Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

SHU'UMIN NAMIJI CHAPTER 7 BY FATYMA SARDAUNA

 SHU’UMIN NAMIJI CHAPTER 8 BY FATYMA SARDAUNA

                     Www.bankinhausanovels.com.ng 

Idanu ta Ζ™ara zarowa domin tabbatar mawa kanta cewa abun da tagani gaskiya ne, ko kuwa, gizo idanunta keyi mata.

Tabbas dagaske ne bawai gizo bane, hoton zanen fuskarta ne raΙ—au ajikin takardan. Hanunta na rawa haka ta durΖ™usa Ζ™asa, haΙ—e da sanya hanu ta sake ware takardan, tabbas itaΙ—ince babu ko kokonto, zanen fuskarta ce kwance ajikin takardan, amma saboda tsananin kyawun da zanen yayi tamkar azahiri haka zaka gani, hanu tasanya ta shafi zanen, cike da fargaba haΙ—e da Ι—aurewar kai.

Lallai yazama dole a gareta tanemo wanda yake aikata mata waΖ΄an nan abubuwan, kusan kwana uku yanzu kenan ana turo mata da saΖ™onni, bata kuma san daga waye bane.

Bata damu da ta duba sauran kayan dake cikin kwalin ba, ta tattara shi ta Ι“oye acikin kayanta.

Zama tayi dirshan akan katifa tana mai da numfashi akai akai, sosai abun yabata mamaki, tabbas ko ma waye ne wanda yake bibiyarta ta tabbata yayi mata farin sani, amma kuma rainin hankalin yayi yawa, dole zataimawa tufkar hanci. Abun da ta Ζ™udurta kenan acikin zuciyarta domin iskancin yasoma isarta.

Ƙarfe 6:30 na yammaci Dr Sadeeq yayi wa gidansu Zahrah tsinke, bayan yasha adon sa cikin riga da wando na shadda Ζ΄ar bugu mai kyau. Zama yayi acikin motarsa yana mai jiran fitowar Zahrah, domin kuwa yamata waya yasanar da’ita cewa gashi nan, a Ζ™ofar gidansu.

Kafeta da idanu yayi domin kuwa bakaΙ—an ba tayi masa kyau, cikin shigar doguwar rigan dake jikinta, lallai Zahrah Ζ™arshe ce wajen haΙ—uwa dakuma kyau.

Fuskarta Ι—auke da murmushi Zahrah ta Ζ™araso wajen da motar tasa take fake. Tsayawa tayi ajikin motar, batare da ta buΙ—e tashiga ba. Ganin haka yasa Dr Sadeeq buΙ—e murfin motar yafito.

“Yau kuma aji ake jamin ne?” ya tambayeta cikin yanayin tsokana.

Ɗan guntun murmushi tayi haΙ—e da juya idanunta. “Eh mana, ko bankai naja aji bane?” itama ta tambayesa cikin yanayi na shauΖ™i.

“Murmushi yayi haΙ—e da Ι—age giransa sama “Kin isa har kinma wuce, ko bakisan cewa keΙ—in tamusamman bace?”

Hararan wasa Zahrah ta wurgamai haΙ—e da kawar da kanta gefe, batare da tace dashi komai ba. Haka take al’adar ta ne, bakoda wani lokaci take bada amsar tambaya ba, domin a cewarta shiru ma magana ne.

“Kona zagayo na buΙ—e miki murfin motar ne gimbiyata, saboda naga kamar bazaki iya ba ?” yafaΙ—i hakan cike da kulawa.

“A’a ba buΖ™atar hakan, ni dakaina ma zan iya” taΖ™are maganar tana mai buΙ—e murfin motar, haΙ—e da shiga tayi mawa kanta mazauni.

Shima komawa yayi cikin motar ya zauna. Bayan ya Ι—aura duka idanunsa a kanta.

“Kinyi kyau sosai, fiye da ko yaushe” yafaΙ—i haka yanamai kashe idanunsa.

Ɗanguntun murmushi Zahrah tayi “Nagode” tace dashi ataΖ™aice

Jinjina kansa yayi azuciyarsa kuwa cewa yayi “Lallai Zahrah tana da aji, duk da ta rasa Virginity Ι—inta hakan baisanya ta zama wata sakaka da’ita ba, yanason mace wacce ta’iya takunta, wacce bata sakar baki tayita dariya like mental problem, wasu matan da zaran kace dasu sunyi kyau tofa take zasu wage baki suita Ζ™yaΖ™yata dariya, babu wani Ι—an jan aji ba komai. nima shaida ce irin su Sister Munubiya idan kace dasu sunyi kyau ae har kyautan kuΙ—i zasu baka tsabar daΙ—i?”

STORY CONTINUES BELOW

Sake gyara zamansa yayi haΙ—e da dawo da nutsuwarsa zuwa gareta.

“Zaki’iya zama dani a ko wani irin hali Zahrah?”

Ya jefomata tambayar da bata tsammaci jinsa ba.

Cikin yanayin mamaki Zahrah ta dawo da kallonta garesa, haΙ—e da cewa “Banfahimci maikake nufi ba”

“Inanufin zaki iya rayuwa dani ako wani irin hali na tsinci kaina? sannan zaki iya yarda na haΙ—aku ku biyu na aura?” yakuma maimaita tambayar tasa.

Dummm haka Zahrah taji Ζ™irjinta ya buga, idan da badon kada yace ta rainasa ba, to tabbas da zatace dashi yasake maimaita maganar da yayi. Domin idan kunnuwanta sunjiye mata dai dai, to kuwa bata da amsar da zata basa, domin koda ta basa amsa zata iya faΙ—uwa, saboda balallai ta bashi amsa dai dai da abun da ya tambaya ba.

Idanunsa duka ya tsura mata, amsa kawai yakeson ji daga bakinta.

Kasa ce dashi komai tayi, domin kuwa haryanzu bata gama haΙ—a amsar da zata basa ba.

“Nasani dama ba lallaine ki amince ba, Hajiya na ta amince da aurena dake, amma kuma kamar yanda nafaΙ—amiki a baya, tun tuni akwai zaΙ“in da tayimin, takuma umarceni da na aureku duka biyu, shin zaki iya aurena a haka, zaki iya zama da wata a matsayin kishiyar ki?” yafaΙ—i hakan cike da zaΖ™uwan son jin amsa daga gareta.

