Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

SHU'UMIN NAMIJI CHAPTER 8 BY FATYMA SARDAUNA

SHU’UMIN NAMIJI CHAPTER 8 BY FATYMA SARDAUNA

                    Www.bankinhausanovels.com.ng 

Yajima zaune a kan gadon nasa, gaba Ι—aya kansa ya kulle yarasa meke damunsa,  wai shin da gaske SO yake ko kuwa? anya kuwa yanaga zaman sa haka zai yi wu? zaifi masa kyau yanemi Abid domin shi ne kaΙ—ai zai iya fayyace masa halin da yake ciki,  tabbas shi koda son Zahrah Abid Ι—in yace masa yanayi yanzu bazai musa masaba, idan kuwa har haka so yake to yana mawa Zahrah so me tsanani,  saurin laluΙ“ar wayarsa Ζ™irar  Samsung dake kusa dashi yayi. Numbern Abid ya dannawa Ζ™ira, bugu biyu Abid ya Ι—aga Ζ™iran cikin muryan kasala yace “Mutumin ya akayi ne, ka katseni ina cikin holewata”+

“mcheeww aikin ka kenan cin Ζ΄aΖ΄an mutane, kana ina yanzu inaso muyi serious magana da kai” Zaid yafaΙ—i haka cike da zaΖ™uwa.

MiΖ™a Abid dake kwance shame shame a gado yayi haΙ—e da sakin daria, wai yau shi Zaid ke cewa baida wani aiki se cin Ζ΄aΖ΄an mutane, hmm ai duk iskancinsa shikansa yasan a Ζ™arΖ™ashin Zaid yake, domin kuwa Iskancin Zaid me lasisi ne.

Cike da Ζ™uluwa Zaid yace ” Nifa bana Ζ™ira ka kamin iskanci bane, da zaka tsaya kanamin dariya”

“Yi haΖ™uri mana nawan, maganartaka ce tabani dariya, zuwa anjima mu haΙ—u a Millinion Park ina fata de bawata matsala bace ta afku?”

Ɗan yamutsa fuska Zaid yayi haΙ—e da duban agogon Rolex Ι—in dake Ι—aure a tsintsiyar hanunsa.  “Shikenan to muhaΙ—u Ζ™arfe 5 na yamma banakumason kamin african time, 5 nacika idan bakazoba, bazan tsaya Ι“ata time Ι—ina wajen jiranka ba” yayi maganar cikin yanayi da yake nuna cewa ba wasa yake ba..

“Okay” kawai Abid yace haΙ—e da aje wayartasa yajawo babe Ι—in dake kusa dashi, suka ci gaba da watsewarsu ko kunyar Allah dayake ganinsu basayi, Allah karabamu da Ζ™eΖ™ashewar zuciya Ameen.

Zaid yana aje wayartasa yasanya hanu yashafi cikinsa, sai alokacin yake tuna rabonsa da yasanya abinci acikin cikinsa tun jiya da yammaci,  amma saboda tsabar yashiga tension ko yunwarma bayaji,  murmushi yayi tunowa da yayi da yanda yaji muryan Abid, dagajin yanda yaji yanayin muryartasa yatabbatar masa cewa holewa da mace Abid Ι—in keyi, “hmmm Abid ba dama wajen iya latsa mace” yafaΙ—i haka a fili, shikamma rabonsa daya kusanci wata mace harya manta,  shi yanzu ko mace ma yagani bata wani burgesa, yanzu idan zaiyi sex to badakowacce mace yakeso yayi ba, face Zahrah ita kaΙ—ai yakejin cewa zai iya sauΖ™ewa damuwarsa yanzu, itakuma kaΙ—aice zata iya basa gamsuwa Ι—ari bisa Ι—ari.  MiΖ™ewa yayi yanufi wajen fridge Ι—in dake Ι—akin nasa, fresh milk ya Ι—auka haΙ—e da tsiyayawa a cikin glass cup, zama yayi yasoma sipping fresh milk Ι—in a hankali,  gaba Ι—aya hankali da tunaninsa sunaga Zahrah, ko yanzu wani hali take ciki? Allah masani…

***

Sake narke masa murya tayi cikin shagwaΙ“a tace “Nide bance bana sonka ba, aikaima kasan inasonka, kawai de nakasa sakewa da kai ne har yau!” taΖ™are maganar tana me rausayar dakanta gefe tamkar yana ganinta..

Dr.Sadeeq dake zaune cikin luntsumemiyar kujeransa na office ya lumshe idanunsa haΙ—e da gyara zaman wayar akan kunnensa,  sosai shagwaΙ“an Zahrah ke sauΖ™ar mai da kasala acikin jikinsa, yayinda idan yaji muryarta yake samun nutsuwa a cikin zuciya da ruhinsa…

STORY CONTINUES BELOW

“To meyasa bakya iya sakewa dani ne My Princess, kinkuwa san irin sonda nake miki?  inasonki Zahrah fiye da tunaninki,  amma bazaki gane hakan ba, sai idan nasameki a matsayin matata, na tabbata nan da 3 weeks kinzamo mallakina daganan kuma zaki gaskata soyayyata a gareki!” yafaΙ—i maganar tasa cikin  yanayi na shauΖ™i..

Saurin kulle idanunta  tayi haΙ—e da sanya hanu tarufe fuskarta, saikace wanda take aga banshi,  sosai maganarsa yasa taji kunya,, ta lura haka Dr.Sadeeq Ι—in yake watarana baruwansa kansa tsaye yake faΙ—ar maganar da zaisanya taji kunya.

“My Princess kinyi shiru” Dr.Sadeeq  yafaΙ—i haka a kasalance.

Numfashi Zahrah ta fesar haΙ—e da sake yin Ζ™asa da muryarta cikin shagwaΙ“an daya zamemata sabo tace “Munyi magana da Baffa, yace ku kawo kayan lefen duk sanda kuka shirya kawai”

DaΙ—i ne yakama Dr.Sadeeq harsaida yakasa Ι“oye murnarsa idan kuwa hakane to tabbas acikin satin nan zai sanar da Ζ΄an uwansa saisu shirya rananda zasu kawo kayan, shida zasuce yauma to tabbas da zaiso hakan.

“Naji daΙ—in maganarki My princess saboda haka kincancanci nabaki kyauta ta musamman, idan banzo da dare ba gobe zanzo insha Allah”

Murmushi kawai Zahrah tayi haΙ—i da cewa “Nagode amma kariΖ™e kyautarka bayanzuba”

“Meyasa?” yatambayeta cikin yanayi na Ι“ata fuska.

“Saboda hidiman da kakeyi yayi yawa, dan Allah kabari haka kaji!” taΖ™are maganar cikin yanayin shagwaΙ“a. 

“Inde akan kine Zahrah bazan taΙ“a gajiyawa ba, zanyi wani aiki yanzu zanΖ™iraki anjima kinji princess Ι—ina!” yafaΙ—i haka cike da lallashi…..

Haka sukayi sallama cike da kulawa ga junansu, yanzu kam tagama aminta da Dr.Sadeeq insha Allah kuma idan ta auresa zata basa farinciki me Ι—orewa, iyaka iyawarta…..

Sosai Zaid yashaΖ™a da irin yanda Abid yasanyasa agaba yaketa yi masa dariya,,   tsuka Zaid yaja me tsayi haΙ—e da kawar da kansa gefe jiyake tamkar ya tashi ya rufe Abid da duka, idan banda iskanci taya zai sanyasa gaba yayi ta masa dariya bayan yagama jin matsalarsa…

Wani mugun kallo Zaid yajefawa Abid me Ι—auke da tarin ma’anoni da yawa, ganin haka yasanya Abid saurin gimtse dariyarsa haΙ—e da kama hanun Zaid Ι—in…

“Yi haΖ™uri Abokina, maganar ce tabani dariya”

Tsuka Zaid yakuma ja batare da yace komai ba…..

“Nafuskanci inda matsalanka ta dosa Zaid amma kuma nasan abune me wahala ka yarda da abun dazan faΙ—a ma”

“Bazaka gane yanda nakeji agame da’ita ba ne Abid, dakasan yanda nakeji a zuciyata da ka tausaya kasanar dani maganin matsala ta, kodai shine so Ι—in da kake cewa?” Zaid  yatambayi Abid cike da damuwa…

“Ƙwarai kuwa Zaid wan nan shine SO, sai de naka SO’n ya banbanta da sauran soyayya’n, kai naka soyayya’r me tsanani kakeyi, wanda tariga da tajima acikin jikin ka batare da ka sani ba, ina da yaΖ™inin cewa tun farko Son Zahrah kake bawai sha’awarta ba kamar yanda ka Ι—auka!” Abid yafaΙ—i haka da iyaka gaskiyarsa…

Nannauyar ajiyar zuciya Zaid ya sauΖ™e haΙ—e da sanya duka hannayensa ya dafe kansa wanda yake Ι—an sara masa a hankali..   Tabbas yanzu kam ko yaso ko yaΖ™i dolensa ya yarda da maganan da Abid yafaΙ—a masa, domin kuwa idan har ba soyayya ba menene ke damunsa dayake sawa yakejin zafi a zuciyarsa? idan ba soyayya ba menene yake sanya tunaninsa hargitsewa da zaran yatuno Zahrah? idan ba soyayya ba menene yake sanya sa rasa sukuni da nutsuwarsa aduk sanda yatunanota kokuma yaganta? lallai kuwa soyayya baimasa adalci ba da bai sanar dashi kansa ba tun sanda yafarasa batare da yasani ba..  

Idanunsa da sukayi jajur dasu ya Ι—aga haΙ—e da maida kallonsa ga Abid  “Inasonta Abid inasonta sosai!”

Waro idanu Abid yayi yana me kallon Zaid  idan da ba Zaid Ι—in ne da gaske a gabansa ba, to tabbas da sai yace badaga bakin Zaid wa Ζ΄an nan kalaman suka fitoba, yau Zaid da kansa yake cewa yakamu da son wata? lallai kuwa rayuwa tana shirin juyawa abokin nasa baya.1

STORY CONTINUES BELOW

MiΖ™ewa Zaid yayi daga zaunen da yake haΙ—e da sanya hanu ya kwashe wayoyinsa dake kan Ι—an Ζ™aramin table Ι—in dake aje gabansu.

Kallonsa Abid yayi cike da mamakin ganin yanda lokaci Ι—aya yanayin Zaid Ι—in ya sauya.

“Inakuma zaka?”   Abid yatambaya..

“Zanje gidansu Zahrah Abid, idanuna sun matsamin zuciyata har bugawa take Abid, ita kawai nakeson gani,  idan har zata amince inaso ayau base gobeba koda Ζ™arfe Ι—aya ne  na dare  a Ι—aura mana aure da’ita” yanakai wa nan a zancensa yayi tafiyarsa.. Hangame baki Abid yayi yana kallonsa harya Ι“acewa ganin idanunsa.   Anyakuwa Zaid yana cikin hankalinsa? Kodai asiri yarinyar talakawan nan tayi masa ne?  Abid yajerowa kansa waΖ΄an nan tambayoyin,  bayan yasan baida amsa bai kuma da me basa amasar…

Zahrah dake zaune tana gudanar da assigment Ι—inta, wani yaro yashigo cikin gidan nasu haΙ—e da kwaΙ—a sallama..  Amsa masa Zahrah tayi batare da taΙ—ago kanta takalli yaron ba..

“Wai ana Ζ™iran Zahrah a waje” yaron yafaΙ—a yana me kallon Zahrah domin kuwa yasan cewa itace wacce aka aikosa yayi Ζ™iranta..

Sai alokacin Zahrah taΙ—ago kanta ta kalli yaron, haka nan taji gabanta yafaΙ—i, to waye kenan yake sallama da’ita? ta tambayi kanta, wayarta dake kusa da’ita ta Ι—auka haΙ—e da dubawa, 1 missed call tagani na Dr.Sadeeq,  dayake wayartata a silent tasanyata shi yasa bataji Ζ™iran nasa ba, kenan shine yazo yaΖ™ira wayarta bata Ι—auka ba shiasa yaturo yaro.   “Jekace inazuwa” ta  bawa yaron amsa a taΖ™aice..

MiΖ™ewa tayi haΙ—e da tattara takardunta tayi Ι—aki.  Mayafi taΙ—auka   ta yafa akan kayan dake jikinta…

Tsaye yake ajikin motarsa yayinda yakifa kansa asaman  motar yana me kaΙ—a key Ι—in motarsa dake riΖ™e a hanunsa..

Kanta a Ζ™asa tafito daga cikin gidan tana me duba wayar dake hanunta.  Tsayawa tayi cak bayan ta haΙ—e wani  miyau dayazo me Ι—aci ya maΖ™ale mata a maΖ™oshinta. 

Murmushi yasakarmata haΙ—e da soma takowa zuwa gareta..

Lokaci Ι—aya idanun Zahrah suka sauya kala daga fari zuwa ja, juyawa tayi a fusace tanufi hanyar shiga gida, da sauri Zaid yasha gabanta haΙ—e da marairaice fuska cike da tashin hankali yasoma cewa….

“Dan Allah Zahrah kitsaya ki saurareni, dan Allah kada kimin haka Zahrah,  inaso ki saurare…..” kasa Ζ™are maganar nasa yayi sakamakon kyakkyawan marin da Zahrah ta shimfiΙ—a masa akan  kyakkyawar fuskarsa…

Cikin Ζ™una da kuma zafin zuciya     haΙ—i da raΙ—aΙ—i Zahrah ta haΙ—a yatsanta na tsakiya dakuma babbar yatsarta, ta kaΙ—a ade de fuskar Zaid duk da kuwa cewa yakerema tsayinta..

“Natsaneka tsana mafi muni, natsani jin kowani irin kalma ce da zata fito daga bakinka,  wlh wlh nayi rantsuwa sau biyu, idan har ka sake naΖ™ara ganin fuskar  ka to zanyi maka abun da baka taΙ“a tunani ba!” cikin matsanancin Ι“acin rai taΖ™are maganar tana me raΙ“an gefensa zata wuce,  Zaid da zuciyarsa tariga da ta karye baiyi Ζ™asa a guiwa ba yasake shan gabanta.

“Kimin duk abun da kikeso Zahrah, zanfi jin daΙ—ima idan akace kece zakiyi silan mutuwa ta, dan Allah ki saurareni mana Zahrah!!” yaΖ™are maganar cikin rawan murya…

Kuka ne ya Ζ™wacewa Zahrah me tsanani cikin muryan kukan tasoma cewa…..

“Miye laifina Zaid? Menene aibuna? shin wani abu na aikata maka da ka zaΙ“i cutar da rayuwata? ashe de ganganci ne don na Ι—au soyayyata na baka? me yasa ka yaudareni Zaid? meyasa dole saini kazaΙ“i ka tozarta? Kacutar da rayuwata ka dasamin Ζ™unci a cikin zuciyata, wlh natsaneka Zaid,  Idan har yaudara zata zamemaka abun ado mezaka amfana dashi acikin rayuwarka? Miye ribar aikata zina da fasiΖ™anci? Natsaneka Zaid! Natsaneka!! Bana fata Allah yaΖ™ara haΙ—a fuskata da taka fuskar har gaban abada! Dan Allah kafita a rayuwata Zaid!!!” cikin matsanancin kuka taΖ™are maganar tana me durΖ™ushewa Ζ™asa domin kuwa zuwa yanzu tsayuwa ya gagarewa Ζ™afafunta…

Idanun Zaid ne suka kaΙ—a suka zama jajur dasu tamkar wanda aka zuba musu jan barkono.   gaba Ι—aya jikinsane yasoma Ι“ari, shi Ι—in ma durΖ™usawa yayi agabanta cikin murya me tsananin rauni yaΖ™ira sunanta,, saurin Ι—aga masa hanu Zahrah tayi alaman batason jin komai daga garesa..

