinta ya shiga watan haihuwa mahaifiyar Yusuf ta rasu. Mutuwar data girgiza kaf ahalinsu domin Hajiya Hauwa’u mace ce mai yakana. Bayan makoki da sati uku Allah Ya sauki Labiba lafiya ta sami Ιiya mace. Ai kuwa murna wajen Yusuf kamar ya goyata, ranar suna yarinya ta ci sunan Hajiya Hauwa suke kiranta da suna Ummi. Baba Ιaure da Baba Ζangaladima basu bar Yusuf ya kashe taronsa ba, komai su suka yi tun daga hidimar haihuwar har zuwa ragon suna. Anyi suna da kwana biyu, Labiba ta dawo gida wanka. Amne ta zage ta kula da ita yadda ya kamata. Ummi yarinya mai haΖuri da saurin shiga rai, kowa na Ζaunarta kodan dattakon kakkaninta da mahaifinta. Kullum Baba Ζangaladima kafin ya fita sai ya leΖo ya ganta, da tsokana da komai zai ce,
‘Ku kawomin akori kishiya!”
Amne kan ce,
“Kakanin zamani da babu kunya a idanunsu, sun iya biyo jikanya”
Duk da yasan shaguΙe take masa, yakan maida abin a wasan dare domin cikar mutuntaka. Takai ta kawo tsegumi kala-kala cikin gida, tun wasu na mitar rashin kawaici, har suka sa idanu. Sunan a kori kishiya ya so yin tasiri ga Ummi sai da Labiba ta nuna jan ido sossai sannan aka daina faΙa.
***
ZAHIDA.
Zahidaht kuwa zaman nasu ba acewa komai, domin dai satinsu huΙu ta soma fuskanta asalin waye Kabir. Bata taΙa sanin halinsa haka yake ba, ta shiga nadama mara iyaka daga bisani ta rungumi Ζaddara tana yi masa addu’a.
Matsala ta farko da suka soma fuskanta, maganar karatu da ta yi masa. Nan ya sawa idonsa kwalin Audu ya nuna be son batunba, tun suna yi ita su kaΙai magana har kunnanan Baba Ιaure amma ya Ζyirmushe ya ce bazata yi ba. Tilas tana ji tana gani ta haΖura. Bata da aiki sai zaman gida kamar me gadi. Ganin zaman bazai mata ba yasa ta soma saida kayan gargajiya, wanda Yaya Asabe ke mata aikinsu ana turamata Ζasar da suke tana saidawa. Su kuka, daddawa kayan Ζamshi da sauransu har ma da lalle da salatif. Akan zuzzubasu cikin roba, tare da mana tambarin sunanta da addreshi. Ai kuwa nan da nan ta yi sabo da mutane irinta Ζ΄an asalin nijeriya, idannunta suka Ζara buΙewa tana fuskantar rayuwa yau da gobe. A irin haka ta gano mijinta manemin matane ta hanyar wata mai siyan kayanta Ζ΄ar bariki kuma mashayi.
Ranar ta yi kuka ba kaΙan ba, babu wanda ta sanarwa sai Yaya Asabe, ita kuma ta fututtuke kan ta baro Ζasar domin ba zata zauna da fasiΖi ba. Sai dai kuma Ζiri-Ζiri ta nuna mata ba zata iya fuskantar iyayensu da mummunan labari ba. Kuma tana son mijinta zata iya zama da shi ta yi masa addu’a. Yaya Asabe ta Ζulu matuΖa, tana son Ζwatarwa Zahidaht Ζ΄ancinta sai dai ta lura so ya rufe mata idanu. Ta ciza ta hura amma ta ΖeΖashe Ζasa ta Ζi karΙar batun. Hakan yasa ta watsar da sha’aninta tare da yi mata gargaΙi kan nan gaba kadda ta nemi taimakonta kan matsalarsa. Ta kuwa amince da hakan Ιari bisa Ιari.
Sai dai tako’ina bata jin daΙin zama da shi. Zai shawo giyarsa idan ta gaya masa Ζarya ya naΙa mata duka. Hakan ba zai hana idan ta tashi ta kyautatta masa ba. Ya zageta ya hantareta kuwa ba komai ba ne, amma murmushi ne aikinta tare da furta,
“Na gode mijina!”