Jikinta ne gaba Ι—aya yayi sanyi, take taji zuciyarta ta karaya, batasan ya’ake zama da kishiya ba, haryanzu ita yarinyace, bakomai tasani na game da al’amarin duniya ba, tanaji a labarai irin illan da kishiyoyi suke mawa junansu saboda kishi, amma ita yanzu ba wannan bane a gabanta, makomarta na gaba take tunawa, shinya zata kasance?” ta tambayi zuciyarta…

“Kinyi shiru kice wani abu mana zahrah ko zuciyata zata daina bugawan da takeyi” Dr yafaΙ—i hakan cikin yanayin damuwa.

“Bazan taΙ“a Ζ™in aurenka ba, sai dai idan har kaine kace kafasa aurena, sai dai kuma inajin tsoro, bansan mene zai kasance dani gaba ba, dan Allah kada soyayyar matarka ta ruΙ—eka, ka wulaΖ™antani, banda wani madogari sai ALLAH sai kuma kai” taΖ™are maganar cikin rawar murya, yayinda idanunta sukayi rau rau dasu, alamar zasu zubda Ζ™walla.1

Ajiyar zuciya mai Ζ™arfi ya sauΖ™e, haΙ—e da sakin Ι—an taΖ™aitaccen murmushi. “Har abada kada kitaΙ“a tunanin zan wulaΖ™antaki Zahrah, inasonki da gaske bada wasa ba, namiki alΖ™wari zan kamanta adalci a tsakaninku, bazan juya miki bayaba insha Allah!” Doctor Sadeeq ya faΙ—i haka cike da lallashi.

Tuni idanun Zahrah suncika da Ζ™walla, amma idan ta tuno cewa bata da zaΙ“i sai taji gwamma kawai ta daure zuciyarta, haka ta ta Ζ™addaran take.

“Kada kiyi kuka kinji My Princess, ina tare dake ako wani lokaci, zankuma share miki dukkanin hawayenki nan bada jimawa ba namiki alΖ™awari”

Saurin maida hawayenta tayi haΙ—e da Ζ™aΖ™alo murmushin dole ta’aza akan fuskarta, wan nan damuwarta ne ita kaΙ—ai, baikamata ace tabari Dr Sadeeq yagane ba, lallai tun yanzu yakamata ta zama mai juriya.

“Baffa yana gida kuwa?” Dr. Sadeeq ya tambaya.

Wasa da yatsun hanunta tashiga yi, haΙ—e da kaΙ—a masa kai alamar “Eh”

Kai yajinjina haΙ—i da cewa “Yanaga duk jikinki yayi sanyi? banace kada kisa damuwa a ranki ba” cikin kulawa yayi maganar.

Cike da shagwaΙ“a Zahrah ta langwaΙ“ar da kanta gefe haΙ—e da turo Ι—an Ζ™aramin bakinta gaba, “Nibansa damuwa a raina ba” tace haka cikin sanyayewar jiki.

Wani irin kallo maiΙ—auke da ma’anoni masu yawa Dr.Sadeeq yashiga yi mata, ji yake tamkar yajawota jikinsa ya rungumeta tsam acikin Ζ™irjinsa, saboda ako da yaushe idan yana tare da’ita wani irin feeling yakeji a jikinsa.

STORY CONTINUES BELOW

“Kije kimin sallama da Baffa inaso zamuyi magana”

“To” kawai tace dashi haΙ—i da buΙ—e murfin motar tafita. Dakallo kawai ya bita harta shige gida.

Tana shiga cikin gida ta iske Baffa yana Ζ™oΖ™arin fitowa daga Ι—akinsa.

“Zahrah har kindawo? badai likitan yatafi ba?” Baffa yajeromata tambayoyi alokaci Ι—aya.

“A’a baitafi ba Baffa, shine ma yace nace ma yana son magana dakai” Zahrah tafaΙ—i haka ga Baffa cikin girmamawa.

“To Allah yasa lafiya, yanzu kuwa zanje na sa mesa” ya faΙ—i maganar yana mai nufar hanyar fita daga gidan.

Zahrah kuwa Ι—akinta takoma.

Sosai maganar Dr.Sadeeq yataΙ“a mata zuciya, bakomai take hangomawa kanta ba, sai yanda makomarta zai kasance acikin gidansa, tabbas ta tabbatar wacce zai aura, ba irin ta bane, tasan tana da galihu, saΙ“anin ita da take ko oho, sannan kuma dole zata ga banbanci daga Ζ΄an uwansa, haka ma Dr.Sadeeq Ι—in dole zai banbantasu, saboda waccar zai sameta a budurwa, saΙ“anin ita da zai sameta ba’a budurwa ba, kukane yaΖ™wace mata mai sauti, cusa kanta cikin cinyoyinta tayi tashiga rera kukanta, har abada cutar da Zaid yayi mata bazai taΙ“a gushewa ba…..

“Alhmdlh masha Allah! haΖ™iΖ™a naji daΙ—in wannan magana taka Likita, lallai kacika mutumin kirki kuma mutumin Ζ™warai, Allah yasaka ma da gidan Aljanna, kuma idan dai Zahrah ce kada kaji komai natabbatar itama tana Ζ™aunarka, saboda haka nabaka izini ka turo magabatanka, don mu tsaida magana,kuma maganar bayarwa nabaka Zahrah!” Baffa yafaΙ—i haka cikin farinciki, duk da kuwa cewa dama tun abaya yasan cewa Dr.Sadeeq yanason Zahrah, amma sake tabbatar masa da Dr. Ι—in yayi yanzu, yasanyashi jin daΙ—i, domin shima yanzu burinsa shine ya inganta farincikin marainiyar Allah wato Zahrah..

Farinciki ne sosai yakama Dr.Sadeeq, yaji daΙ—in aminta dashi da Baffa yayi.

“Nagode da wannan dama da kabani Baffa, Allah yajiΖ™an magabata” Dr Sadeeq yafaΙ—a cike da girmamawa.

“Mune da godiya Likita, ai mu ba’abun da zamuce maka saidai fatan alkhairi” Baffa yafaΙ—a shima cikin jin daΙ—i, domin yasan Zahrah na auren Dr.Sadeeq wahalanta yaΖ™are da yardan Allah,saboda yana da tabbacin cewa Dr.Sadeeq zai bata kyakkyawan kulawa, duk da kuwa cewa Dr.Sadeeq Ι—in yasanar dashi cewa ba Zahrah ita kaΙ—ai zai auraba, yasanar dashi komai, kuma Baffa yayi na’am da hakan, saboda shi baimaga wani aibu acikin hakan ba, ai namiji mijin mace huΙ—u ne.