“Banason nasake koda jin muryarkane Zaid, kafita a rayuwata, wai mekake nema dani ne? ko kana tunanin zan sake aminta da kai ne? hmmm kayi babban kuskure Zaid idan kuwa har haka kake tunani,  zaifi maka kyau, kamanta dani kakuma manta da wacece ni, ni na barwa Allah cutarwan da kayi agareni, kuma insha Allah nasan zai Ι—aukarmin fansa,, sai de inaso kasani cewa har abada bazan taΙ“a yafe maka ba, inaso kuma kada kamanta da cewar natsaneka !”  a fusace ta faΙ—a cikin gida haΙ—e da banko Ζ™ofar gidan nasu. 

Tashi yayi daga durΖ™uson da yake haΙ—e da bin bayanta da kallo, gaba Ι—aya zuciyarsa tagama karaya, wani irin abu yakeji ajikinsa yayinda kansa yayi masa wani irin masifaffen nauyi,  zafi yakeji azuciyarsa irin sosai Ι—in nan.

Zahrah kuwa zamewa tayi jikin Ζ™ofar gidan nasu tasaki wani irin kuka me tsuma zuciya. Se yaushene zata warke daga raΙ—aΙ—i dakuma ciwon abun da Zaid yayi mata?   ganinsa yasake tasomata da mikin daya Ζ™i warkewa tsawon lokaci acikin zuciyarta,  maiyasa Zaid yazame mata bala’i acikin rayuwarta? kuka tashiga yi sosai da sosai…

Zaid kuwa daΖ™yar ya iya jan Ζ™afafunsa yanufi motarsa,  kasa tuΖ™a motar tasa yayi, gaba Ι—aya idanunsa duhu suke gane masa, tabbas bazai taΙ“a iya tuΖ™a mota yana a irin wan nan halin ba,, da Ζ™yar ya’iya laluΙ“a wayarsa yaΖ™ira driver’nsa… Mintuna kaΙ—an drivern Zaid yazo ya wuce dashi….

Saida tayi kukanta son ranta har sai da taji kanta yasoma ciwo kafun ta tsagaita, haΙ—e da miΖ™ewa daga jikin Ζ™ofar tashige cikin gida, direct Ι—akinta ta wuce ta kwanta numfarfashi kawai take sauΖ™ewa, lokaci Ι—aya zazzaΙ“i yarufeta, harsaida tajawo mayafi ta lulluΙ“i jikinta….

Sanda yashiga falonsa ko gani bayayi sosai,  wani irin ciwo kansa ke masa me tsanani wanda yasanya idanunsa sukayi nauyi,  da Ζ™yar ya’iya jan Ζ™afansa yashiga Ι—aki,  kalaman Zahrah ne sukeyi masa yawo acikin kansa,, yatsani jin kalmar tatsaneshi da take yawan faΙ—a Ι—in nan,  wlhy a gurinshi da ta faΙ—i wan nan kalman gwamma ta sharara masa maruka koda kuwa guda biyarne akan Ζ™uncinsa..     Ya yanke shawara da de yakasance a irin wan nan yanayin ya gwammace yafita daga cikin hayyacinsa idan yaso bayan wasu tsawon lokaci yadawo cikin hayyacin nasa,,  wasu Ζ™wayoyin magani yaΙ—auko harkala biyu, wanda suke gusarwa mutum da hankalinsa, maganin suna da hatsari sosai hakan nema yasanya ba’a sai dasu a bayyane sai de a Ι“oye, kuma suna mugun sa bacci sosai…   Saida ya Ι“alli guda uku uku daga jikin kowani sachet, kafun ya watsa maganin cikin bakinsa, wan nan karon ko ruwa baisha ba haka ya haΙ—iye magungunan,  yanda kalaman Zahrah ke dawowa cikin kunnensa yafi komai Ι—aga masa hankali,  kwanciya yayi lamo akan gado yayinda yake Ζ™wato numfashinsa dake Ζ™oΖ™arin Ζ™wace masa da Ζ™yar.  wani irin fusga numfashinsa yayi lokaci Ι—aya kuma komai najikinsa ya sake…1

Zahrah kuwa zazzaΙ“ine ya dirarmata me zafin gaske, wanda yasanya lokaci Ι—aya jikinta yasoma Ι“ari ta fara rawan Ι—ari, har zuwa yanzu hawayenta bai tsaya ba. Zaid ya cuceta itakam duk irin Ζ™uncin daya jefata a baya bai ishe saba saida yakuma da wowa gareta, sai yaushene hawayenta zasu tsaya? sai yaushene zata samu farinciki ingantacce wanda babu algus acikinsa? tunda ta haΙ—u da Zaid Ζ™uncin rayuwarta yasoma, wani irin annoba Zaid yazame mata ne?…..Baki Labisat dake tsaye taturo gaba haΙ—e da Ι“ata fuskarta duk wai akan don  Mom Ι—insu tace taΖ™ira mata Zaid a Ι“angarensa ne yasa take wan nan abun…

“Tsayuwan uban me kike bacewa nayi ki Ζ™iramin yayanki ba!” Mom tafaΙ—i haka cike da faΙ—a, ganin Labisat Ι—in bata da niyar zuwa aiken datayi mata.

“Mom wlhy tsoro nakeji kada naje ya masifance ni!” Labisat tafaΙ—i haka cikin shagwaΙ“a. 

Harara Mom tawurga mata bashiri Labisat takama hanyar fita daga cikin falon…

Aranta kuwa roΖ™on Allah take yasa idan taje kada ya masifanceta saboda shi abun faΙ—a baya masa kaΙ—an ko kaΙ—an,  jiya jiya dawowanta daga boarding school amma Mom zata haΙ—ata da masifan Yaya Zaid (Su yaya manya?)

Kusan sau huΙ—u Labisat tana knocking Ζ™ofar daze kaita cikin falonsa, amma shiru ba amsa, hakan yasanya tatura Ζ™ofar tashiga,,   bakowa acikin falon sai daddaΙ—an Ζ™amshinsa dake tashi.. Direct Ζ™ofar bedroom Ι—insa tanufa haΙ—e da soma knocking Ζ™ofar,, jin shiru ne yasanya tashiga Ζ™iran sunan sa…

“Brother! Brother!”  ko gyaran murya bataji yayiba balle tasa ran zai amsa mata, batama tabbatar yana cikin Ι—akin ko baya ciki ba..

Gajiya tayi da knocking Ζ™ofar ta juya tayi tafiyarta…

“Mom inaga fa kamar Bro bayanan domin nayita knocking door Ι—insa amma bai amsa ba”

“Tabbas yana cikin gidan nan Labisat domin kuwa tunjiya daya shigo baifita ba, har me gadi na tambaya naji ko yaga fitarsa amma yacemin tunjiya daya shigo bai fita ba,  miskilancin nasa ne ya motsa, banaje dakaina nasa mesa nikam ae be isa yanunamin halin Ζ™yaliya ba” Mom tafaΙ—i haka tana me miΖ™ewa tsaye daga zaunen da take..

Itama Ι—in de knocking tayi masa haΙ—e da Ζ™iran sunansa amma shiru bai amsata ba, hakan yasa ta murΙ—a handle Ι—in Ζ™ofar ta kutsa kanta ciki bakinta Ι—auke da sallama..

Tsuka Mom taja sakamakon ganinsa da tayi kwance akan gado yayi ruf da ciki, lallai ma wato iskancine ya hanasa amsa mata, da fari hartayi zaton ko baya gidan ne..

“Zaid!” taΖ™ira sunansa cikin kakkausar murya… Ko motsawa baiyi ba balle tasaran ze amsa mata..

Kafeshi da idanu tayi tana me nazartarsa, a iya saninta da Zaid baya bacci a irin wan nan lokacin, impact ma shiba mutum bane ma’abocin yawan bacci ba’a bisa Ζ™a’ida ba, idan kuwa harda gaske baccin yake to baya rasa Ι—ayan biyu kodai baida lafiya ko kuma yayi halin nasa nashan Ζ™wayoyi,  “Sai yaushene Zaid ze san ya girma? sai yau shene zai dena nuna rashin damuwa da lafiyarsa?” tajeromawa kanta waΖ΄an nan tambayoyin,  “HaΖ™iΖ™a Zaid Ι—anta ne amma ita kanta har yau batasan wani irin haline da shi ba, shi mutum ne me nuΖ™u nuΖ™u bakoda wani lokaci ne kake sanin gaba da bayansa ba, haka nan yake bakomai ne zaka masa Ζ™a burgesa ba yanada wani shegen shu’umin hali saide kawai Allah yashirya mata shi”…

STORY CONTINUES BELOW

A hankali tashiga takawa zuwa gaban gadon nasa..

Idanu Mom tasake warowa waje, tabbas idan de idanunta de de suka gane mata to kuwa Zaid baya numfashi, domin  babu wata alamar  da take nuna akwai nunfashi a tattare dashi saboda ko cikin sa baya motsawa, alama ta baya shaΖ™an numfashi kenan..

Hanunta takai setin hancinsa ko da zataji Ι—umin numfashin sa.

Salati Mom tasa haΙ—e da dafe Ζ™irjinta, sakamakon wani irin bugawa da taji zuciyarta tayi.

“Zaid!Zaid!” Mom tashiga Ζ™iran sunansa cikin tashin hankali haΙ—e da soma jijjigasa.

Hawayene suka shiga bin Ζ™uncin Mom bashiri ta fita daga Ι—akin, direct Ι“angaren Alhaji Ma’aruf ta nufa saboda yana gida baikai ga fita office ba..

“Alhaji! Alhaji! katemaka wlhy Zaid baya numfashi zo muje ka gani, katemakeni kada na rasa Ι—ana mafi soyuwa a gareni!!” gaba Ι—aya cikin tashin hankali Mom keyimawa Dad bayani..

Mamaki haΙ—i da al’ajabi ne yakama Alhaji Ma’aruf amma de yanzu balokacin tambaya bane gwamma yabita yaga meke faruwa da Zaid Ι—in….

Shima sosai ya tsorita kuma hankalinsa yatashi daganin Zaid yashe a gado baya numfashi sai kace gawa…

Da Ζ™yar Abba ya’iya sungumarsa yasanyasa a mota, abunka da Ζ™aΖ™Ζ™arfa kuma ma’abocin yin gym shiasa jikinsa yake ko ina a murΙ—e, san nan kuma me Ζ™aramin Ζ™arfi bazai iya Ι—aga sa ba, Dad Ι—in ma saida temakon Mom ya iya Ι—agasa… Daga Mom har Labisat hankalinsu amatuΖ™ar tashe yake haka suka shiga mota suka rankaya zuwa asibiti…

Direct Emergency  aka kai Zaid cikin gaggawa likitoti suka shiga basa temakon gaggawa…

Jigum jigum haka Abba da Mom sukayi a wani Ι—an corridor dake kusa da Ι—akin da aka kai Zaid, iya Ζ™ololuwar tashin hankali sun shigesa, kuka kawai Mom da Labisat keyi, kasa koda rarrashinsu Alhaji Ma’aruf yayi domin shima da akwai hali da kukan ze sanya ko da zaiji sassauci a cikin zuciyarsa…

Likitotin nan sunci baΖ™ar wahala kafun da taimakon Allah suka samu suka daidai ta numfashin Zaid. Haka suka fito suna sharce gumi….   Kallon Alhaji Ma’aruf Ι—aya daga cikin Doctors Ι—in yayi haΙ—e da cewa “Ranka ya daΙ—e muje office”    Ζ™oΖ™arin binsu Mom tasomayi Alhaji Ma’aruf yaΙ—aga mata hanu alamar tajirasu….

Handkerchief likitan nan yaΙ—auka ya Ζ™are share gumin dake tsatstsafawo akan goshin sa..

Ganin haka yasa Abba cike da tashin hankali yace “Yade Dr.Bilal meke faruwa ne, dan Allah kada kafaΙ—amin wani mummunan labari!”

Jinjina kai Dr.Bilal yayi haΙ—e da kallon Dad.  “Kwakwantar da hankalinka Alhaji zuwa yanzu komai ya daidaita munshawo kan matsalan”

Nannauyar ajiyar zuciya Dad yasauΖ™e haΙ—e dayin hamdala acikin ransa…

Sake gyara zama Dr.Bilal yayi haΙ—i da cewa “Sai de kuma agaskia bazan Ι“oye maka ba Alhaji Ι—an ka yana cikin matsala wanda yake gab da rasa rayuwarsa matuΖ™ar baikiyayewa kansa shan Ζ™wayoyi masu mugun haΙ—ari ba, baya ga haka kuma idan har ya cigaba dashan giya  nan da Ζ΄an kwanaki tofa sai de kuma abun da Allah yayi!”

Yanzukam Dad ne yashare gumi ba Dr.Bilal ba, domin kuwa a iya tsawon rayuwarsa baitaΙ“a sanin Zaid nashan wasu Ζ™wayoyi masu bugarwa ba,  yade san da ya nashan giya amma kuma atunaninsa yajima da dena shan giyan.

“Bangama fahimtarka ba likita, naji kace Ζ™wayoyi na bugarwa, kana nufin shiΙ—in ne yakeshan Ζ™wayoyin bugarwa?” Dad yatambayi Dr.Bilal cike da son sanin Ζ™arin haske akan batun..

“Wato a iya bincikenmu mungano cewa akwai wata Ζ™waya me haΙ—arin gaske da yakesha lokaci zuwa lokaci, wanda kuma haΙ—arin Ζ™wayar yana da matuΖ™ar yawa,  bazanyi mamakin a ina yasamu Ζ™wayan ba, saboda nasan shiΙ—in isashshene, saboda Ζ™wayar ba ako ina ake samunta ba, a Ζ™a’ida ma anhana shigo da Ζ™wayar nan gida Nigeria, kawai de rayuwar yanzune  da ta zama sai a hankali, zai iya yuwuwa kuma ba anan yake sayan Ζ™wayan ba daga can waje yake shigowa da abarsa, sai de kuma wan nan duk bashine damuwar ba, idan har ya cigaba da shan wan nan Ζ™waya to ina me tabbatar maka da cewa zai iya rasa ransa ako da yaushe, duk da kuwa dama munsan mutuwa tana kan kowa yanzu ko anjima, amma tabbas kiyayewan shine yafi, san nan kuma giya tayi masa mummunan illa saboda tasamu mafaka acikin cikinsa, wataΖ™ila yamai da ita ruwan shansa ne, amma kuma duk hakan ba wani babban matsala bane idan har ze kiyaye to da taimakon Allah komai zezo masa cikin sauΖ™i!”

STORY CONTINUES BELOW

Salati Alhaji Ma’aruf yayi a bayyane haΙ—e da sanya hanu yazame hular dake kansa,  ashe bayan giya hadda wata tsinanniyar Ζ™waya me haΙ—ari Zaid yake sha? anya kuwa Zaid yanada cikakken hankali? shin wani irin haline haka da Zaid? amma babban abun tambayar shine laifin waye acikinsu, laifinsune su iyayensa kokuwa laifinsa ne shi kansa Zaid Ι—in?