Kabir mugune sossai, ba shi da mutunci ga izgilanci da nuna kowa ba kowa bane. To itama Khamisa kusan duk matsalar Ιaya ce. Haka take ΖoΖarin danewa sai dai ta zo gun Zahidaht ta ci kukanta. Wani lokacin KUSKURAN WASU IYAYEN take gani, sun san halin namiji su Ιauki nutsatsiyar Ιiya su bashi kawai dan taΖamar cewa mace zata saitashi. Ita a rayuwarta bata taΙa ganin an Ιauki mace mara ji ba an bawa namiji, da sunan wai zai saitata. Hasalima gudun auransu ake koda kuwa cikin dangine amma namiji sai ka riskeshi da tarin guma-guman aibu sai ace duk abin da ya yi ADO NE.
Tana mamakin yadda laifi yake zama ADO! A saninta duka tabo sunansa tabo wala ga mace wala ga namiji. Sau tari Zahidaht ita take kwakkwafarta domin shi iskanci nasa ya wuce na Kabir gida yake komai gaban idanunta. Sai dai kuma, matsalar da aka samu Khamisa mace ce mai zurfin ciki da saka abu a rai. Gata da san a kula da ita kamar me, dan haka ta matsawa kanta da damuwa sossai.
A hankali ciwo ya soma cin Khamisat, kafin a farga ya ci Ζarfinta. Sau biyu tana yin Ιari saboda damuwa da tunani, asibiti sun yi iya bakin ΖoΖarinsu wajen nuna mata illar abin da take yi amma a banza haka ma Ζ΄ar uwarta. Damuwar data sawa ranta, ita ta haifar mata da ciwon zuciya ta mutu farat Ιaya. Tabbas mutuwarta ta taΙa iyayyensu, musamman da suka sami labarin abin da ya yi sanadin mutuwarta. Daga wannan lokaci suka sallama Jawwada, ba kuma su yi tunanin bincikar Kabir ba domin zahirinsa ya gamsar da su.
Mutuwarta ta sukurkuta Zahidaht Ζwarai, sai ma ya zamo sillar asassa damuwarta domin Jawwad dai gidansu ya dawo da zama kacokan kuma aciki ya cigaba da gudanar da rayuwarsa yadda ya saba. Bata da ikon magana, Kabir zai ci mutuncinta. Haka ta cigaba da haΖuri da daΙi babu daΙi. Komai ta yi a hantare. Babu yadda bai yi da ita ba akan ayi mata allurar hana Ιaukar ciki taΖi amincewa. Hakan yasa yake amfani da wani mai duk lokacin da zai kusanceta. Wanda matuΖar akwai ciki jikinta to kuwa a daren take Ιarinsa. Ba tare data ankare ba, cikin shekara guda da auransu Ιarinta biyar.
Tilas aka yi mata Ιaurin bakin mahaifa saboda tana neman samun matsala. Lokacin da ta sami labarin haihuwar Labiba kamar ta yi hauka. Kwata-kwata bata san cewar Kabir ne yake mata bita da Ζuli ba. Sai baΖar izaya da yake mata kullum. Tana da son Ζananun yara haka zata bi constomer Ιinta ta yi ta yi wa yaransu kyautar kayan wasa.
WulaΖanci dai ba kama hannun yaro, tun tana daurewa har ya zamana ta soma yunΖurin barin gidansa. Sai dai bata da me goyon bayanta. Yaya Asabe ce dama maogararta kuma bata bata dama ba tun farko. Sai yanzu take hango KUSKURANTA da a baya ta Ζi amincewa da Ζuduri yayartasu. Sai dai kuma kash, a wannan lokacin bata da me goyon bayanta. Domin dai Yaya Asabe nuna mata ta yi ta je ta yi haΖuri, haka kowace mace take yin haΖuri da mijinta. In ta samu wannan, ba lalai ta sami wannan ba. Babban abinda ya ke Ζara dakusar da ita kuwa, ganin cewa da wuya ka ga a zuri’arsu wata ta kawo karar miji. Wannan na sarar da guiwarta matuΖa. Kabir kuwa sai abin da ya yi gaba. Musamman da ya kasance makarantarsu ana damawa da shi, akwai kwanya shi ne first class dan haka Ζ΄an mata binsa suke ba shi ne yake binsu ba uwa uba ga kyau tsayayyen namiji ne.
Post a Comment for "WATA MACE CHAPTER 2 BY SANA S MATAZU"