(Nima nace wannan gaskia ne, sbd haka duk me mace Ι—aya ya Ζ™ara??)1

Cike da farinciki Baffa da Likita sukayi sallama, yayinda Baffa yakoma cikin gida, ya kumace da Dr.Sadeeq zai turo masa Zahrah suyi sallama.

Tanajin Muryan Baffa a tsakar gida, tayi saurin share hawayenta, haΙ—e da miΖ™ewa tsaye, domin har Baffa yafara Ζ™waΙ—a mata Ζ™ira.

Fuska cike da fari’a Baffa yace “Likita ke yake jira, zai tafi”

Sumi sumi haka Zahrah ta fice yayinda tabar Baffa yana gayamawa Inna abun da ya wakana tsakaninsa da Likita.

Tun fitowarta yake ta zabga murmushi, kallo Ι—aya zakai mawa fuskarsa ka gane cewa yanacikin farinciki.

“Kitayani murna My Princess saura Ζ΄an kwanaki Ζ™alilan na mallake ki!” Dr Sadeeq yafaΙ—i haka cike da shauΖ™i.

Kunyane yakama Zahrah, don haka ta sanya duka hannayenta biyu ta rufe fuskarta, bayan ta Ζ™aΖ™alo murmushi ta aza akan fuskar ta..

“Baffa yabani daman naturo magabatana don asa mana ranan aure, kuma insha Allah, gobe magabatana zasu zo, za’asa ranan aurenmu nan bada jimawa ba, so sai ki shirya domin kin kusa zama amaryata!” yanayin yanda ya Ζ™are maganar kaΙ—ai ya isa taΙ“a zuciya..

Kunyane yasake kama Zahrah, har batasan sanda murmushi mai sauti ya kufce mata ba, gaba Ι—aya ta lura Dr.Sadeeq ya Ζ™osa da ayi aurensu bata kumasan dalilinsa nayin hakan ba..

STORY CONTINUES BELOW

“Kinyi shiru kodai bakya farinciki ne my princess?” yatambaya.

Ɗan satan kallonsa tayi haΙ—e da sakarmasa murmushi mai tsayawa a zuciya.

Ƙaran wayarsane ta katsesa daga kallonta da kuma zancen zucin da yakeyi. Ajiyar zuciya ya sauΖ™e ganin wacce take Ζ™iran nasa, maida wayar tasa cikin aljihu yayi batare daya Ι—aga Ζ™iran ba.

“Dare yayi Zahrah kishiga gida, zamuyi waya, kikulamin da kanki ” yafaΙ—i hakan yana me Ζ™oΖ™arin shiga cikin motarsa.

Murmushin dole Zahrah tayi haΙ—e da yi masa saida safe, tajuya ta nufi cikin gida, hakanan taji wani iri a zuciyarta duk da batasan me yasa baiΙ—aga Ζ™iran da ake mai ba, amma tana da yaΖ™inin cewa matar da zai aura tare da itane ta Ζ™irasa. Saurin kawar da tunanin tayi aranta, domin tuna hakan ma bashida amfani a gareta.

Washe Gari….

Kamar yanda Dr.Sadeeq yafaΙ—a hakanne ya kasance da da dare bayan sallan magriba Baffa Amadu shida amininsa suka zo gidansu Zahrah don tambayan aurenta, balaifi Baffa yayi musu tarba mai kyau, sunkuma ji daΙ—in hakan, duk da sun lura cewa suΙ—in basuda wani Ζ™arfi, ma’ana arziki…

Magana ta fahimta akayi tsakanin Baffa da kuma Baffa Amadu, a taΖ™aice dai Baffa yabasu auren Zahrah, yayinda sukuma suka Ι—au alΖ™awarin cewa a cikin satin za’akawo kayan tambaya dakuma na lefe, daga nan sai asa ranan aure, amma basason auren ya Ι—au lokaci, saboda rana Ι—aya suke so ayi dana Salima.. Da to kawai Baffa ya amsa musu domin shi baida wani abun cewa banda hakan, sai dai a Ζ™asan zuciyarsa tunani yake taya zai samu kuΙ—in da zaiyi mawa Zahrah kayan Ι—aki, domin dai bayanda za’ayi ace anyi aure ba kayan Ι—aki… Haka dai sukayi sallama cike da mutun ta juna…

Baffa ne Zaune akan tabarma ya yi jigum bakomai ke damunsa ba, kamar sha’anin auren Zahrah, Allah yasani ko abincin da za’aci abikin bai tanada ba, balle wata uwa uba kayan Ι—akin da za akaita dashi..

“Wai tunanin mekakeyine haka tun Ι—azu?” Inna dake zaune gefensa ta jefo masa tambaya.

“Ba dole nayi tunani ba Salame, kinga dai yau iyayen yaron nan Sadeeq suka zo, kuma da duk kan alama basa so aja auren nan yakai wani lokaci, kin kuma san halin dai da muke ciki na rashin kuΙ—i”

“Yo dama akan wannan kake Ι—aga hankalinka? hmm Malam kenan to ai ni banga abun Ι—aga hankali anan ba, ca nake shi Sadeeq Ι—in yasan duk halin da muke ciki, kuma shi yakawo kansa yace ya na so, bawai mu makai masa dole ba, saboda haka malam ka kwantar da hankalinka, Zahrah ya nema kuma Zahrah’n zamu bashi” Inna tafaΙ—i haka da’iyaka gaskiyarta…

Kallon Inna kawai Baffa yayi haΙ—e da girgiza kansa, yasan ma koda yayi Ζ™oΖ™arin fahimtar da’ita to fa bazata fahimta ba.

***

“What? Mom cewa fa kikayi wai bani kaΙ—ai Sadeeq zai aura ba, anya kuwa Mom kinji abun da Hajiya Habiba tafaΙ—amiki da kyau?” Salima tatambayi mahaifiyarta Hajiya Furaira cike da mamakin jin abun da mahaifiyarta tace da’ita..

“Abun da na faΙ—a miki shi naji daga bakin Hajiya Habiba, Salima kicire Sadeeq a ranki, domin kuwa aurenki dashi bazai taΙ“a yiyuwa ba, da raina dakuma hankalina bazan taΙ“a bari Ζ΄ata taje kan kishiya ba!” Hajiya Furaira tafaΙ—i haka cikin Ι“acin rai..