“HaΖ™iΖ™a dukansu suna da laifi, amatsayinsu na iyaye basu wani tsaya sunbawa Zaid kyakkyawar kulawa ba, kuΙ—i kawai suka sake masa haΙ—e da turasa makaranta har wata uwa duniya, amma duk da haka bekamata ace yakasance haka ba, idan su basa lura da al’amuransa shi Ι—in mahaukaci ne da be san dede ba?   tabbas yasan shiyake da alhakin kulawa da tarbiyan Zaid tunda shine yaΙ—aukosa daga wajen Mahaifiyarsa yadawo dashi  America kusa dashi,  tunda suke America bai taΙ“a tsayawa da kyau yakula da wani irin rayuwa Zaid Ι—in keyi ba, shide kawai yabuΙ—e masa bakin aljihu yana ganin hakan shine gata,  Ζ™warai mafiyawancin iyaye ayanzu sunfi bada kulawarsune ga Ζ³aΖ΄a mata, yayinda Ζ΄aΖ΄ansu maza kuwa ko oho, duk wata kyakkyawar tarbiya Ζ³aΖ΄a mata ake Ζ™oΖ™arin koyawa, yayinda Ζ³aΖ΄a maza kuwa suka zama hoto, aganin iyaye komiye Ι—a namiji yayi adone bakamar Ζ΄a mace ba, tabbas hakane duk abun da Ι—a namiji yayi adone bakamar mace ba, amma hakan bawai yananufin shi Ι—a namiji abarsa sakaka haka bane batare da annuna masa kulawa ba,  shi namiji a koda yaushe ana ganin zai iya kula da kansa, amma yana da kyau ana nuna masa kulawa ana kuma jansa ajiki kodan yasamu inda zena faΙ—an damuwarsa, kowafa yanason yasamu tarbiya me kyau daga Namiji har mace, saboda haka yazama lalle iyaye su tashi tsaye wajen kulawa da Ζ΄aΖ΄ansu maza saboda ba mata ne kaΙ—ai suke buΖ™atan kulawa ba harsuma maza suna buΖ™ata……

Dr.Bilal ne yakatse Dad daga tunanin da yafaΙ—a me zurfi tahanyar cewa da yayi dashi.    “Zaid yana buΖ™atar hutu saboda haka sai nan da 4 hours kafun su samu ganinsa”

Jiki ba Ζ™wari haka Dad yafito daga office Ι—in  yanufo inda su Mom ke tsaye suna sharce hawaye..

“Yaya de Alhaji me likitan yacema?” Mom tatambaya cike da damuwar son sanin wani hali Ι—anta yake ciki..

“Kada kidamu, ku kwantar da hankalinku jikinsa da sauΖ™i zuwa anjima kuma insha Allah zamu samu ganinsa yanzu likita yace yana buΖ™atar hutu ne, to dole zamu barsa yaΙ—an huta” Dad yaΖ™are maganar yana me kamo duka hannayen mom alamun rarrashi..

Hamdala Mom tayi haΙ—e da sauΖ™e ajiyar zuciya

Sake kallon Dad tayi cikin yanayi na tuhuma tace “Meyasanya naga fuskarka Ι—auke da tashin hankali me tsanani Alhaji?”

Murmushin dole Dad yanemo ya ara akan fuskarsa bayason faΙ—a mata wan nan maganar yanzu yafiso saisun samu nutsuwa sunkoma gida tukunna, sai de kuma abun da shi besani ba shine tafikowa sanin cewa Zaid yanashan giya, saboda tasha kamasa acikin maye yayi mankas, san nan kuma tajima da sanin cewa yanashan Ζ™wayoyi, sede abun da bata sani ba shine haΙ—arin da Ζ™wayoyin suke Ι—auke dashi….

********

Haka Zahrah tawayi gari yau da zazzaΙ“i sede duk da haka bata nunawa kowa cewa bata da lafiya ba, sede kuma idanunta sun kunbura sakamakon kukan da taci ta Ζ™oshi a daren jiya..

Haka de tashirya kanta tsab don zuwa makaranta amma kowa yaganta yasan bata da wani isashshen kuzari a tattare da’ita,, ko abun kari bata tsaya taci ba haka ta fice a gidan nasu….

********

“Kuka bazai taΙ“a yimiki maganin komai ba Zahrah, tabbas nasan kinajin raΙ—aΙ—i a cikin zuciyarki amma zuwa yanzu yakamata ace kimanta da baya kifuskanci gaba,   aure zakiyi  yanzu babu amfani kicigaba da sanya kanki cikin Ζ™unci!” Husnah tafaΙ—i haka ga Zahrah cikin yanayi na tausasawa, kasancewar duk wunin yau Ι—in da sukayi amakaranta bata gane kan Ζ™awarta ta ba…

Hannayen Husnah duka Zahrah takama haΙ—e da kallonta.  Cikin murya me rauni tasoma cewa…..

“Ni kaina inaso naganni cikin farinciki Husnah, amma nasan hakan bazai samu ba matuΖ™ar Zaid yana raye a doron Ζ™asa,  koda ma ace baya raye nasan bazanyi farinciki ba Husnah saboda yariga daya gama lalatamin rayuwa, bana tunanin cewa  akwai wani namiji da zaiyi Ι—okina idan ya aureni?  Shifa budurci wani abune me matuΖ™ar mahaimmanci a rayuwar Ζ΄a mace Husnah, babu wani mutumci dakuma karamci wanda ya wuce mace takai budurcinta Ι—akin mijinta,  mafi ganganci da kuskure da mace zata aikata kafun aurenta shine ta yarda ta bawa wani  kyautar budurcinta,   mata irina suna da yawa Husnah wa Ζ΄anda aka mawa fyaΙ—e aka Ζ™waci budurcinsu da Ζ™arfin tsiya, san nan kuma akwai waΖ΄anda maza suke ruΙ—ansu da kuΙ—i ko kuma da soyayya harsu yi nasaran rabasu da budurcinsu,  san nan akwai kuma wanda dan kansu suke bada kyautar nasu budurcin  ga wani daban,   rasa budurci abune me matuΖ™ar ciwo Husnah musamman ma ga iri na wanda aka mawa fyaΙ—e, Yawancin maza suna fatan idan sunyi aure  su samu matansu  da cikekken mutumcinsu, inde kuwa har a matsayin budurwa suka aureta,  haΖ™iΖ™a akwai wata soyayya dakuma girmamawa dake shiga tsakanin mace da mijinta matuΖ™ar takawomasa  budurcinta Ι—akinsa, saΙ“anin haka kuwa shike hargitsa tunanin namiji, shike jagulawa mace zaman aure’nta, koda ace ya yarda Ζ™addarane hakan amma tabbas wani lokaci abun zaina masa ciwo, duk da nasan cewa Dr.Sadeeq yasan komai daya faru dani, amma duk da haka tabbas nasan duk randa yakusanceni saiyaji ciwo acikin ransa, saikuma yaji wani abu saΙ“anin tunaninsa, shi a yanzu yana ganin cewa hakan bakomai bane, amma kuma hakan komai ne bakuma ze gane hakan ba sai randa ya aureni yakuma nemi dana basa haΖ™Ζ™insa na aure,,   wan nan ranan nake gujewa kaina  Husnah bansan ina zan tsoma kai da zuciyata ba amma nabarwa Allah komai!!” gaba Ι—aya hawaye sungama wankewa Zahrah da Husnah fuska, lalle kuwa wan nan itace mummunar Ζ™addara wand ba’a taΙ“a mantawa da’ita,,  rungume Zahrah Husnah tayi cike da tsananin tausayin Ζ™awarta ta,,, tabbas duk abun da Zahrah tafaΙ—a gaskiya ne kai budurci Ι—akin miji yafi komai daΙ—i a rayuwa saboda ko ba komai zaiΖ™ara muku danΖ™on soyayya dakuma mutunta juna, duk da cewa Zahrah ba’asonta tarasa budurcinta ba amma kuma tabbas kamar yanda Zahrah ta faΙ—a hakan yake dolene Dr.Sadeeq zaiji zafin abun sosai aduk ranarda kusantar farko tashiga tsakaninsu, amma kuma babu wanda ya isa ya tsallakewa Ζ™addararsa…..

STORY CONTINUES BELOW

Hawayenta tasanya hanu tashare kafun tashiga sharewa Zahrah ma nata hawayen,,,,   

“Ki kwantar da hankalinki Zahrah komai zai zo cikin sauΖ™i insha Allah taso muje musamu ruwa muwanke fuskarmu ko”

Ba musu Zahrah ta tashi tsaye Husnah takama hanunta suka nufi wajen da sukasan zasu samu ruwa……

***********

Jigum haka su Dad  dake tsaye  agefen gadon Zaid sukayi, yanzu awa 5 kenan suna irgawa batare daya buΙ—e idanunsa ba, gashi kuma  4 hours likita yace musu zaiyi….

Babban yatsar Ζ™afansane tasoma motsawa kafun idanunsa da sukayi nauyi suka soma buΙ—ewa a hankali,, da sauri Dad Ι—insa yaΖ™araso jikin gadon yanayi masa sannu…

ƘoΖ™arin tashi zaune yasomayi da sauri Dad Ι—insa yamaidasa ya kwanta “Ba sai ka tashi ba Zaid yakamata kabari kaΙ—an wastsake tukunna kafun kasoma yunΖ™urin tashi”

Ɗan yamutsa fuska Zaid yayi haΙ—e dabin ledar ruwan da aka Ι—aura masa da kallo.

Dai de lokacin Labisat suka shigo ita da Dr.Bilal domin dama Mom naganin Zaid Ι—in yabuΙ—e ido tace da Labisat tayi mata Ζ™iran Doctor…

Ζ³an gwaje gwaje Dr.Bilal yayi masa haΙ—e dayi masa wasu Ζ΄an tambayoyi, ko motsawa bakin Zaid beyiba balle Dr.Bilal yasa ran samun amsa, ganin haka yasa Dr.Bilal yin murmushi batun yauba yasan Zaid Ι—in saboda haka shirun da Zaid Ι—in   yayi masa bawani abu bane daya kamata ace yadamu ba,,  kallon Dad Dr.Bilal yayi haΙ—e da cewa

“Ko yanzu idan kuna buΖ™atar sallama se a baku saboda babu wata damuwa, se daifa a kiyaye kamar yanda na faΙ—a”

Kai Dad yajinjina haΙ—e da cewa “Shikenan Doctor insha Allah za’a kiyaye, muje sai nakarΙ“i takardan sallaman ko”    Dad da Dr.Bilal suna fita Zaid yatattaro duka wani kuzarinsa dayayi masa saura yamiΖ™e tsaye, kafaΙ—un Labisat dake tsaye kusa dashi ya kamo haΙ—e da Ι—aura hanunsa akan kafaΙ—an nata suka nufi hanyar fita daga Ι—akin, domin kuwa koda Dr.Bilal be basu sallama ba tabbas bazai Ζ™ara 1 hour a cikin asibitin ba…

Yana riΖ™e da kafaΙ—an Labisat harzuwa cikin mota, shida Labisat  mota Ι—aya suka shiga, yayinda su Dad da Mom suka shiga wata motar wanda duk su sukazo da ita… Direct  gida suka nufa

Idanunsa gaba Ι—aya suna a lumshe yayinda yajingina bayansa a jikin kujeran motar wanda yake zaune akai.

Ɗan satan kallonsa Labisat tayi hakanan taji wani irin mugun tausayin Ι—an uwan nata ya kamata, tabbas basuyi wani shaΖ™uwa da yayan nata ba amma tafuskanci cewa yanacikin damuwa, takuma tabbatar da cewa sanadin damuwarne ma har ya kaisa ga kwanciya a asibiti, to wan nan wace irin damuwace yayanta yake ciki haka? tabbas zataso sanin damuwar dake damunsa  saboda tana matuΖ™ar son Ι—an uwan nata bandashi batada wani Ι—an uwa dasuke uwa Ι—aya uba Ι—aya shikaΙ—aine yayanta kuma garkuwanta……

Koda suka isa gidama Labisat ce tarakasa har Ι“angarensa,,  zama yayi akan kujera haΙ—e da jawo wani Ι—an Ζ™aramin table Ι—in dake tsakiyar falon yaΙ—aura Ζ™afafunsa akai..

“Yaya mezan kawo maka, yakamata kasa wani abu acikin ka!”  cike da Ι—ar Ι—ar Labisar tafaΙ—i maganar saboda tasansa sarai ba’a iyarmasa yanzu saiya saceka..

“Friedrice” yafaΙ—a a taΖ™aice batare kuma daya buΙ—e kyawawan idanunsa dasuke a lumshe ba..

Jiki na mazari haka Labisat ta tafi kawo masa friedrice Ι—in dayace, domin kuwa dama agidan nasu ba a rasa friedrice..

Mintuna kaΙ—an tadawo hanunta Ι—auke da Ζ™aton tire hadda plate Ι—in  yankakkun kayan marmari akan tire Ι—in,, adede gabansa ta ajiye tire Ι—in haΙ—e da Ι—aukan plate ta buΙ—e kulan da friedrice Ι—in ke ciki ta zuba masa.

“Yaya gashinan na kawo” tafaΙ—a tana me tura masa plate Ι—in friedrice Ι—in gabansa.

Ganin da tayi bece da ita komai ba yasanyata miΖ™ewa sumu sumu tafice daga falon nasa…

STORY CONTINUES BELOW

Jawo plate Ι—in yayi gabansa yasoma tsakuran abincin yanaci kaΙ—an kaΙ—an duk da kuwa bawai buΖ™atar abincin yakeyi ba adole kawai yakeci…   Lomansa huΙ—u ya aje spoon Ι—in dake hanunsa haΙ—e da jawo plate Ι—in yankakkun kayan marmarin dake gabansa yasoma sha,  sai alokacin yasoma jin daΙ—in bakinsa, amma da kwata kwata bayajin Ι—anΙ—anon komai,, fruits Ι—inma baiwani sha me yawaba haka yature yakuma maidakansa yajingina da kujera,, idan akwai abun dayake Ζ™auna dakuma muradin gani yanzu arayuwarsa baiwuce Zahrah ba, dole yaje gidansu ayau Ι—in koda kuwa idan yaje zata Ι—auki wuΖ™a ne taluma masa a cikinsa…..

Yauma de kamar kullum Zaune take a tsakar gidan nasu,  kwanon abincine aje agabanta tana tsakura da kaΙ—an kaΙ—an tana kaiwa bakinta domin kuwa haryanzu bata wani jin daΙ—in jikinta..

Inna ce zaune daga gefenta tana ta Ζ™oΖ™ari wajen ganin ta seta tashan radion ta..

Wani yarone yayi sallama yace wai ana Ζ™iran Zahrah,,   “Jekace tanazuwa” Inna tahanzarta faΙ—a, har yaron yakama hanyar fita daga gidan, Zahrah ta tsaidasa haΙ—e da cewa “Kace bazata zo ba”

Hangame baki Inna tayi tana kallon Zahrah “Bazakijeba fa kikace?”

“Eh Inna dan Allah kuma kada kitambayeni dalili” tayi maganar tana me langwaΙ“ar da kanta gefe.

Harara Inna ta watsa mata haΙ—e dayin tsuka baΖ™in ciki kawai Zahrah’n takeyi mata wayasani ma ko wanda ke Ζ™iran nata da alkhairi yazo…

“Wai Bazata zoba” yaron nan yafaΙ—awa wanda ya aikosa.