Kuka ne ya Ζ™wacemawa Salima cikin muryan kuka ta soma cewa “Wani irin cin amana ne wannan mom, sai da maganar aurena dashi ta kankama sannan wata banzar magana zata Ι“ullo, wallahi bazan haΖ™ura da shi ba, bakuma zan taΙ“a zama da wata a matsayin kishiyata ba, dole ne Sadeeq ya aureni ni Ι—aya batare da wata ba, bazan iya jure rashin saba Mom, dan Allah kiyi wani abu” Salima ta Ζ™are maganar cikin shaΙ“e shaΙ“e da hawaye.

“Mekikeso nayi Salima? so kike naje na basu haΖ™uri akan su sa Sadeeq ya aureki ke kaΙ—ai? ko ko sokike na zubar miki da Ζ™ima daΖ™uma Ζ΄ancinki? Hajiya Habiba Ζ΄ar uwatace kuma Ζ™awata, bantaΙ“a tunanin haka daga gareta ba, amma bakomai, zanyi maganin abun, kuma ni banzauna da kishiya ba, Ζ΄a tama bazata zuana da kishiya ba, wannan alΖ™awarine na Ι—aukar mawa kaina” still cikin Ι“acin rai Hajiya Furaira take maganan…

STORY CONTINUES BELOW

Cikin matsanancin Ι“acin rai Salima ta juya ta koma Ι—akinta, ji takeyi zuciyarta na tafarfasa, kamar ita ace ta haΙ—a miji da wata, sam bazai yi wuba, lallai ko da mahaifiyarta bazatayi wani abu ba yakamata ace ita tayi, wayarta da mayafinta ta Ι—auka, a fusace ta fice daga Ι—akin nata, tana son Sadeeq tun ba yau ba, zata kuma iyayin komai akan sa.

Ɓangaren Dr Sadeeq kuwa tuni yasoma haΙ—a mawa Zahrah kayan lefe, sosai yake iya Ζ™oΖ™arin sa wajen ganin yasanya duk wani abu da yasan zai burge Zahrah.

Ɓangaren Hajiyarsa da Aunty Raliya kuwa, sam basu wani damu da auren ba, hakanne ma yasa suka tura masa aniyarsa, su dai sunfi bada Ζ™arfi wajen ganin Salima tasamu abun da take so, yayinda Hajiya Furaira ta kafe kan cewa Ζ΄arta bazata auri Sadeeq ba matuΖ™ar ba’a fasa aurensa da Zahrah ba, ranta bai Ζ™ara Ι“aci ba ma, sai da taji labarin cewa Zahrah Ζ΄ar talakawa ne, sannan kuma bata da wani galihu, ai take ranta yaΖ™ara Ι“aci, tace sam bata amince ba, yayinda Salima kuwa ta kafe akan cewa lallai sai ta ruguza auren da Dr.Sadeeq yake nema bayan nata.

Gaba Ι—aya Zahrah ta ruΙ—e, zuwa yanzu wanda yake turo mata saΖ™o ya uzurawa rayuwarta, a yanda ta fahimta shine duk inda tayi yana biye da’ita, wani babban tashin hankali daya kunnu mata shine, sabbin saΖ™onnin da yafara turo mata a cikin wayarta, tagama iya hasashenta ko zata gano a ina yasamu number’n ta amma takasa samun daman sanin inda yasamu number’nta, gaba Ι—aya yanzu salon saΖ™onnin nasa sun sauya salo, domin kuwa yanzu saΖ™on kalamai yaΖ™e turo mata masu daΙ—i, wanda kuma duk rabin saΖ™on yaba kyawunta yake, babban abun daya Ζ™ara ruΙ—ata shine irin maΖ™udan kuΙ—aΙ—en dayake turomata ta waya. sannan kuma idan ta gwada Ζ™iran number’n da yake turo mata saΖ™o dashi, bata samu domin da zaran taΖ™ira wayan za’ace mata a kashe wayar take, hakan yasa tafara tunanin cewa kodai gamo tayi…

Ɗan Ζ™ara wayarta tayi alamar shigowar saΖ™o, take taji gabanta yafaΙ—i, zuwa yanzu har tsoro take taji wayarta tayi Ζ™ara, domin kuwa tasan idan har wayanta tayi Ζ™ara to ko Ζ™iran Dr.Sadeeq ko kuma saΖ™on mutumin da batasan shiba…

Number’n nan ce dai, da aka saba turo mata saΖ™o dashi, yauma saΖ™onne aka kuma turowa..

_Tunaninki ya hanani sukuni My Zahrah, ina fatan dai kina lafiya, ina kuma fatan zuwa yanzu kindaina tsoro da kuma mummunan tunanin da kikeyi akaina, kina da kyau My Zahrah, komai naki me kyau da burgewa ne._

Abun da saΖ™on ya Ζ™unsa kenan.

Zahrah ta karanta saΖ™on nan yafi sau biyar, kwata kwata ta kasa fahimtar abun da saΖ™on yake nufi.

Saurin yin Deleting saΖ™on tayi haΙ—e dayin switch off Ι—in wayar tata, bazata taΙ“a yarda wan nan mai saΖ™on ya haukata mata tunanin ta ba, yazama dole a gareta ta sanja layi.. Kwanciya tayi lamo tana mai addu’an Allah yasa bacci ya Ι—auketa. domin bacci ne kaΙ—ai zai kawo mata sauΖ™i a zuciyarta.

Zaune suke dukansu a Ι—an madai dai cin tsakar gidan nasu, domin dama idan dare yayi sukan zauna a tsakar gida su Ι—an taΙ“a hira, haka al’adarsu take..

Wani yarone yashigo cikin gidan bakinsa Ι—auke da sallama, haΙ—a baki sukayi wajen amsa masa sallaman.

“Wai ana sallama da mai gidan nan” yaron yafaΙ—a.

“To kace inazuwa” Baffa yafaΙ—i haka yana Ζ™oΖ™arin miΖ™ewa tsaye.

Kusan tare suka fita shida yaron sai da Baffa yaji wani irin faΙ—uwar gaba sakamakon wasu irin danΖ™ara danΖ™aran motoci guda biyu da yagani fake a Ζ™ofar gidansa.

Ja Baffa yayi ya tsaya turus yana me mamakin ganin waΖ΄an nan rantsatstsun motocin a Ζ™ofar gidansa, “Allah yasa da alkhairi suka zo” Baffa yafaΙ—i haka a cikin zuciyarsa.

BuΙ—e murfin motar Alhaji Ma’aruf yayi haΙ—e da sako Ζ™afarsa waje.

Sake waro idanu Baffa yayi haΙ—e da kafe Alhaji Ma’aruf dake Ζ™oΖ™arin fitowa daga cikin mota da ido.

Fuska cike da annuri Alhaji Ma’aruf ya Ζ™araso wajen Baffa, haΙ—e da miΖ™a masa hanu alamar su gaisa.

Cikin Ι—ari Ι—ari Baffa ya Ι—ago hanunsa haΙ—e da miΖ™amawa Alhaji Ma’aruf suka gaisa.

“Inafatan kaine ma mallakin wannan gida, kuma Baffa ga Zahrah?” Alhaji Ma’aruf ya tambaya.

Saida Baffa yaji zuciyarsa tayi tsalle sakamakon jin an ambaci Zahrah, Allah yasa ba wani abun Zahrah tajawo musu ba.

“Eh nine ranka ya daΙ—e, Allah yasa lafiya?” cikin dar Ι—ar Baffa yafaΙ—i hakan.

Murmushi irin nasu na manya Alhaji Ma’aruf yayi haΙ—e da kallon Baffa…”Nazo da magana mai mahimmanci, inaga zaifi kyautuwa kabiyoni cikin mota mu tattauna, don maganar bata tsaye bace”

Kallon Alhaji Ma’aruf Baffa yashiga yi, haΙ—e da excort Ι—in da suke bayan Alhaji’n, tabbas Alhaji Ma’aruf baiyi masa kama da irin mugayen mutanen nan ba, domin daga ka gansa zaka fahimci cewa dattijon arziki ne, hakanne yasa Baffa bai musa masa ba, yabisa zuwa mota..

Acikin mota kuwa bayan sun sake gaisawa, Alhaji Ma’aruf yayi gyaran murya haΙ—e da cewa…

“Sunana Alhaji Ma’aruf, kasancewar dare ne yasanya ka kasa shaida fuskata, domin ni ba Ι“oyayyen mutum bane. Nazo gare ka ne domin nemawa Ι—ana Auren Ζ³ar Wajenka Zahrah, ina fatan bazaka watsa mini Ζ™asa a ido ba”…….Shirune yashiga tsakanin Baffa dakuma Alhaji Ma’aruf,  bakomai ne kuma yasa hakan ba face nazari da Baffa yashigayi, lallai wannan abu da mamaki yake, neman aure mace Ι—aya duk alokaci guda.+

“Naji kayi shiru, Allah yasa dai ba wata matsala bace ta faru” Alhaji Ma’aruf  ya faΙ—a, domin ko kaΙ—an baya fatan wani abun da zai zo ya gifta har ya katsewa  Zaid cikar burinsa..

Gyara zama Baffa yayi haΙ—e da sauΖ™e ajiyar zuciya..

“A gaskiya Alhaji bazan Ι“oyemaka ba, yanzu haka na bada auren Zahrah ga wani,  wanda kuma tariga da ta aminta dashi, sai dai bazan yi saurin yanke hukunci ba, idan har Zahrah ta aminta dashi Ι—an wajen naka, shikenan, saboda ni bazan mata dole ba, duk wanda takawo tace shitake so, to  shi zan aura mata, amma kuma a iya sanina babu wani wanda yake zuwa wajenta, bayan likita’n dana bashi aurenta, sai dai kuma bansan shi Ι—an wajen naka a ina yaganta har yaji yanada burin aurenta ba”

Ɗan jim Alhaji Ma’aruf yayi haΙ—e da sauΖ™e ajiyar zuciya. Lallai yakamata yayi duk abun da zaiyi, domin shikansa yanaso Zaid  yayi aure, amma kuma yasan cewa nema cikin nema haramunne, tunda gashi har shi Baffan yarinyar ya ri ga daya shaida masa cewa yabada auren yarinyar ga wani, yazama dole suyi haΖ™uri kenan.

“Naji maganarka Malam Hayatu, nakuma gamsu, amma bayar da aurenta ga wani, ae  bashi yake nufin anΙ—aura aurenta ba, koda yaushe ra’ayin mutane yana iya sanjawa,  saboda haka zanbaka dama kayi tunani mai kyau” Alhaji Ma’aruf yafaΙ—i haka bayan yaciro wasu maΖ™udan kuΙ—i a cikin aljihun rigarsa ya Ι—auramawa Baffa akan cinyarsa..

Ware idanu Baffa yayi sakamakon ganin  maΖ™udan kuΙ—in da Alhaji Ma’aruf yaΙ—aura masa akan cinyarsa, badai yana nufin duk nasa bane.

Murmushi irin na manya Alhaji Ma’aruf yayi haΙ—e da cewa “Kada kadamu bawai nabaka kuΙ—innan bane,don ka bawa Ι—ana auren Ζ΄arka ba, nabaka ne kawai saboda shi meyin alkhairi ako da yaushe baya rasawa”

Cikin sanyin jiki Baffa yayi masa godiya haΙ—e da buΙ—e murfin motar yafita, zuciyarsa cike da Ι—unbin mamaki…

Baffa na fita daga motar Alhaji Ma’aruf yamawa driver’nsa umarni akan cewa su tafi, aikuwa ba Ι“ata lokaci drivern yatada mota..