Waro idanu Zaid yayi maganar ma shi dariya taso basa, amma a irin wan nan yanayin dayake ciki bayatunanin zai iyayin dariya…

“Wayene yacema bazata zo ba?” Zaid yatambayi yaron.

“Ita da kanta” yaron yabasa amsa domin kuwa shiΙ—in Ι—an maΖ™otansu ne saboda haka yasan Zahrah’n.

Kai Zaid yajinjina haΙ—e da cije laΙ“Ι“ansa,,  Allah sarki rayuwa babu yanda bata juyawa mutum, amma in banda haka wai yau shine a wata Ζ™asΖ™antacciyar unguwa kuma Ζ™ofar gidan su mace yakuma aika tace bazata zo ba, shine fa Zaid Ι—in da har gobe Ζ΄an mata suke rushing akan sa, to amma meyasa haka takasance dashi?”   ganin da yayi yaron nashirin tafiya ne yasanya yace “Kaje kace injini nace tayi haΖ™uri tafito”   bamusu yaron yakoma yakuma faΙ—i saΖ™on da akabasa umarnin yafaΙ—a..

Tsuka Zahrah taja haΙ—e da tashi tsaye  “Kaje kace wai inji Zahrah kozai mutu a tsaye baza ta zoba” tanakaiwa nan azancenta tayi wucewarta Ι—aki..

Abunda Zahrah tafaΙ—a shi yaron nan yazo ya sanarwa Zaid,   kuΙ—i Zaid yaciro a aljihunsa 1k yabawa yaron  dafari yaron yatsorita yaΖ™i amsa, amma Zaid yatilasta masa saida ya amsa, haka yaron yatafi yana murna…

Motarsa yabuΙ—e yashiga yayinda yakifa kansa a steering motar meyasa soyayya zata masa haka, idanunsa Zahrah kawai suke son gane masa tabbas yau bazai taΙ“a iya runtsawaba matuΖ™ar baiga Zahrah ba,  yana mawa Zahrah wani irin mugun so me tsananin zafi..      Jan motarsa yayi yakoma Ζ™arΖ™ashin wata bishiya tayanda bakowa zai lura da cewa yana wajen ba, yaΖ™udurta aransa cewa koda zai kwana a wajen ne bazai gusa ba harsai idanunsa sun mai tozali da Zahrah….

Bayan awa Ι—aya

Zahrah ce tafito daga cikin gidan nasu sanye da wani siririn mayafi wayarta ce riΖ™e a hanunta se kuma wani littafi.     Zaid dake zaune cikin motarsa yana ganinta ya sake waro idanu haΙ—e da sauΖ™e ajiyar zuciya me Ζ™arfi,   jiyakeyi tamkar yaje ya Ι—auΖ™ota can caΙ—ak yatafi da ita… Yana kallonta tayi shigewarta wani gida dake kusa da nasu gidan.. Bayan kamar mintuna 8 da shiganta gidan yaga takuma fitowa  da sauri yabuΙ—e murfin motarsa daniyar Ζ™arasawa gareta sai de kuma ko taku biyu baiyiba tashige cikin gida ko ganinsa ma ita batayi ba,  haushine yasanyashi buga tayar motarsa da Ζ™afarsa,      haka yakoma yayiwa motarsa key haΙ—e dayin reverse yabar unguwar tasu cike da Ζ™uncin rashin samun daman yi mata magana da be yiba, amma de yaji sanyi sosai a zuciyarsa daya ganta…

*********

Yau tunsafe Zahrah tashiga busy hidama kawai sukeyi ita da Husnah domin kuwa yaune ranar da Dr.Sadeeq yace mata za’a kawo lefenta,,   yanzuma daga shopping suke sunje sun sayo kayan drinks da kuma su snacks wanda za’abawa baΖ™i.  Zama sukayi akan tabarma suna me da numfashi saboda sungaji sosai,,,   kallon Zahrah Husnah tayi haΙ—e da sakin murmushi.

“Ƙawata nifa yau daΙ—i nakeji jinake tamkar ma nice za’a kawowa lefen”   dariya Zahrah tayi haΙ—e dacewa “To aike kince bayanzu zakiyi aure ba saikin gama school gashi Nuruddeen yana tsananin son kuyi aure amma ke kinΖ™i”

“Hmm ai zan masa maganane yaturo kawai domin ni mafa yanzu dagaske auren nakeso nagaji da rungumar pillow idan nazo bacci” Dariya suka sanya su dukansu hadda tafawa,   “Allah yashiryeki Husnah” Zahrah tafaΙ—a tana dariya..  Haka de sukaci gaba da Ζ΄an hirarrakinsu irin na Ζ™awaye……….

Ƙarfe biyar dai dai wasu rantsa rantsan motoci suka soma tsayuwa a Ζ™ofar gidan su Zahrah duk macen da tafito acikin motar sai kaga tana yatsuna fuska haΙ—e da soma Ζ™arewa wajen gidansu Zahrah kallo,   motocine kusan guda goma sha biyu suka kawo kayan lefen ahankali aka shiga fito da akwatuna ana shiga dashi cikin gidan su Zahrah..  Fuska babu yabo ba fallasa haka matan nan suka soma shiga cikin gidansu Zahrah,,,,, da fari’a Inna da tawagarta suka tarΙ“i mutanen haΙ—e da basu wajen zama, haka suka zauna wasu daga cikinsu suna yatsuna fuska kamar wanda akace su zauna akan kashi…

“Sannunku da zuwa lale marhaba” Wata mata maΖ™ociyar su Zahrah tafaΙ—a ga matan da suka kawo lefen.  Amma kuma daΖ™yar aka samu biyu daga cikinsu suka amsa mata..

Akwatuna ne harguda shabiyu aka jibge akan wata tabarma dake shimfuΙ—e,,  su Inna ne suka fara Ι—agawa matan da suka kawo lefen gaisuwa ciki ciki suka amsa musu cike da isa,,,,,  Aunty Raliya ce ma tayi Ζ™arfin halin cewa  “Ga kayanan munkawo Allah yasa ayi bikin a sa’a,  Allah kuma yasa asamu kyakkyawar zuri’a”  dagajin yanda tayi maganar kaΙ—ai ya isa ya tabbatarmaka cewa kalaman ba anyi su bane cikin daΙ—in rai,,,  da Ameen kawai su Inna suka amsa musu,,,  kuΙ—i Aunty Raliya taciro acikin jakarta bandir Ι—in Ζ΄an dubu dubu har na dubu Ι—ari ta Ι—aura akan wani akwati haΙ—e da kallon Ζ΄an uwanta tace  “Muje ko”   dukansu miΖ™ewa sukayi suka nufi hanyar waje,,, yayinda Inna tasa yaran maΖ™otansu suka kwashi kayan tarban baΖ™in da suka musu aka kai musu cikin mota, maman Badi’a Ι—aya daga cikin maΖ™otan su Zahrah ita tazari dubu hamsin daga cikin kuΙ—in da suka aje tabawa Ζ΄arta Badi’a tace takaiwa matan dasuka kawo lefen,,,  dawowa da kuΙ—in Badi’a tayi tace ae sun riga da sun tafi koda tafita Ζ™urar motarsu kawai tagani,,, “To suko wasu irin mutanene haka ae ba haka akeyi ba, ko fa kayan basu tsaya sun nuna mana ba saikace wanda suke akan Ζ™aya” Maman Badi’a tafaΙ—i haka cike da mamakin hali irin na matan da suka kawo lefen,,,    washe da baki wata mata daga cikin gayyar Inna tace “Kai amma kuwa Zahrah tayi goshi kuga kayafa kamar wanda za a buΙ—e kanti” ae kuwa basusan cewa Zahrah tayi goshi ba saida suka soma buΙ—e akwatunan,, kowanni akwati shaΖ™e yake da kaya nagani na faΙ—a,, take Inna tasoma rangaΙ—a guΙ—a hadda rawan murna…….Hayaniya haΙ—i da guΙ—an da su Inna keyi  shiyayi sanadiyar janyo hankalin Zahrah dakuma Husnah da suke zaune a Ι—akin Zahrah sunyi muΖ™us,,,,+

“Ke nifa tashi zanyi naje nabawa idanuna abinci, dan wlh bazan iya zama aΙ—aki kamar wata sabuwar amarya ba, ke dai da zaman yazamemiki dole saiki ta fama” Husnah tafaΙ—i haka tana me miΖ™ewa tsaye daga zaunen da take,,,  murmushi kawai Zahrah tayi mata haΙ—e da binta da kallo hartafice daga cikin Ι—akin…

Hamdala Husnah tayi haΙ—e da nunatsantsar farincikinta alokacin da idanunta sukai mata tozali da kayan lefen Ζ™awartata,,,, lallai Dr.Sadeeq yayi Ζ™oΖ™ari domin kuwa naira tayi kuka, koda kyawun akwatunan aka barka sun isa sanyaya maka rai, balle kuma aje ga kayan ciki masu kyau da tsadar gaske, wan nan shiyasake tabbatar mata da cewa Zahrah bazatayi kuka ba idan ta auri Dr.Sadeeq, saboda me sonkane kaΙ—ai zai iyayin komai dayasan zai faranta maka rai….

Duk yawan atamfofin dake cikin akwatunan nan saida su Inna suka irgesu kaf, turame hamsin banda su laces haΙ—i da shaddodi dakuma  dangin su materials,,     Ι“angaren dogin riguna ma akwati guda aka cika dasu, sosai kuma yasaki bakin aljihunsa wajen zaΙ“o masu kyau da tsada,,  haka Ι“angaren sarΖ™okima komai yaji domin kuwa kaf cikin sarΖ™oΖ™i da Ι—an kunnayenta babu wani mai sauΖ™in kuΙ—i acikinsu gwala gwalanta har guda uku,, san nan kuma Ι“anagaren jaka da  takalma ma yayi Ζ™oΖ™ari sosai, domin kuwa  kusan kowani kaya yanada jaka da takalmi hadda mayafinsa,, wajen kayan shafa ma yayi Ζ™oΖ™ari sosai  wajen fidda naira yasai kayan shafa Ζ΄an yayi masu kyau duk da kuwa yasan cewa ita ba gwanar kwalliyan fuska bace…

“Gaskiya kaya yayi kyau yarinya tayi goshi,  ai wan nan kayan ko Ι—iyar babban attijiri sai haka” Maman Badi’a tafaΙ—i haka bayan taΖ™arewa wani haΙ—aΙ—Ι—en leshi dake riΖ™e a hanunta kallo wanda a Ζ™alla kuΙ—insa zai kai 50k,,,

“Ƙwarai kuwa yarinya tayi goshi Maman Badi’a ai dama tuntuni nasan fiye da haka ma sai yafaru, ga kaya kan nan harda nasadakarwa!” Inna tafaΙ—i haka cikin murna…

Wata dake zaune kusa da Inna tace “wan nan haka yake muma dai Allah yabawa namu Ζ΄aΖ΄an mazajen aure masu Ζ™ashin arziki” 

Duka matan suka haΙ—a baki wajen cewa Ameen domin kuwa babu wacce  zataΖ™i ace Ζ΄arta ce tasamu wan nan kayan more rayuwan….

Sai kusan magriba matan dasuka karΙ“i lefen Zahrah suka  soma tafiya, bayan Inna ta yaga musu wani abu daga cikin dubu hamsin Ι—in daya rage,, haka suka tafi suna mata godiya suna kuma zuba santin kayan domin kuwa koda maΖ™iyin Zahrah ne yaga wan nan uban kaya da Dr.Sadeeq yayi mata tabbas dole sai ya jinjina abun…..1

Lokacin da Zahrah taga irin yawan kayan lefen da Dr yayi mata kasacewa komai tayi,  sosai abun yabata mamaki domin kuwa bata taΙ“a zaton zai Ι“arnata dukiya mai yawa harhaka wajen yi mata lefe ba, bayan kuma yasan cewa ita ba cikakkiyar budurwa bace,,, sai de taΖ™udura aranta cewa zata faΙ—a masa   kayan sunyi yawa……

STORY CONTINUES BELOW

Gidansu Doctor…

“Gaskiya da sake Hajiya, yakamata a dakatar da wan nan batun auren na Sadeeq da yarinyar nan,  kinkuwa ga gidansu Hajiya? wlhy ko suminti babu a tsakar gidansu zallan turbuΙ—in yashine, kallo Ι—aya zakai musu kafuskanci cewa suΙ—in faΖ™ara’une basu da komai, kwata kwata ma Sadeeq baisan inda zaije ya nemo aure ba domin a wan nan gidan bana tunanin akwai wata halitta da zata burge wani Ι—a namiji acikinsa, kawai dai ni inaga ma asiri sukayi masa wlhy, amma bacin haka banjin dakansa zaije neman aure wan nan gidan!” Auntie Raliya ce ke faΙ—an haka cikin Ι“acin rai…..

Ajiyar zuciya Hajiya tayi cikin Ι—acin rai tace  “Hmmm Raliya kenan aeni ban isa hana wan nan auren ba ko kinmanta cewa har Ζ™arana wajen Baffan ku Sadeeq yakai akan naΖ™i amincewa da aurensa,  ni yanzu baruwana acikin lamarin aurensa ko mai ya jajiΙ“owa kansa shiya sani”

Ƙwafa Auntie Raliya tayi haΙ—e da sakai tafice daga cikin Ι—akin Hajiyar, harga Allah ita sam batason wan nan auren da Sadeeq zaiyi, yarasa ma wacce zai kwaso musu sai wacce wani ya haiΖ™ewa a waje san nan kuma Ζ΄ar talakawa futuk…

Auntie Raliya tana fita falo Ζ™awayenta da ta gaiyato suka kai lefe  tare, sukayi caaa akanta kowacce tana ingizata akan cewa tasa afasa auren domin kuwa sam ajin  Sadeeq  yagirmewa neman aure a wan nan gidan matsiyatan,,, take kuwa Auntie Raliya tahau kan zancen tazauna dabas, takuma Ζ™uduri aniyar lalata zancen auren abune me sauΖ™i kuma dakanta zataje ta kwaso kayan lefen Ζ™anin nata……..

1

Ɓata fuska Zahrah tayi haΙ—e da tunzuro Ι—an Ζ™aramin bakinta gaba  cike da shagwaΙ“a tace “Dagaske nake faΙ—a maka kayan lefen nan sunyi yawa, ko Ι—azu dawowan Baffa daya gani shima haka yace, kuma kafasan ba kyau yin wasa da dukiya” taΖ™are maganar tana me langwaΙ“ar da kanta gefe.

Murmushi Dr.Sadeeq yayi haΙ—e da kwantar da bayansa ajikin kujeran motar dayake zaune akai kana ya lumshe gajiyayyun idanunsa, sautin muryarta nayi masa daΙ—i sosai…

Shirune yashiga tsakaninsu har na tsawon minti Ι—aya.

“Duk abun da mayi miki kin can can ci haka daga gareni ne Zahrah, dan Allah kibar maganar yawan lefen nan, ni banga wani yawa da sukayi ba, naso ma nayi miki wanda yafi wan nan to abubuwane sukai min yawa, amma kin wuce haka a wajena, kuma kinsan ku biyu ne” yafaΙ—i haka yana me kafeta da idanunsa..