Saida suka Ι“acewa ganinsa kafun Baffa ya iya Ι—auke idanunsa daga kansu,  kuΙ—in dake hanunsa yashiga juyawa,  “Lallai wannan mutumi yanada ihsani, amma kuma yazo da babbar magana, da ace yanada dama to da a yanzu yabawa Ι—an Alhaji Ma’aruf Ι—in auren Zahrah, to saidai kuma yanzu ya saduda, sakamakon wa’azi mai tsoratarwa dayaji akan cutar da maraya, da kuma irin azabar da za’amawa mai cutar da maraya,  tundaga wannan lokacin yaΖ™udurta aransa cewa bazai sake cutar da Zahrah ba, yanzu ma dolensa zai bata zaΙ“i, domin ita zatayi zaman auren ba shiba…

Yanashiga gida Inna da takasa zaune takasa tsaye, ta Ζ™araso wajensa da sauri tana me cewa “Lafiya naga ka jima, har nafara jin tsoro naΙ—auka irin mutanen nan ne masu garkuwa da mutane suka kamaka, domin na leΖ™a naga wasu fankama fankaman motoci a waje”

STORY CONTINUES BELOW

Harara Baffa ya wurgamata, haΙ—e da jan tsuka “Bazaki taΙ“a sanja halinki ba ko Salame, wato ke dai koda yaushe kai da kuma idanunki sunaga Ζ™ofar gida, kullum cikin leΖ™e kike, wato dai har dare ma yanzu leΖ™e kikeyi, Allah ya kyauta” yafaΙ—i haka yana mai nufar hanyar Ι—akinsa…

Fuska Inna ta Ι“ata haΙ—e da kafe aljihunsa da idanu, domin kuwa tuni idanunta sun Ζ™yallaro mata tudun da aljihunnasa yayi, Ζ™wafa tayi haΙ—e da rufa masa baya, koma mene sai

taje taganema idanunta, idan ma abuncine aci da’ita..

Sake gwalo idanu Inna tayi, ganin kuΙ—in da Baffa ya’aje akan gadonsa,   “Malam kace farar fita kayi, a shema baΖ™in arziki ne, nayi musu mummunar fahimta, ae irinsu muke fatan suta zuwa” washe da baki ta Ζ™are maganar…

“Akwai matsala Salame, amma jeki Ζ™iramin Zahrah” Baffa yafaΙ—a bayan yayimawa kansa mazauni, a bakin gadonsa.

“Yanzu kuwa” Inna tafaΙ—a tana me fita daga Ι—akin..

Zahrah ce zaune akan gadonta, game take bugawa a cikin wayarta, da’alama dai game Ι—in yayi mata daΙ—i, domin kuwa ita kaΙ—ai sai murmushi take.

Inna ce tashigo cikin Ι—akin haΙ—e sa shaida mata Ζ™iran da Baffa keyi mata,  haka nan taji gabanta yafaΙ—i. Tare suka fito da Inna, dukansu suka Ι—unguma zuwa Ι—akin Baffa’n…

Gyara zama Baffa yayi haΙ—e da maida kallonsa ga Zahrah, wacce ta duΖ™ar da kanta Ζ™asa.

“Bayan Likita akwai wani wanda kikasan yanasonki, ko kuma kika basa dama ya turo magabatansa wajena?”  Baffa yatambayeta cike da kulawa.

“A’A Baffa bana mu’amala da kowa sai likita, bankuma bawa kowa izinin zuwa wajenka ba” tafaΙ—i haka cike da girmamawa, duk da kuwa cewa kanta ya Ι—aure da jin tambayar da Baffa’n yayi mata…

Kai Baffa yajinjina haΙ—e da cewa “Ƙiran da akai min Ι—azu wani ne yazo nemawa Ι—ansa aurenki, shine nayi tunanin ko kinsan da zuwansa”

Wani irin bugawa Zahrah taji Ζ™irjinta yayi, har batasan sanda ta Ι—ago da idanunta ta kalli Baffa ba.

Baffane yacigaba da cewa “Bansan ko su Ι—in suwaye bane, amma ban Ι“oyemusu komai ba, nasanar dasu cewa nabada aurenki ga wani, amma mahaifin yaron yace yabani lokaci nayi tunani,  saboda hakane ma naΖ™iraki domin ni bazan miki dole ba,  zanbaki dama ne ki zaΙ“i wanda kikeso”

Take idanun Zahrah suka kawo Ζ™walla, sakamakon jin wani baΖ™on al’amari dayake shirin kunno kansa cikin rayuwarta.

“Kinyi shiru, ki kwantar da hankalinki bazan miki dole ba Zahrah, kema kina da Ζ΄an ci, zan kuma baki Ζ΄ancin ki, sai dai abun da nakeson sani  shine wanene yaron nasa, saboda bai yiwuwa a haΙ—aki aure  da wanda  bamusani ba, amma idan ke kinsan sa shikenan ba damuwa”

“Bansan saba Baffa, kuma ma koda nasansa bazan aminta dashi ba, saboda idan nayi haka ban yi mawa Dr.Sadeeq adalci ba” Zahrah tafaΙ—i haka cikin sanyayewar murya…

“Adalci, kaji shirmen banza don Allah Malam, wani adalcine yarage miki, wanda yawuce ki kai kanki cikin arziki kicisa yanda yakamata,  saidai ko inkuma baΖ™in ciki kike mana”

Inna ta tsomo bakinta cikin maganar batare da angayyaceta ba…

“Tashi kije Zahrah, idan suka sake zuwa zan sanar dasu cewa hakan da sukeso bazai yi wuba” Baffa yafaΙ—a, yana mai wurgamawa Inna harara..

Cikin rashin Ζ™warin jiki haΙ—e da Ι—aurewar kai Zahrah tabar Ι—akin..  Haushin Zahrah da Baffa ne yacika zuciyar Inna, amma ganin yanda Baffa yahaΙ—e fuska bai bata damar yin Ζ™orafi ba yasanya itama tafice daga Ι—akin tana me Ζ™ananan maganganunta wanda ita kaΙ—ai tasan metake cewa..

Zama Zahrah tayi jigum haΙ—e da zurfafa tunanin ta,  ba’abun dake bata mamaki da Ι—aure mata kai, kamar neman aurenta da Baffa yace anzo anyi,  “To waye zai zo neman aurenta batare da saninta ba? batare da ta kuma sanshiba, lallai koma waye baisan meyafaru da’ita ba, domin tasan daya sani, da baiyi gigin turo magabatansa nema masa aurenta ba” Haka dai tayita saΖ™awa da kuncewa har bacci ya Ι—auketa……

STORY CONTINUES BELOW

Cike da tsananin mamaki Zaid yake kallon mahaifinsa, sakamakon ji da yayi mahaifin nasa nacewa “Wai anbada auren Zahrah’nsa ga wani”  ” Anya kuwa gidan su Zahrah Dad Ι—insa yaje? kodai yayi mistake ne yaje wani gidan amadadin nasu Zahrah?” duk wannan tambayar kansa ya mawa.

“Inaga zaifi kyautuwa kanemi wata My Son, domin kafasan nema cikin nema haramunne”  Alhaji Ma’aruf ya faΙ—a yana me kallon Ι—an nasa.

“Inaga ba gidansu kaje ba Dad,

domin ni nasan Zahrah tawace, baza’a bawa wani ita ba bayanni” Zaid yafaΙ—i haka bayan yayi sipping holandia milk Ι—in dake aje cikin  glass cup Ι—in dake gabansa.

Kallon mamaki Alhaji Ma’aruf, yashiga yi mawa Zaid, sakamakon jin abun daya faΙ—a.

Baisan me yake shirin faruwa da Ι—ansa ba, amma tabbas ya hango wata irin soyayya acikin idanun Zaid Ι—in me matuΖ™ar zafi, wanda Zaid shikansa baisan da’ita ba…

“Akwai matan aure dayawa Zaid, zaifi kyau ka zaΙ“i wata, koda a cikin Ζ΄an uwankane” Alhaji Ma’aruf yafaΙ—i haka cikin lallashi. 

Murmushi kawai Zaid yayi haΙ—e da kallon mahaifin nasa…

“Kai mahaifinane saboda haka bana iya Ι“oye maka komai,  a gaskiya banjin zan iya zama da wata daban, idan ba Zahrah ba, zanyi komai da kaina kawai” yafaΙ—i haka yana me miΖ™ewa tsaye…  Da kallo kawai Alhaji Ma’aruf yabi sa dashi har ya fice daga cikin  falon nasa. Ajiyar zuciya yayi haΙ—e da cewa “wataΖ™ila idan kuΙ—i na magani, to zasu maya Zaid, ta hanyar samo masa auren Zahrah”

(hmm bakomai ake nema a samu ba, bakuma komai kuΙ—i yake iya saya ba)

Kai kawo Zaid yashigayi a tsakiyar tankamemen aljannar duniyar falonsa, gaba Ι—aΖ΄a yarasa me yake masa daΙ—i, shin maganar da Dad Ι—insa ya faΙ—a masa cewa anbada Zahrah, gaskiya ne kokuwa Dad Ι—innasa ne yayi mistake wajen gano gidan su Zahrah,  dudduniya babu wani mahaluΖ™i daya isa yimasa shamaki da muradinsa,   lallai lokaci yayi daya kamata ya bayyana kansa gareta,  baidamu da yanda zata Ι—aukesa ba, shidai burinsa kawai shine ya mallaketa amatsayin matarsa,    lallai yanzune zai gudanar da babban takunsa, sannan kuma yazama dole yagano bayanshi wayake bibiyan Zahrah, har ake yunΖ™urin aura masa ita, dole yagano wannan, domin yayi imani cewa Zahrah tasa ce…

***

Fitowarsu daga lecture kenan, wayarta tayi Ζ™ara alamar shigowar saΖ™o,, ko kaΙ—an batayi mamaki ba, domin zuwa yanzu tasaba da saΖ™onnin da’ake turo mata batakuma san waye yake mata hakan ba. 

Ajiyar zuciya ta sauΖ™e bayan ta gama karanta saΖ™on, yau madai kalamaine masu tsayawa a zuciya, Ι“oyayyen mutumin nata Ζ΄arubuta mata, sai dai kuma duk sanda ya turo mata da saΖ™o, idan takaranta kalaman sukan tsaya mata arai suna kuma yawan yi mata yawo a Ζ™waΖ™walwarta,   koda sau Ι—aya ne bata taΙ“a tunanin mayar masa da amsa ba, amma hakanan taji yau tanason tambayarsa ko shiΙ—in waye.

“Waye kai?” Abun da tarubuta tatura masa kenan.

Zaid dake kwance cikin wata luntsumemiyar kujera yana  sipping wine yaji wayarsa tayi Ζ™ara alamar shigowar saΖ™o,   Ι—aga wayartasa yayi yaduba, murmushinsa me kyau yayi bayan yagama karanta tambayar nata..

“Kinason ganina?”  shima yamayar mata da tambaya, tahanyar tura mata saΖ™o.

Zahrah na karanta saΖ™on tasoma typing kamar haka….”Mezai hana idan zaka bayyana kanka”  tana gama rubutawa tayi sending..

“Kishirya ranan friday 8:00 pm zankawomiki ziyara, ina fatan zakiji daΙ—in ganina, sannan zan taho miki da kyakkyawan surprise”  yana tabbatar da cewa saΖ™on ya isa zuwa wayarta, yayi switch off na wayarsa,   sake gyara  kwanciyansa  yayi ajikin kujeran, haΙ—e da lumshe idanunsa,  jiyake mararsa tana yi masa ciwo, kusan kwana uku kenan da yake fama da wannan ciwon maran,  hakan kuma yasamo asali ne da wata irin sha’awa da ta damesa, sai alokacinne ma yake tuna cewa yajima baiyi sex ba, lallai akwai abun da yake damunsa, Zaid Ι—in da baya iya kwana Ι—aya baiyi sex da mace ba, wai shine yanzu yake iya kwanaki batare da yayi sex ba,  shida mace Ι—ayama bata isan sa, amma sai gashi, yau Ι—ayan ma, yakasa nutsuwa yakusanceta, lallai yanzu kam yayarda da cewa akwai abun dake damun jiki da zuciyarsa….

Ɗan jim Zahrah tayi bayan tagama karanta saΖ™on nasa,  idan bata mantaba yau Tuesday kenan saura kwana biyu jumma’a tayi, lallai tanaso taga wanene wannan wanda yaΙ—au lokaci yan Ι“ata tunaninta,  ta wani Ι“angare na zuciyarta kuwa, ji takeyi tamkar akwai wani gagarumin abu dazai faru da’ita, yayinda idan ta tuna aurenta da Dr.Sadeeq  saitaji ta zama wani iri da’ita, bakuma aurenta da Dr. Ι—inne bataso ba, a’a kawai dai tanaji ajikinta kamar basu dace da juna ba ita dashi…

Dariya sosai Salima tashiga yi, sakamakon labarin da Ζ™awarta kuma aminiyarta Laura tabata yanzun.     Wani irin daΙ—i taji haΙ—e da sanyi acikin zuciyarta,  gaba Ι—aya labarin Zahrah Laura ta kwashe ta sanar da Salima, wanda Laura ta samo asalin labarin Zahrah ne daga bakin wata Asma da take unguwarsu Zahrah’n kuma har school Ι—insu Ι—ayama da Zahrah..