Murmushi kawai Zahrah tayi haΙ—e da kawar da kanta gefe, sam bataso idan yana kallonta itama ta kalleshi saboda takanjin nauyinsa awasu lokutan,, amma kuma hakanan taji kalmar dayace su biyu ne yaΙ—an sosa mata rai,  wato idan ma ta manta to yatuna mata…

Wani murmushin Dr.Sadeeq yakumayi sakamakon ganin yanda fuskarta ya Ι—an sauya lokaci Ι—aya yakuma san maganarsa ce batai mata daΙ—i ba, dama kuma yafaΙ—i hakanne don yagane cewa tana kishinsa ne ko a’a….

“Bansan wani irin daΙ—i da kuma farinciki zan tsinci kaina ciki ba aduk sanda wannan ranar  taruskeni, amma kuma da zanfi kowa jin daΙ—i idan har Allah ya gwadamin wannan rana!” yafaΙ—i haka cikin shauΖ™i, dason kawar da wancen zancen nasu..

Cike da mamaki Zahrah taΙ—an saci kallonsa haΙ—i da cewa “Wace rana ce wan nan?”

“Ranar da zaki zamo mallakina, ranarda za’akawomin ke Ι—akina amatsayin matata ta sunna, ranar da zan kwana ina kallon wannan kyakkyawar fuskar taki babuko Ζ™yafta ido”

Kunyane yakama Zahrah wanda haryakaita ga cusa kanta  tsakankanun cinyoyinta, sautari Dr.Sadeeq yakan faΙ—i abubuwan da suke sanyawa takejin kunyarsa sosai…

Murmushi Dr.Sadeeq yayi haΙ—e da sake kwantar da jikinsa akan kujeran motar,,,, yana matuΖ™ar son komai na Zahrah ciki kuwa hadda wan nan kunyar nata, tun asalinsa yanason mace me kunya, sai gashi kuma yanzu Allah yabasa, sai de kuma yasan nan gaba kaΙ—an zaisha fama da’ita saboda idan sunyi aure yasan wan nan halin nata na kunya zatai ta gwadamasa.

STORY CONTINUES BELOW

Kallon agogon dake Ι—aure a hanunsa na dama yayi.

“8:30pm” yafaΙ—a a bayyane  kana yadawo da kallonsa ga Zahrah wacce har yanzu bata Ι—ago kanta ba.

“Shikenan to tunda dai kunyana kikeji ni zantafi naga dare yasoma yi” yafaΙ—i haka adai dai lokacin da yake Ζ™oΖ™arin  Ι—aura sit belt ajikinsa..

Sai alokacin taΙ—ago kanta amma bata yadda ta kallesa ba,, “Sai da safe” tafaΙ—i haka tana me Ζ™oΖ™arin fita daga cikin motar domin dama taΖ™osa yace mata zaitafi saboda tagaji da zaman motan gashi tana da assigment kuma gobe zasuyi submit Ι—inshi, san nan kuma tana buΖ™atar kasancewa ita kaΙ—ai domin tattaunawa da zuciyarta a game da sabon al’amarin dayake shirin kunnu mata kai….

Kansa yajinjina haΙ—e da cewa “Dama so kike natafi ko?”

Murmushi tayi masa kana taΙ—an  girgiza kan ta alamar a’a, cikin murya me sanyi tace “Bahaka bane kawai de nafara jin bacci ne”

Kansa yakuma jinjinawa cike da gamsuwa  haΙ—e da juyawa baya yaΙ—auΖ™o wata farar leda dake aje kan kujeran gidan baya na motar.

“Idan Allah yakaimu da safe zanΖ™iraki ina fata zakiyi bacci me daΙ—i” yafaΙ—i maganar yana me miΖ™omata ledan dake riΖ™e a hanunsa…

ShagwaΙ“e fuska Zahrah tayi haΙ—e da marairaice manya manyan idanunta da suke sauΖ™ar masa da kasala aduk sanda ya kallesu,,   “Gaskiya ni dai a’a nagaji da wayon da kakemin, kuma tun ba yauba na faΙ—a ma hidiman dakakemin yana yawa!”

Lumshe idanunsa yayi  haΙ—i da buΙ—esu alokaci guda, idan yanaganin irin wan nan shagwaΙ“an nata to tabbas zata iya zautar dashi lokaci Ι—aya, yafice a hayyacinsa, domin shi shagwaΙ“an mace nasanyawa yaji feeling ajikinsa sosai,, cikin murya me sanyi yace “Kiyi haΖ™uri  ki Ζ™arΙ“a kinji princess Ι—ina, kinga ba kyu maida hanun kyauta baya!”

Sake turo baki tayi haΙ—e da kwaΙ“e fuska,    abun mamaki sai taga shima ya marairaice mata fuska kamar wani Ζ™aramin yaro,,  “Please!” yafaΙ—a cikin muryarsa da tayi Ζ™asa sosai..

Dole babu yanda ta’iya haka tasanya hanu takarΙ“i ledan haΙ—e dayi masa saida safe tafice daga cikin motar,,,  yanaganin shigewarta cikin gida yasaki murmushi haΙ—e da sanya hanu yashafi sajen dake kwance akan Ζ™uncinsa,  key yayi mawa motar haΙ—e dayin reverse yabar unguwar tasu.    Yana tuΖ™i amma shikaΙ—ai yaketa zuba murmushi, aduk sanda yake tare da Zahrah yakansamun kansa cikin farinciki da nishaΙ—i, tabbas yanayimawa Zahrah so me tsanani…..

Zahrah kuwa tana shiga cikin gida direct wajen da Inna ke zaune tanufa,  Ζ™oΖ™arin zama tasomayi haΙ—i dayimawa Inna sannu da gida.

Washe da baki Inna ta amsa mata bayan ta kafe Zahrah da’ido, Allah Allah take taga menene acikin ledan da  Zahrah ta shigo dashi..

Dariyane ya Ζ™wace mawa Zahrah sakamakon ganin yanda Inna ta tsareta da’idanu tamkar wata mayya.

“Dariyan uban me kike? banson shashanci wallahi” Inna tafaΙ—i haka ga Zahrah a hasale, ganin bata da shirin buΙ—e ledan…

Hannayenta tasanya ta toshe bakinta haΙ—e dasoma Ζ™oΖ™arin shanye dariyar ta.

Ledan da tashigo dashi ta buΙ—e tasoma dubawa gasassun kajine manya guda biyu sai kuma sauran kayan ciye ciye kamar su snacks dakuma chocolate,,

Ledan da kajin ke ciki ta ciro ta miΖ™amawa Inna ae kuwa hanun Inna har rawa yake lokacin da tazo karΙ“an ledan tsabar kwaΙ—ayi.

Fari’ar Inna ne yasake yawaita sakamakon ganin kaji da tayi, babu wani Ι“ata lokaci ta yago cinyar kaza Ι—aya takai bakinta,, tsabar daΙ—in kazar saiga Inna tana lumshe idanu haΙ—i da jijjiga kai.

Murmushi kawai Zahrah tayi haΙ—e da Ι—aukan sauran kayan tawuce Ι—akinta yayinda tabar Inna tayi pieces  tana cin kaza hadda rausayar da kai gefe alamar daΙ—inta takeji….

STORY CONTINUES BELOW

Jigum tayi haΙ—e da sake takurewa  waje Ι—aya akan Ζ΄ar katifartata,,,  tabbas Dr.Sadeeq yacancanci ta sadaukar masa da duka soyayyarta ko dan saboda halaccin da yayi mata a rayuwa, bazatace batasan menene so ba, itacema zata ba da labari akan so, domin ta Ι—anΙ—ana zafinsa me matuΖ™ar Ι—aci da dafi,,   idan tace Dr.Sadeeq baya burgeta tayi Ζ™arya, haka kuma idan tace Dr.Sadeeq baida abubuwan burgewa ajikinsa da zasu sa mace tasosa nan ma tayi Ζ™arya? tabbas Dr.Sadeeq baida wani makusa daga halayya Ι—abi’a harma da surarsa yacika cikakken namiji, amma babban abun dake damunta shine batajin tsananin soyayyarsa acikin zuciyarta, bawai tana Ζ™insa bane, kawai de zafin soyayyar tasa ne bataji a jiki da zuciyarta, ba kamar yanda taji na Zaid ba,, ada batajin soyayyar Dr.Sadeeq acikin zuciyarta amma ayanzu tayi Ζ™oΖ™ari wajen ganin takoyawa zuciyarta sonsa,  takuma yarda cewa zata iya zaman aure dashi domin baida wani makusa  atattare dashi wanda zaisa a Ζ™isa, murmushine yasuΙ“uce mata sakamakon tunowa da tayi da irin kallon dayakeyi mata Ι—azu, tabbas ya iya nuna soyayyarsa a fili, abu Ι—aya ne ajikinsa wanda yake Ι—aukar hankalinta,  shine Ζ™wayar idanunsa, duk da cewa shi Ι—in namiji ne amma yanada idanu masu kyau wanda zasu sanya maka nutsuwa aduk sanda ka kallesu, hakan yasa ako da yaushe takeson kallon cikin idanunsa amma bata iyawa saboda kunya….. Tunanin Zaid ne yakutso kansa cikin zuciyarta harsai da taji faΙ—uwar gaba,,    “Innalillahi wa’inna ilaihirraju’un!” shine abun da tashiga nanatawa acikin zuciyarta,, wannan wani irin bala’i ne? tunda Zaid yashigo cikin rayuwarta shikenan kuma komai nata ya ruguje, lallai itakam taΙ—aukeshi amatsayin annoba wanda gani da jinsa babu alkhairi …..1

Yau Kwanansa Ι—aya da wuni Ι—aya cur baisanya ko wani irin abinci abakinsa ba, sai ruwan giya dayake ta kwankwaΙ—a ba dare ba rana,, damuwa ce tayi masa mugun yawa abubuwa gaba Ι—aya sun caΙ“emasa,    kallo Ι—aya zakai masa kafuskanci cewa yanacikin halin damuwa, domin kuwa lokaci Ι—aya ya zabge rama ta bayyana kanta ajikinsa, yayinda manya manyan idanunsa suka sake fitowa waje,,    wani irin zafi zuciyarsa keyi masa, baisan da yaushene kuma ta yaya yakamu da soyayyar Zahrah me tsanani haka ba,     tunjiya yarasa nutsuwarsa a sakamon labari dayaji daga bakin wanda yasanya  yana kulamasa da shiga da ficen   Zahrah,  inda yasanar masa cewa ankawowa Zahrah kayan lefe, iya Ζ™ololuwar tashin hankali Zaid yashiga dajin wannan magana, sam be shirya wa rasa Zahrah ba saboda rasata dai dai yake da rasa rayuwarsa gaba Ι—aya, akuma yanda yakejin matsanancin sonta a cikin zuciyarsa zai iya sadaukar da komai nasa gareta, ko da kuwa ransa ne…

Yanzuma zaune yake yatusa wani Ζ™aton hoton zanen fuskarta daya zana a daren jiya a gaba yana kallo, saboda tsabar kyawun da zanen yayi idan kagani bazamakace zane bane…

Idanunsa dake kan idanunta na cikin zanen ne suka kaΙ—a sukai jajur dasu.  Saiyanzu yakejin tsanar kansa dakuma tsanar wannan banzan halin nasa, sai yanzu yake tsananin danasanin abun daya aikatawa Zahrah, haΖ™iΖ™a yasan cewa ya zalunci Zahrah ya cutar da’ita ya lalata mata rayuwa, kuma hakan da yayi mata shiya nisan ta masa ita, wani irin tsana ne Zahrah tayi masa haka? shin tasan irin zafi dakuma raΙ—aΙ—in dayakeji akanta kuwa? yadaina cin abinci tasanadiyar ta, wannan yasa  ulcer tayi masa mummunan kamu, gakuma soyayyarta da ta sanya masa ciwo a zuciya,, ta wani Ι“angare kuma yana fama da wani  matsanancin ciwon kai wanda dashi yake kwana yake kuma tashi, cikinsa kuwa tamkar anhura masa wuta haka yakeji aciki,, hanu yasanya yashafi zanen fuskartata, tabbas idan baisamu Zahrah ba bazai taΙ“a iya cigaba da rayuwa ba,,, abun da Zaid baisani ba shine tuni  ruwan hawaye sun cika idanunsa gangarowa kan fuskarsane kawai da basuyi ba,  zumbur haka yamiΖ™e tsaye haΙ—e da zura silifas Ι—insa ko wayoyinsa bai tsaya Ι—auka ba, haka yafice daga cikin Ι—akin nasa….

Yana fita compound Ι—in gidan nasu driver’n sa yaΖ™araso garesa da sauri,,,, “Oga fita zamuyi ne?” driver’n yatambaya cike da girmamawa,,  kai kawai Zaid ya Ι—aga masa alamar “eh”    jikin driver’n na rawa yace “Oga da wacce motar zamu fita?”

Cike da Ζ™osawa Zaid yace “Kowacce”

Driver yayi mamaki sosai dajin maganar Zaid domin yasan idan dai har fita Zaid Ι—in zaiyi to sai yazaΙ“i motar dayakeso amma kuma sai gashi yau yace kowacce..   Wata haΙ—aΙ—Ι—iyar baΖ™ar benz driver’n yatuΖ™o daga cikin parking space zuwa inda Zaid ke tsaye ya harΙ—e hannayensa acikin  aljihun wandon track suit Ι—in dake jikinsa..

Zaid nashiga cikin motar driver yabawa motar wuta yayinda me gadi ya wangale musu gate suka fice daga cikin gidan…..

Baffa ne zaune akan dakalin Ζ™ofar gidan yana me latsa Ζ΄ar Ζ™aramar wayarsa, zaman da yayi Zahrah yake jira ta dawo daga aiken da yayi mata,, daf dashi motar tayi parking, hakan yasa Baffa  ya kafe motar da’ido don ganin wanene zai fito daga ciki…

A hankali Zaid yabuΙ—e murfin motar yafito, kallonsa Baffa yashigayi daga sama har Ζ™asa saboda sarai yagane shine  Ι—an iskan me kuΙ—in da yamawa Zahrah fyaΙ—e,  saida Baffa yagama Ζ™aremasa kallo kafun yakawar da kansa gefe…

Da sallama Zaid yaΖ™arasa wajen Baffa,, ciki ciki Baffa ya amsa masa sallaman,    durΖ™usawa Zaid yayi haΙ—e dayin Ζ™asa da kansa cikin murya me sanyi yace “Kagafarceni Baffa, nasan ban kyautaba amma dan Allah kada ka hanani auren Zahrah, wallahi a yanda nakeji idan bansamu Zahrah ba mutuwa zanyi!”

Baki Baffa yasake yana kallon Zaid,  namiji har namiji amma wai yana cewa idan bai auri Zahrah ba mutuwa zaiyi kuji iskanci fa,,

Sake Ι—ago kansa Zaid yayi haΙ—e da watsawa Baffa jajayen idanunsa,   “Wlh Baffa yanzu da gaske nake aurenta zanyi, kada kace zaka hanani ita dan Allah, wallahi Zahrah tana da matuΖ™ar mahimmanci acikin rayuwata!”

Yanzukam kallon tsab Baffa yashiga yi masa saida yaΙ—auki kusan minti biyu yana kallon Zaid Ι—in kafun yaΙ—an nisa haΙ—e da cewa “BantaΙ“a tunanin kana da idanun da zaka dawo ka kallemuba, amma sai gashi kadawo kana kallona har kuma kana roΖ™ona dana baka auren Zahrah, idan da kanasonta tunfarko mai yasa baka aureta ba kalalata mata rayuwa? ni bazance maka komai ba saide ince munbarka da Allah saboda bamu da yanda zamuyi dakai, amma kuma kasani bazan baka auren Zahrah ba harsai da amincewarta, idan har tace ta amince zata aureka shikenan nime iya baka aurenta ne” Baffa yana kaiwa nan a zancensa yatashi yayi shigewarsa cikin gida.. Da Ζ™yar Zaid ya’iya tashi ya  zauna akan dakalin da Baffa yatashi hannayensa duka biyu yasanya ya dafe kansa dake yi masa nauyi kamar ze faΙ—o Ζ™asa…..

Da Ι—an sauri take tafiya tana latsa wayanta burinta kawai shine taganta acikin gida, duk sanyin da akeyi yau yagama ratsata, saboda haka take Allah Allah ta’isa gida.. sam bata lura da akwai mutum a Ζ™ofar gidan nasu ba dan hankalinta gaba Ι—aya nakan wayartata…

“Zahrah!” taji anΖ™ira sunanta da murya wacce bazata taΙ“a mantawa da’ita ba a iya tsawon rayuwarta…

Ja tayi  ta tsaya haΙ—e da maida kallonta inda taji sautin muryar tafito,, tabbas kuwa  ba gizo kunenta keyi mata ba shiΙ—inne dai, kallonta yashigayi da idanunsa wanda suka zama jajaye, itama tsayawa tayi tana kallonsa, a wannan karon kam babu alamar wasa kokuma tsoronsa akan fuskarta,, kallonsa takeyi ido cikin ido…

“Dan Allah Zahrah ki saurareni, wallahi inasonki inamiki so me tsanani, inamiki soyayyar da babu wani wanda zaiyi miki shi a duniyar nan, meyasa bazakisoni ba Zahrah? Inasonki, Inasonki, Inasonki da duka zuciyata, dan Allah kiyarda muyi aure Zahrah!” cikin rauni yaΖ™are maganartasa saikace ba jarumin namiji ba…

Kallonsa Zahrah tashigayi tundaga Ζ™asan sa harzuwa samansa, wani irin murmushi tayi masa wanda ita kaΙ—ai tasan ma’anarsa,,,      “BantaΙ“a tunanin zaka iyayin wannan jarumtar ba,  Ζ™warai kayi Ζ™oΖ™ari dahar ka iya tunkarana da wannan maganar, sai de kuma tun awancan lokacin na faΙ—amaka kafita a rayuwata, idan duka mazan duniya zasu Ζ™are na gwammace na mutu babu aure dana aureka,  ka kalleni da kyau bancancanci zama matar mazinaci kuma Ι—angiya ba,  niba irin matan nan bane da yacancan ci fasiΖ™ai irinka su samuba,  natsaneka Zaid tsana me tsanani, wlhy danaga ranar da zan zamo matarka gwamma acemin naga ranar mutuwa ta,  katafi kawai Zaid kaje nabarka da Allah, kuma inaso kasani cewa yau Ι—in nan za’a tsaidamin ranar aurena da wanda zuciyata ta aminta dashi, wanda yake kamili me tsoron Allah,  shi ba kamar kai bane Ι—an giya!” tanakaiwa nan azancenta tajuya daniyar shigewa cikin gida…

Dasauri Zaid ya kamo hanunta haΙ—e da jawota  da Ζ™arfi tafaΙ—a cikin jikinsa, dai dau lokacin ne kuma motar Dr.Sadeeq taΖ™araso wajen….Saurin turesa tayi haΙ—e da hankaΙ—asa gefe da iya Ζ™arfinta ta Ζ™wace jikinta daga nasa, wani irin mugun kallo tashiga yimasa haΙ—e da tofar da yawu aΖ™asa, da ace wulaΖ™anta Ι—an adam abune me kyau to tabbas da akan fuskarsa zata tofa wan nan yawun ko hakan zai sanya ya gamsu da irin tsantsar tsanar da takeyi masa.

“Banafatan na sake haΙ—a jikina da wan nan Ζ™azamemmen jikin naka mai Ι—auke da tarin najasa!” cike da tsananin Ζ™yamata Zahrah ta faΙ—i haka ga Zaid haΙ—e da juyawa tanufi hanyar shiga gida..+

“Koda kuwa na daina aikata zina nakuma daina shan giya?” Zaid yafaΙ—i haka cikin dakakkiyar muryarsa…

Cak ta tsayawa daga tafiyan dakeyi, sosai maganar tasa ta daki zuciyarta..

A hankali yashiga takowa zuwa inda take saida yazo gaf da’ita kafun ya tsaya……. ” I promise to leave all my bad habit if you wish to marry me, I love you Zahrah, trust me for the sake of God, i will not hurt you!” gaba Ι—aya muryarsa tayi rauni dagajin muryartasa kasan cewa yana cikin matsanancin damuwa…1

Idanunta da suka kawo ruwa ta Ι—ago ta watsa masa su,,,,, Shi Ι—in ma kallon ta yakeyi da idanunsa wanda suka zama tamkar an watsa musu garin barkono,, sun Ι—auki tsawon mintuna biyu suna kallon juna kafun da ga bisani Zahrah tajuya ta shige cikin gida, ko sake waiwayosa batayi ba yayinda yashiga Ζ™iran sunanta amma bata amsa masa ba harta shige cikin gida, because tagaji da wannan Ι—an iskan yaudaran nasa, yanzukam bazata iya Ι—auka ba….

Iskan dake cikin bakinsa ya fesar haΙ—e da meda duka hannayensa cikin aljihun wandonsa, cikin sanyin jiki haka yakoma cikin motarsa driver yayimawa motar key suka Ι—auki hanyar fita unguwar batare da sun kula da Dr.Sadeeq dake zaune cikin motarsa ba…

HaΖ™oransa ya sanya ya danne laΙ“Ι“ansa na Ζ™asa komai daya faru akan idanunsa ya wakana sai de baijiyo magan ganun da suka shiga tsakaninsu ba,, wani irin Ι—aci yaji maΖ™oshinsa nayi, iya matuΖ™a Ι“acin rai yashigesa, bakomaine yafi komai Ζ™ona masa ransa ba kamar yanda yaga Zaid yajawo Zahrah jikinsa, hakanan yaji wani irin mugun kishi ya turnuΖ™e masa zuciya,, babban abun dayafi Ι—aga masa hankali shine yanayin daya hango fuskar Zahrah, tabbas yafuskanci wani Ι“oyayyen abu daga gareta,,, key yayi mawa motarsa cikin Ζ™unan rai yayi reverse haΙ—e da barin Ζ™ofar gidan nasu batare da ya aika ayi masa Ζ™iranta ba..

Zahrah na shiga cikin Ι—akinta ta durΖ™usa a Ζ™asa haΙ—e da fashewa da wani irin kuka me tsuma zuciya kaicon zuciyarta da ta so mata namiji irin Zaid, ashe da gaske shiΙ—in mazinaci ne tunda gashi da bakinsa yafaΙ—a, kuka tashiga yi tamkar wacce aka sanarmawa da ranar mutuwarta, yayinda wani abu yataso ya tokare mata Ζ™irji wanda batasan komenene shi ba kamar yanda batasan kukan me takeyi ba…

Driver yana parking motar Zaid yace yafita ya bashi waje, aikuwa babu musu driver’n yafita daga cikin motar….. Kansa ya kafa ajikin kujera haΙ—e da fidda wani irin zazzafan numfashi ta bakinsa, zuwa yanzu kam bazai iya jurewa ba, sam bazai iya jure raΙ—aΙ—i dakuma azaban soyayyar Zahrah dake damunsa ba, tabbas da ace zai iya to da yayi iya ka Ζ™oΖ™arinsa wajen ganin ya yakice soyayyarta acikin zuciyarsa amma hakan bazai yiwuba domin kuwa duk kowani kwanan duniya soyayyarta Ζ™ara ninkuwa takeyi acikin zuciyarsa, zuwa yanzu soyayyar Zahrah babu inda bata ratsa acikin jikinsa ba,,,, a Ζ™alla yakai kusan 30 minute acikin motar yana saΖ™awa da kuncewa, da Ζ™yar ya’iya fitowa daga cikin motar kai tsaye yanufi babban parlour’nsa dake cikin guest house Ι—in nasa, domin kuwa daga gidan su Zahrah guest house Ι—insa suka yiyo….

STORY CONTINUES BELOW

Yana shiga cikin falon ya faΙ—a kan doguwar kujera haΙ—e da lumshe kyawawan idanunsa, kansa ne ke saramasa yayinda juwa ke Ι—ibansa, lallai yazame masa dole yasamawa kansa mafita, yazama dole yafarka daga wannan mafarkin daya keyi tabbas al’amuransa a yanzu suna masa kama da al’amara,, tabbas yana buΖ™atar samun relief daga damuwar dayake ciki, amma sai dai babu amfanin shangiya a yanzu domin kuwa koda yashama bata basa wani relief Ι—in da ya kamata, miΖ™ewa yayi yashiga cikin Ι—akinsa, kai tsaye wani Ι—an drower yanufa haΙ—e da buΙ—ewa, hanu yasanya ya Ι—auko wata wayarsa Ζ™irar techno phantom 9 wanda dama yana ajewane saboda rana irin haka, kasancewar baifito da wayoyinsa ba duk yabarsu a gida,, yana kunna wayar ya laluΙ“o wata lamba haΙ—e da turawa lambar text message, yana ganin alamar saΖ™on ya isa inda yakeson yaje yayi switch off Ι—in wayar haΙ—e da maidata inda ya Ι—aukota kwanciya yayi akan makeken gadonsa wanda yasha shumfuΙ—a ta alfarma, cusa kansa yayi cikin pillow haΙ—e da soma fitar da numfarfashi akai akai….

A hankali taturo Ζ™ofar Ι—akin wanda kafun ma tashigo tuni Ζ™amshinta yarigata shigowa, sanye take da jan wando pencil wanda yayi matuΖ™ar bayyana kyakkyawar surar jikinta yayinda rigarta yakasance baΖ™a me kyau, rigan irin masu faΙ—in wuyan nan ne hakan ne yasanya manya manyan breast Ι—inta bayyana kansu tasaman rigar,, takalmine me uban tsini a Ζ™afarta yayinda ta tufke dogon gashin kanta da jan ribbon kalan wandonta,, kallo Ι—aya zakayi mata kafahimci cewa wayayyar macece Ζ΄ar duma, shigarta kaΙ—ai ya isa yabayyana maka ainihin ko wacece ita, saboda bashigane da mata masu mutumci sukeyi su fita ba kamar yanda ita tayi, domin kuwa ko Ι—an kwali babu akanta, wani irin murmushine kwance akan fuskarta dake nuna alamar cewa tana cikin farinciki,, lumshe idanunta tayi haΙ—e da buΙ—esu alokaci guda, kallon surarsa kaΙ—ai ya isa sanya mata nutsuwa, tajima tana tsumayi da kuma fatan Allah ya sake Ι—aurata akansa, harta cire rai saikuma gashi yau shi da kansa ya gayyatota, lallai zata iya cewa a rana irin ta yau tafi kowa sa’a..

Duk da yaji Ζ™amshin turarenta acikin hancinsa hakan baisanya yaΙ—ago kansa ba,,

Cikin taku irin na matan da suka goge wajen iya Ι—aukar hankalin Ι—a namiji tashiga takowa har zuwa inda yake kwance ya yinda juyawa Ζ™ofa baya…

Hanunta tasanya a bayan wuyansa haΙ—e da soma shafawa a hankali,, cikin wata murya me sanyi dajan hankali tace “Man!”

Shiru yayi bai amsa mata ba, duk da kuwa cewa yanajinta,,, ganin bai amsa taba yasanya tayi murmushi haΙ—e da cire takalman dake Ζ™afarta ta hawo kan gadon,, bakinta ta sanya adai dai saitin tsakiyar bayansa tashiga tsotsa haΙ—e da shafa bayan wuyansa a hankali,,,, wani irin zubawa Zaid yaji tsikar jikinsa tayi, adai dai sanda take Ζ™oΖ™arin nuna masa wani sabon salo…. “Meenal!” yaΖ™ira sunanta da wata irin murya wacce ta riga da ta cushe..

Murmushi Meenal tayi haΙ—e da mirginowa ta dawo gabansa suna fuskantar juna, lumshe idanunta tayi alokacin da tayi arba da kyakkyawar fuskarsa, wallahi tana matuΖ™ar son Zaid komai nasa me kyaune daga ciki har waje, ba abunda yake Ι—aukar hankalinta akan fuskarsa kamar wannan kyakkyawan sajen nasa dayake shan gyara da mayuka masu kyaun gaske..

“Nayi kewarka Man, ashe de kaima kayi kewata? katafi ka barni da tunanin daΙ—in da kajiyar dani, wanda har rana me kamar ta yau babu wani Ι—a namiji da yajiyar dani kwatan kwacin wannan” Meenal taΖ™are maganar cikin yanayi na shagwaΙ“a haΙ—e da sake matsowa tashige cikin jikinsa,, Ι—an guntun murmushi yasakar mata haΙ—e da soma Ζ™arewa fuskarta kallo, Meenal kyakkyawar yarinyace wanda kyawun nata kuma yazama na Ι—an maciji, domin kuwa Meenal tantiriyar Ζ΄ar iska ce kuma cikakkiyar mazinaciya wanda idan ta kafamawa namiji Ζ™ahon zuΖ™a duk nuΖ™u nuΖ™unsa sai ta jefasa cikin raminta, sai dai idan kuma shiΙ—in ya kasance gwaska na gasken gasken, tofa nan ne zasu dai dai ta, kamar dai Zaid da ta buga ta rawa yaΖ™i faΙ—owa raminta, domin kuwa shi Ι—in ma Ι—an iskane me lasisi san nan kuma gwaska ne me zaman kansa, wannan yasa Meenal takasa turasa a cikin raminta..

Hanu Meenal tasanya akan faffaΙ—an Ζ™irjinsa tashiga shafawa haΙ—e da cusa kanta acikin wuyansa cike da Ζ™warewa take manna masa kiss,, tamkar wata mayya haka take sake shigewa cikin jikinsa..

STORY CONTINUES BELOW

Lumshe idanunsa yayi haΙ—e da cusa hanunsa cikin sumar kanta,, take yasoma sauΖ™e ajiyar zuciya akai akai domin kuwa gani yake tamkar Zahrah ce kwance haka a jikinsa,, idanu Meenal ta kafesa dashi cike da mamakin irin sauyawan da yayi, nafarko ta hango tarin damuwa acikin idanunsa yayinda na biyu kuma ta hango wani abu mai Ι—aure kai acikin idanunsa,,, “Man!” taΖ™ira sunansa cikin wata irin murya, idanunsa kawai ya jefa acikin nata idanun batare da yace da’ita komai ba,, dama haka takeso burinta shine yaΙ—aga kyawawan idanunsa ya kalleta,, take ta sauya salon nata kallon ta marairaice idanunta,, fuskarta ta matso daf da tashi fuskar lokaci Ι—aya tasoma Ζ™oΖ™arin haΙ—e bakinsu waje Ι—aya, kamar koda yaushe Ζ™in aminta da hakan yayi da sauri ya kawar da kansa gefe, saboda hakan baya daga cikin tsarinsa haΙ—a miyau da matan bariki, domin babu abu mafi saurin sanya shaΖ™uwa kamar haΙ—akar yawun baki, sosai kiss yake sanya shaΖ™uwa a tsakanin masu yinsa, domin haΙ—uwar yawun bakuna biyu wani sinadari ne na musamman,,,, bata damu ba domin dama tasansa bayawa mace kiss batakuma san dalilinsa na hakan ba, wan nan kuma ita duk ba damuwarta bane matuΖ™ar zai kusanceta to zatafi kowa farinciki,,,,, hanunta ta sanya akan mararsa tashiga shafawa a hankali haΙ—e da Ι—aura bakinta akan nipples Ι—insa, jawota yasakeyi jikinsa bayan ya cire mata Ζ΄ar Ζ™aramar rigar jikinta, kansa ya cusa acikin Ζ™irjinta yana me shaΖ™ar Ζ™amshin turarenta, haΙ—e da sanya hannayensa a bayanta yasoma shafawa a hankali,, take Meenal tasoma sauΖ™e numfashi akai akai dama Ζ™iris take jira saboda akunne take Ζ™warai… Lokaci Ι—aya Meenal tarikice wasu irin salo take gwadawa Zaid masu sanya mutum ya fita a hayyacinsa, yayinda shima yagama ruΙ—ata da nasa salon har saida yakusa sanyata shiΙ—ewa,, amma kuma wani abun mamakin shine yanayin hakan ne cikin wani irin yanayi wanda baisan dame zai Ζ™ira sunan yanayin ba, kwata kwata baijin wani abu mai suna sha’awa a jikinsa duk dakuwa irin romancing Ι—insa da Meenal keyi, lumshe idanunsa yayi haΙ—e da jawota yadawo da ita Ζ™asansa aniyarsa shine ya kusanceta amma kuma sai yaji zuciyarsa tashiga bugawa da sauri sauri yayinda Zahrah tashigo cikin ransa ta tsaya cak, take idanunsa suka haskomasa irin kallon tsanan da tayi masa Ι—azu, nan danan yaji komai yafice masa arai, da sauri ya ture Meenal gefe haΙ—e da sanya hanu ya dafe kansa da yayi masa nauyi, da wani irin kallo Meenal da takai Ζ™ololuwa wajen sha’awa ta bisa, meye haka yakeyi? badai halin nasa na wulaΖ™anci zai gwada mata ba? idan kuwa hakane Zaid yacuceta, saida yagama jefata acikin masifaffiyar sha’awarsa san nan yajuya mata baya, hanu tasanya ta rungumosa ta baya haΙ—e da soma goga masa breast Ι—inta akan bayansa “Meke damunka Man? kada kabari damuwa ya hanaka jin daΙ—in rayuwa please” tafaΙ—i haka cikin narkakkiyar murya, hanunsa yasanya ya zameta daga jikinsa wani irin haushinta ma yake ji, miΖ™ewa yayi direct ya wuce toilet Ι—insa ko waiwayota baiyi ba, baki sake haka Meenal tabisa da kallo harya shige cikin toilet Ι—in,, kuka ta fashe dashi haΙ—e da matse cinyoyinta, tsakani da Allah take kuka domin kuwa iyaka cuta a wajenta shine abun da Zaid yayi mata…

Zaid kuwa yanashiga bathroom ya zame wandon dake jikinsa haΙ—e da nufar inda babban bathtub Ι—in wankansa yake, ruwa ne me kyau da tsabta acikin bathtub Ι—in, amma duk da haka saida ya zubar yakuma taran wani ruwan, turaren wankansa me daΙ—in Ζ™amshi ya sanya a cikin ruwan haΙ—e da shiga cikin ruwan ya kwanta a hankali,, lumshe idanunsa yayi haΙ—i da jingina kansa, zafi yakeji adai dai saitin zuciyarsa, tabbas yanaji ajikinsa cewa akwai abun da zai faru dashi bayan wanda yake faruwa dashi yanzu, “wace irin soyayya ce haka yake yiwa Zahrah me zafi?” tambayar da kullum sai yayimawa kansa kenan, lallai yau yasake tabbatar mawa kansa cewa yazama mutum me rauni, A she dama akwai wata rana da zai iya kasancewa haka? yaΖ™ira Meenal ne don taΙ—ebemasa kewa yakuma samu ya rage tarin sha’awar dake damunsa, domin kuwa har wani ciwo yakeji mararsa nayi masa, amma kuma sai gashi ya kasayin komai da Meenal, ashe ba Meenal Ι—in bace muradinsa Zahrah ce, haΖ™iΖ™a yasake yardarwa kansa cewa abunda kake so shi yake wahalceka sannan kuma yasake tabbatar mawa kansa cewa ƘAUNA guda Ι—ayane tal aduniya, SO ne kawai yake da yawa, amma Ζ™auna Ζ™aunace,, kafun yaΖ™ira Meenal yayi tunanin cewa idan tazo zata gusar masa da damuwarsa, sai kuma bayan tazo yaga ashe bazata iya ba, ashe yin sex da shan giya basune maganin damuwarsa ba, Zahrah har lau itace maganin damuwar sa,, anya kuwa zai warke daga damuwar nan tasa?

STORY CONTINUES BELOW

Yajima acikin bathroom kafun yayi wanka yafito jikinsa sanye da farar rigar wanka,, kallonsa ya maida kan gado inda yabar Meenal don ganin wani hali ta ke ciki domin kuwa sarai yaji kukanta lokacin dayake cikin bathroom,, dariyane taso Ζ™wacemai sakamakon ganin Meenal da yayi takure a can Ζ™arshen gado tana bacci, yayinda ta cusa hanunta na hagu a Ζ™asanta, sarai yasan Meenal jarabebbiya ce yanzu haka fingering tayi don samawa kanta relief, abun da yafi tsana kenan wato mutum yayi amfani da kansa don biyan buΖ™atarsa, amma kuma wannan halin Meenal ne,, kai kawai ya girgiza haΙ—e da nufan gaban dressing mirror Ι—insa, vaseline yashafa ajikinsa kasancewar garin ana Ι—an yanayi na sanyi, saida ya feshe jikinsa da body spray kafun yasanya kayansa riga da wando na jeans masu kauri, sosai kayan sukai masa kyau, kuΙ—aΙ—e yaciro a cikin drower Ι—insa ya ajiye a kusa da Meenal daketa sharan bacci, kana yayi ficewarsa daga Ι—akin, direct bai zarce ko inaba sai compound Ι—in gidan, yanzu kam shida kansa yakeson yayi tuΖ™i, don hakane ma yazaΙ“i BMW blue colour amatsayin wacce zai fita da ita….

Dr.Sadeeq

Duk yanda Dr.Sadeeq yaso samawa kansa nutsuwa hakan yagagara domin kuwa sam zuciyarsa bata amince da zuwa wajen Zahrah da Zaid keyi ba, duk da yau yafara ganinsa aΖ™ofar gidan su Zahrah’n amma jikinsa ya basa cewa ba yaune zuwansa na farko ba, amma bakomai zaiyi maganin abunne zai nisanta Zahrah da Zaid nisantawa me tsanani kuwa, da wannan tunanin bacci ya Ι—aukesa…

Washe Gari.

Dasassafe Zahrah ta shirya tayi tafiyarta makaranta sai dai a ranta tana mamakin rashin Ζ™iranta da Dr.Sadeeq yayi, rabonta dashi tunjiya da yamma sunkuma rabu dashi akan cewa zai Ζ™irata sai gashi kuma har zuwa yanzu bai Ζ™irata ba, uzuri tayi masa akan cewa ko aikine yayi masa yawa domin tasan hakanan Dr.Sadeeq bazaiΖ™i Ζ™iranta ba…

Tana tafiya ba jimawa motar Dr.Sadeeq ta tsaya a Ζ™ofar gidan nasu, fitowa yayi daga cikin motar yasha adonsa cikin blue Ι—in shadda sosai kuma yayi kyau,, yaro ya aika cikin gidan yace yace ana sallama,, bajimawa yaron daya aika yadawo ya shaida masa ance me gidan yana fitowa…. Washe da baki Baffa yaΖ™araso wajen Dr.Sadeeq dake tsaye ” Maraba da Likita, dama kaine ai da kashigo ciki amma ka tsaya a waje sai kace wani baΖ™o”

Murmushi Dr.Sadeeq yayi cike da girmamawa ya sunne kansa Ζ™asa haΙ—e da durΖ™usawa ya gaishe da Baffa,, fuska cike da fari’a Baffa ya amsa gaisuwan,,,

“Aikuwa kayi rashin sa’a domin kuwa mutumiyar taka bata jima da fita a gidan ba, tatafi makaranta ko karyawa bata tsaya tayi ba, amma ina ga zaifi kyau mushiga daga ciki ko”

“A’a Baffa nan Ι—in ma yayi, dama wajenka nazo ae”

“To to masha Allah, saimu zauna ae ko abisa dakalin nan” Baffa yaΖ™are maganar yana meyi mawa Dr.Sadeeq nuni da dakalin Ζ™ofar gidan.

Duk yanda Baffa yaso Dr.Sadeeq ya hau kan dakalin su zauna Ζ™iyawa yayi, domin kuwa Baffa surikinsa ne baidace ace sun zauna gaf da juna ba kodan saboda kara da matuntawa,,

“Shikenan to tunda dae kaΖ™i zama, inajinka Allah yasa dai lafiya?”

Kansa yaΙ—an sosa haΙ—e da sakin murmushi “Lafiya Ζ™alau Baffa dama akan maganan aure nane da Zahrah…” sai kuma yayi shiru ya kasa Ζ™arasa maganar dake cikin bakinsa, gani yake tamkar idan yafaΙ—i maganar kai tsaye Baffa zaice masa yayi gaggawa ko kuma yace yayi rashin kunya…

“Ka kwantar da hankalinka Likita kafaΙ—i duk wani abu dake ranka” Baffa yafaΙ—i haka ga doctor Ι—in..

“Am dama…dama inaso ne kabani izini nasake turo magabatana dan sukawo sadaki san nan kuma a tsaida ranar aure”

“Alhmdlh to ai wannan abun farinciki ne Likita, wannan ae bawani abun damuwa bane, nabaka dama ka turosu aduk sanda kakeso, sai de kuma zakaΙ—anyi haΖ™uri, saboda zansa lokacin da Ι—an tsayi saboda kasan ba a yin aure kai tsaye haka dole sai anΙ—anyi mawa yarinya sayayya, ina fata hakan bazai sosa ranka ba?”

Murmushin jin daΙ—i Dr.Sadeeq yayi haΙ—e da cewa “Naji daΙ—i sosai Baffa, amma kuma maganar sayayya basai kun wahalar da kanku ba, domin zuwa yanzu gidan da zamu zauna baya buΖ™atan komai, saboda haka don Allah kada kusa kanku a wahala”

Murmushi Baffa yayi haΙ—e da cewa “Ƙwarai mungode da wannan Ζ™oΖ™arin naka, amma sai de nace kayi haΖ™uri, duk da cewa mahaifin Zahrah baya raye ni Ζ™aninsa ina raye kuma niΙ—in ma ubane a wajenta, zan yi amfani da Ι—an abun da nake dasu wajen ganin namata kayan Ι—aki iya dede Ζ™arfina, kamarde yanda kowani uba keyiwa Ζ΄arsa, wannan shine kaΙ—ai gatan da zamu iyayi mata a yanzu” Baffa yafaΙ—i haka da iyaka gaskiyarsa..

Ajiyar Zuciya Dr.Sadeeq ya sauΖ™e, haΖ™iΖ™a shi Zahrah kawai yakeso bawai wani abu na daban ba, kuma shi baiso akawota da komai, domin musamman ya ware mata Ι“angarenta, kuma tuni yabawa wani abokinsa me saida furnitures a Dubai order akan akawomasa setin kujeru dakuma gado harma da duk wani abu wanda yasan zai Ζ™awata Ι—aki,, amma tunda yaga Baffa yadage akan cewa shima zaiyi iya nasa Ζ™oΖ™arin shikenan zai ware wani Ι—aki na da ban idan yaso sai a sanya kayan da Baffan yayi mata acan,,, cike da mutuntawa Baffa da Dr.Sadeeq sukayi sallama….

Baffa na shiga gida ya kalli Inna dake zaune,, “Salame inajin fa tafiyana yola yagabato idan banje jibi ba to zanje gata insha Allah”

Fuska Ι—auke da mamaki Inna ke kallonsa, “Yola kuma Malam?”

“Ƙwarai kuwa, kinga fitana Ι—in nan to yaron nan ne Sadeeq yazo min da maganar cewa inbasa dama yaturo magabatansa don sukawo sadaki akuma sa rana, to ni dai nace yaturosu duk sanda yakeso, yanzu dole zanje yola insanya fili dakuma gonan nan namu na gado a kasuwa idan aka siya intarkata kuΙ—in nan nasamu nasaiwa yarinyarnan kayan Ι—aki dakuma kayan aikace aikace kamar de yanda kowani iyaye kemawa Ζ΄arsu dan baiyiwuwa ace mu miΖ™ata haka”

Ajiyar zuciya Inna tasauΖ™e haΙ—e da gyara zama ” Duk naji batunka Malam, amma kuma mezai hana kabar shi mijin nata yayi mata komai, ae naga yana da halin da zai iyayi mata fiye da wannan ma”

Murmushi kawai Baffa yayi shi kam tun ba yau ba yasan cewa bakoda yaushe ne Inna take gane karatun da’ake biya mata ba, don haka baiΖ™ara cewa da’ita komai ba yawuce Ι—akinsa, domin yasan kozai shekara a wajen yanason ganar da’ita tofa bazata fahimcesa ba,,, Inna kuwa baΖ™in ciki ne yakamata ina ma laifin yace zaiΖ™ara jari da kuΙ—in, sai yace wani wai zai siyawa Zahrah kayan Ι—aki,, haka taita Ζ™ananun maganganunta babu maijinta ma balle yatanka mata……

Da yamma Dr.Sadeeq yaΖ™ira Baffa yasanar masa cewa Baffansa zaizo da dare donsu tsaida magana, duk da cewa Baffa yayi mamakin sauri irin na Dr.Sadeeq Ι—in amma saiya share yace Allah yakawosu lafiya,,

Hargida Baffa yaje yasanarwa Alhaji Umar abun da Dr.Sadeeq yace, kuma dama Alhaji Umar Ι—in tuni yasan da maganar saboda duk abun da yafaru Baffa yanazuwa ya sanarmasa har kawo lefen da akayi ma Baffa yasanar masa,, sosai Alhaji Umar yayi murna yakumace zaizo gidan Baffa’n da dare a Ζ™arΙ“i baΖ™in dashi……

Kamar yanda Dr.Sadeeq yafaΙ—a hakane yakasance domin ana idar da sallan Isha Baffa Amadu da wani shaΖ™iΖ™in amininsa suka zo gidansu Zahrah,, sosai Baffa da Alhaji Umar suka musu tarba na mutunci,, zama sukayi haΙ—e dayin magana ta fahimtar juna, nan Baffa Amadu ya miΖ™a sadakin Zahrah ga Baffa naira dubu Ι—ari (100,000) bawani Ι“ata lokaci Baffa yasanya lokacin aure wata Ι—aya, aikuwa take kowannensu yacika da farinciki haka sukayi sallama cike da girmama juna……

.Idan kin gama rubuce rubucen banzan naki kije Baffan ki nanemanki!” Inna tafaΙ—i haka aΖ™ufule, ko jiran amsan da Zahrah zata bata batayi ba tayi ficewarta acikin Ι—akin,,, da kallon mamaki Zahrah tabi bayan Inna wai meke faruwane tun dawowarta amakaranta tafuskanci cewa ran Inna a matuΖ™ar Ι“ace yake da’ita, domin kuwa ko abincin rana Inna batayi mata tayi ba, kamar yanda ta sabayi mata kullum, to koma dai menene Allah yasa bawani abu bane me zafi… Tattara books Ι—in dake gabanta tayi haΙ—e da miΖ™ewa ta sanya hijab a jikinta kana tafice daga cikin Ι—akin…..+

Da sallama Ι—auke a bakinta takutsa kanta cikin Ι—akin Baffan nata,, zama tayi akan tabarman dake shimfuΙ—e a tsakiyan Ι—aki, haΙ—e dayi mawa Baffa barka da gida,, fuska Ι—auke da fari’a Baffa ya amsa mata..

Gyara zama Baffa yayi haΙ—e da cewa “Bakomai yasa nayi Ζ™irankiba sai dan na sanar dake abun dayake faruwa sannan kuma na danΖ™amiki haΖ™Ζ™in ki a hanunki, yau da safe yaron nan likita yazo yasameni akan cewa zaituro magabatansa don sukawo sadakin ki, nakuma bashi dama, to yanzu dai sun riga da sun danΖ™amin sadakin ki a hanuna saboda haka ga abunki naira dubu Ι—ari ne cus nakine halak malak” Baffa yaΖ™are maganar yana me miΖ™a ma Zahrah maΖ™udan kuΙ—in dake hanunsa….

Gaba Ι—aya jitayi jikinta yayi sanyi laΖ™was gaba Ι—aya duk wani kuzarinta ya gudu, hakanan taji wani iri a cikin zuciyarta.

“Ki karΙ“a mana Zahrah” Baffa yafaΙ—i haka ganin da yayi ko Ι—ago kanta takasa yi.

Girgiza kanta ta shigayi a hankali cikin muryarta me sanyi tace “Duk abun da ka yanke a gareni Baffa dai dai ne, amma maganar sadaki ka riΖ™e a wajenka, saboda ko kabani babu abun da zanyi dasu!” taΖ™are maganar cikin ladabi.

“A’a Zahrah ki karΙ“i abunki haΖ™Ζ™in kine, saboda haka nima babu abunda zanyi dashi ki karΙ“i abunki saiki adana a wajenki, idan kuma wani abu zaki saya saiki saya, amma kada kiyi almubazzaranci dasu, zaifi kyau kisaya abu me mahimmanci wanda zai amfaneki yanzu ko gaba” maganar da tafito daga bakin Baffa kenan.

Shiru Zahrah tayi ita tama rasa yanda zatayi gaba Ι—aya yanayinta yasauya, cikin sanyin jiki Zahrah tasanya hanu ta karΙ“i sadakin nata a hanun Baffa bawai dan ranta yasoba sai dan Baffa ya matsa akan cewa saita karΙ“a..

“Yauwa kinga idan kika riΖ™e abunki a hanunki ae yafi ko, sai kuma maganar sa rana, nasa nanda wata Ι—aya, ai inaganin hakan yayi domin kafun lokacin insha Allah mungama iya Ζ™oΖ™arin da zamuyi wajen sayan Ζ΄an kayayyakin Ι—aki”

Wannan magana ta sa rana yafi komai rugaza mata zuciya, fiye da maganan sadaki, haka nan taji faΙ—uwar gaban da takeji ya tsananta,, amma haka tayi mawa Baffa sallama cikin sanyin jiki tanufi Ι—akinta…

Zama tayi akan katifarta haΙ—e da rumtse idanunta, take hawaye suka shiga fitowa daga cikin idanunta suna gudu akan fuskarta,, shikenan yanzu saura mata wata Ι—aya tazamo matar aure? tambayar da tayiwa kanta kenan, bazata iya faΙ—an wani irin yanayi ta tsinci kanta aciki ba, fargaba ne ko kuma tsoro ne shine abun da bata sani ba,, idanunta ta buΙ—e haΙ—e da maida kallonta ga kuΙ—aΙ—en dake riΖ™e a hanunta,, tsurawa kuΙ—in idanu tayi tamkar mai son gano wani abu ajikin kuΙ—in,, hawayene suka kuma Ι“alle mata, batasan dawani idanu zata kalli Dr.Sadeeq ba, shi wani irin mutum ne? yasani Ζ™warai cewa ita ba cikakkiyar budurwa bace da ita da bazawara duk Ι—aya suke, amma kuma shine ya cire maΖ™udan kuΙ—aΙ—ensa yabada amatsayin sadakinta alhali kuma farashinta baikai haka ba, ita ba irin matan nan bane dasuka dace a sayesu da tsada har haka ba, domin kuwa acikin abubuwa goma da zasu Ζ™ara farashinta babu kaso tara, saboda haka bata cancanci wannan sadaki ba,, hanu tasanya ta share hawayenta, haΖ™iΖ™a bazatace batason Dr.Sadeeq ba amma kuma batajin son nasa acikin jini da jikinta, amma hakan bawai wani abu ne da zaisanya taΖ™i aurensa ba, domin shi ne ma mutum na farko aduniya daya cancanci ta aura, kodan halaccin daya gwada mata a rayuwa…. Cikin wata jakarta tasanya kuΙ—in sadakin nata, haΙ—e da dawowa ta kwanta akan katifarta, bazama ta iya Ζ™arisa assigment Ι—in nata ba domin kuwa gaba Ι—aya yanayinta yasauya damuwa ta bayyana a tattare da’ita,, da Ζ™yar ta iya jawo wayarta taΖ™ira Husnah ta sanar mata da duk wani abun daya faru,, daΙ—ine ya kama Husnah sosai take ta hau farinciki haΙ—e da cewa gobe zatazo yakamata su fara shirye shiryen biki tunda wuri, domin wata Ι—aya bawani lokaci ne me tsawo ba idan har darai da kuma lafiya…

STORY CONTINUES BELOW

*****

“Kiyi kuka da kyau Saleema amma kuma kozaki mutu bazaki auri Sadeeq ba matuΖ™ar bai fasa auren da zaiyi da waccar Ζ΄ar Ζ™asΖ™antattun mutanen ba, ni bazan iya haΙ—a iri da jinsin matsiyata ba!” Abunda Hajiya Habiba take faΙ—a kenan cikin Ι“acin rai.

Ɗago kai Saleema tayi takalli mahaifiyarta ta fuska caΙ“a caΙ“a da hawaye, cikin muryar kuka Saleema tasoma cewa ” Wlhy inasonsa Mom kuma bazan taΙ“a iya auren wani bayan shiba, nidai na amince zan aureshi a haka, idan yaso bayan auren sai nasan yanda zanyi naΖ™ori ita yarinyar”

Kallon ke shashasha ce Hajiya Habiba tashiga yi mawa Saleema, cike da baΖ™in ciki taja tsuka haΙ—e da watsawa Saleema’n harara “Nibansan yaushe zuciyarki ta mutuba wlhy Saleema, ashe ke baki da hankali? to nifa kisani nagama maganata aure da Sadeeq ne anfasa, kuma suzo su kwashe lefensu bama buΖ™ata, domin kuwa kamarni Hajiya Habiba bazan lamunci cinfuskaba, saboda abunda suke shirin yi yanzu cin fuskane a gareni” fuuuu haka tayi wucewarta sama, tabar Saleema tana ta ruskar kuka, saikace wanda akace ubanta ya mutu….

****

Baffa na zaune a wajen sana’arsa wasu maka makan motoci guda biyu suka faka adaf dashi.. Sosai yayi mamakin ganin Alhaji Ma’aruf yakuma dawowa garesa a karo na biyu, wanda ko kusa baiyi tunanin haka ba..

Bayan sun gaisane Alhaji Ma’aruf ya nisa haΙ—e da cewa “Nasan zakayi mamakin dawowata gareka Malam Hayatu, sai de kuma me nema baikamata ya gajiya ba”

Ajiyar zuciya Baffa yasauΖ™e haΙ—e da tattaro duka nutsuwarsa yadubi Alhaji Ma’aruf…

“Bazan taΙ“a Ι“oyemaka ba Alhaji, kamardai yanda nafaΙ—a maka afarko yanzu ma hakane, domin maganan da nakeyi maka yanzu ma jiya aka kawo sadakin yarinyar, saboda haka sedai nace kawai kuyi haΖ™uri”

Kai Alhaji Ma’aruf yashiga jinjinawa, zuwa yanzu dolensa zaibawa Zaid haΖ™uri akan cewa yayi haΖ™uri yacire yarinyar aransa, domin kuwa idan ba wani ikon Allah ba to babu alamun cewa Zaid zaisamu auren yarinyarnan Zahrah..

Haka Baffa da Alhaji Ma’aruf suka rabu, bayan Alhajin yayi mawa Baffa alkhairi maiyawa, amma sam wannan karon Baffa yaΖ™i karΙ“a yace bai buΖ™ata, duk yanda Alhaji Ma’aruf yaso Baffa ya amshi kuΙ—in hakan bai samu ba,, haka Alhaji Ma’aruf yayimawa Baffa sallama shida tawagar body guard Ι—insa suka bar wajen, sam Alhaji Ma’aruf baiji daΙ—in hakan ba, yaso ace Ι—ansa yasamu abunda yakeso…..

Cike da tsananin damuwa Alhaji Ma’aruf ke kallon Zaid dake zaune a Ζ™asa yayi shiru, gaba Ι—aya ya sanja, komai nasa yazama sanyi sanyi, ga alamomin damuwa da suka bayyana kansu a jikinsa, baisan wani irin masifaffen soyayya Ι—annasa ya kamu dashi ba, baimasan taya ya Zaid zai Ι—auki maganar da zai faΙ—a masa ba, amma dai yazama dole yafaΙ—a masa gaskiya amatsayinsa na mahaifinsa.

“Zaid!”

Alhaji Ma’aruf yaΖ™ira sunan Zaid murya a tausashe.

“Na’am Dad” Zaid ya amsa murya Ζ™asa Ζ™asa.

“Inaso kabani hankali da nutsuwarka, dan Allah Zaid ka kwantar da hankalinka, nasani kuma kaima kasani nema cikin nema haramunne, kacire wannan yarinya acikin zuciyarka domin kuwa yau naje nasamu shi Baffan nata, yakuma shaidamin cewa a halin yanzu har ya karΙ“i sadakinta, saboda haka zaifi kyau kacireta a zuciyarka, kanemi wata nasan babu wata mace da zata Ζ™ika”

Tamkar wanda Dad Ι—in ya watsa masa ruwan zafi haka yaji sauΖ™ar maganganun mahaifinsa acikin kunnuwansa, da sauri yaΙ—ago jajayen idanunsa ya watsawa mahaifin nasa su,, bakinsa na rawa yace “AnkarΙ“i sadakinta kuma Dad?”

“Ζ™warai kuwa Zaid abunda Baffan nata yafaΙ—amin kenan, shiyasa nace ka cireta a ranka”

Kai Zaid yashiga girgizawa,,,,, “Bazai taΙ“a yiwuwaba Dad, wlhy wani bazai taΙ“a auran Zahrah ba matuΖ™ar ina numfashi acikin duniyar nan, inasonta fa Dad meyasa bazaku gane hakan ba? bazan iya cigaba da rayuwaba idan har babu Zahrah a gareni, nasan laifinane Dad, amma duk da haka bai dace a hanani Zahrah ba, saboda inasonta inamata wani irin so me tsanani please Dad niko yanzu dan Allah a Ι—aura mana aure idan yaso daga baya ni na amince zan shawo kanta, nasanma tana sona har yanzu, kuma nasan daga baya zata yafemin abunda nayi mata!”

Cike da tsananin mamaki Dad ke kallon Zaid wanda gaba Ι—aya ya ruΙ—e alokaci Ι—aya, anya kuwa ba aljanune suka shiga jikinsa ba ? Dad yatambayi kansa cike da tsananin mamaki, domin kuwa sam Zaid ba haka yake ba, shi mutum ne me nuΖ™u nuΖ™u amma kuma wani babban abun mamaki shine yauga Zaid nan yana faΙ—in wai bazai iya rayuwa ba idan babu wata,,

“Zaid!” Dad yakuma Ζ™iran sunansa cike da tausayawa domin shikam baitaΙ“a ganin soyayya irin wannan ba…

Zaid bai iya amsawa mahaifinnasa ba, saide idanunsa daya Ι—ago ya kalli Dad Ι—innasa dasu.

“Zaid ka kwantar da hankalinka, ba ita kaΙ—ai bace mace a duniyar nan akwai mata da yawa, kana da Ζ΄ancin da zaka zaΙ“i duk irin macen da kake so” Dad yafaΙ—i haka ga Zaid cikin lallami…

“Idan ni inada Ζ΄anci ita kuma dana cuta fa? nacutar da ita Dad cuta mafi muni, na zalunceta, banda wata hanya dazanbi na goge laifina a wajenta, sai ta hanayar aurenta, dan Allah Dad kayi wani abu, bazan iya jure rashin Zahrah ba!” yanzu kam har Ζ™walla suncika idanun Zaid batare daya sani ba. (hmm so mugun wasa)

MiΖ™ewa Zaid yayi daga zaunen da yake haΙ—e da sa kai yafice daga cikin falon Dad Ι—in nasa, da kallo kawai Dad yabisa dashi harya fice, baisan me yake shirin faruwa da Ι—an nasa ba amma ae so ba hauka bane…..1

Zaid yana fita daga Ι“angaren Mahaifinsa direct part Ι—insa yanufa, idanunsa gaba Ι—aya sun rufe yayinda kansa ke matuΖ™ar sara masa, sam bazai iyaba, bazaitaΙ“a iya jure rashin Zahrah ba, lallai yazama dole yakuma yarda da shawaran da zuciyarsa ta basa,, tabbas yazama dole ya kusanto Zahrah zuwa garesa koda kuwa hakan zai jawo faruwar abubuwa masu tarin yawa…key Ι—in motarsa ya Ι—auka yafice daga cikin Ι—akin, gaba Ι—aya zuciyarsa ta bushe babu wani abun dayayi saura aciki banda tsananin soyayyar Zahrah…..

Da wani irin mahaukacin gudu Zaid yafigi motarsa yafice daga cikin gidan saura kaΙ—an yabitakan me gadi daya wangale masa gate, Allah ne ya ta Ζ™aita Me gadin yayi saurin matsawa gefe, domin kuwa ko gama buΙ—e gate Ι—in baiyi ba Zaid yayi yo kansa….

TuΖ™i yakeyi amma kuma kwalbar giya ne riΖ™e a Ι—ayan hanunsa yana sha, jinkansa yake gaba Ι—aya yana juyawa, yayinda zuciyarsa keyi masa zafi, idanuwansa Zahrah kawai suke hango masa, batare da Zaid yakulaba motarsa tayi karo da wata babbar mota, take motar tasa ta Ι—agu sama haΙ—e da faΙ—owa Ζ™asa sannan kuma tashiga gungurawa kan titi, batare da Zaid dake cikin motar ya tsira ba…..

Post a Comment for "SHU'UMIN NAMIJI CHAPTER 8 BY FATYMA SARDAUNA"