“Dama akan sauran wani Doctor yake wulaΖ™antani hadda jamin aji, hmm lallai kuwa bazanyi kishi da mai aji bama ballentana marar aji” Salima ta faΙ—i haka cike da kunfar baki…

“Ae magana taΖ™are Salima, kamar yanda na faΙ—amiki, tashi kawai zamuyi muje hargidansu, muci mata mutunci mukuma gargaΙ—eta da tafita hanyar Doctor Sadeeq” Laura tafaΙ—i haka cike da son zuga Salima.

“Gaskiya ne nima ina bayan maganarki Laura” wata wacce take zaune gefen Laura ta faΙ—i haka, tana me taΙ“e baki..

Kallonta Salima tayi haΙ—e da cewa “Shiyasa nake sonki Ζ™awata, bakida wasa, wajen sawa ayi rashin mutumci, idan kinshirya muje gidan nasu yanzu, domin akan Doctor sai inda Ζ™arfina ya Ζ™are” Salima tafaΙ—i haka tana maitashi daga zaunen da take.

Motar Salima suka shiga su duka ukun yayinda Laura ke tuΖ™asu, domin itace jagoran tafiyan kasancewa har gidansu Zahrah ta sani, saboda tasa Asma ta nuna mata….

Zahrah ce zaune a tsakar gida bisa kan tabarma, kwanon abincine aje a gabanta, gaba Ι—aya ta kasa tsayawa taci abincin yanda yakamata domin kuwa yau Thursday gobe ne kuma haΙ—uwarsu da mutumin dayake Ι“oye mata kansa, duka nutsuwarta baya gareta, hakanan takejin babu alkhairi a haΙ—uwarta da mutumin…

Wani irin bangaja da aka mawa Ζ™ofar gidansu shiyasanyata Ι—ago kanta takai kallonta zuwaga Ζ™ofar gidan nasu..

Wasu tsalan tsalan Ζ΄an mata su uku ta gani, tsaye ko wacce ta kafa makeken glass akan idonta, yayinda suke taunar cingam cike da iyawa haΙ—i da salo……Baki da hanci Zahrah ta sake tana kallon waΖ΄an nan Ζ΄an matan da suke tsaye suna me yimawa cikin gidannasu kallon wulaΖ™anci haΙ—e da Ζ™yama..+

Cire glass Ι—in dake idanunta Salima tayi, haΙ—e da watsamawa Zahrah wani irin kallo mai Ι—auke da mugun tsana, cike da Ζ™yama ta furzar da yawu, haΙ—e da kallon Laura “Itace wan nan?” Salima ta tambaya tana me nuna Zahrah da hanunta cike da taΖ™ama.

“Eh itace Ζ΄ar matsiyata” Laura ta faΙ—a tana yanatsina fuska.

“Lafiya kuwa bayin Allah? su waye ku? Zahrah ko kinsan sune?” Inna da fitowarta a Ι—aki kenan ta tambaya, Tana me mamakin ganinsu haΙ—i da aljabi.

“Ba alkhairi bane ya kawomu, saboda baku kai matsayin da zamuzo muku da alkhairi ba, sunana Salima, nazone domin najawa wannan matsiyaciya kuma karuwar Ζ΄ar taku kunne, koda wasa Doctor Sadeeq basa’an aurenta bane, saboda yawuce ajin macen da taraba mutuncinta a titi” takawa taci gaba da yi cikin isa harta Ζ™arasa gaban Zahrah, da ta kasa ko motsi… “Banzo danna cutar dake ba, amma tabbas idan kika sake nakuma dawowa cikin gidan nan to zanyi miki babban illa, rabuwa dashi zai fi miki, idan kuma kika Ζ™i, hmmmm zakisan cewa bakin rijiya bawajen wasan makaho bane, bake kaΙ—aiba, hatta tsohon da yake riΖ™e dake sai ya Ι—anΙ—ana” Salima tana kai Ζ™arshen zancen nata tamaida glass Ι—in ta dake riΖ™e a hanunta, haΙ—e da kallon su Laura “Muje” tace dasu, babu musu kuwa suka rufa mata baya, suna tafiya suna kareraya…

Tamkar statue haka Zahrah tayi Ζ™asaΖ™e tana kallonsu, harsuka fice daga cikin gidan.

Sallallami Inna tashiga yi haΙ—e da tafa hannuwanta duka biyu, “Lallai kuwa wa Ζ΄an nan Ζ΄an iska masu jajayen fuskar suncika marassa ta’ido, rashin kunya har cikin gida” Inna tafaΙ—i haka cike da mamaki.

Kai kawai Zahrah ta girgiza, haΙ—e da jawo kwanon abincinta ta ci gaba da ci, batare da ta tankawa Inna da take ta Ι“aΙ“atu ba,, sai dai kuma sosai maganganun Salima suka daki zuciyarta, har wani Ι—aci takeji a cikin maΖ™oshinta.. Tura abincin takeyi amma jinsa take tamkar maΙ—acin dayafi kowanne Ι—aci, har wani zafi takeji a Ζ™irjinta. Tana gama cin abincin, ta kora da ruwa, haΙ—e da tashi kai tsaye tanufi Ι—akinta.

“Karuwa” sunan da Salima taΖ™irata dashi yafiye mata komai ciwo, tunda take a duniya ba’a taΙ“a Ζ™iranta da sunan karuwa ba, sai a yau Ι—in, wasu irin zafafan hawayene taji sunshiga gangarowa daga cikin idanunta, durΖ™ushewa tayi a Ζ™asa haΙ—e da soma rusa kuka, filla filla kalaman da Salima ta faΙ—a mata suke dawowa cikin kanta, koda wasa bata taΙ“a tunanin za’afaΙ—i kalma na Ι“atanci masu muni irin haka akan ta ba.

“Kacuceni Zaid, Kacuceni, me yasa ka aikata haka agareni, shin koda sau Ι—aya ne bakayi tunanin yanda rayuwata zata kasance ba, bazan taΙ“a yafe maka ba Zaid har kuwa nakoma ga mahaliccina” cikin kuka ta Ζ™are maganar, domin kuwa sai yau tasake tabbatar da cewa Zaid ya cuceta, takuma Ζ™ara jin matsanancin zafi dakuma ciwo akan fyaΙ—en da Zaid yayi mata.. Abu kamar wasa haka Zahrah tayita kuka tamkar ranta zai fita, sai gashi cikin mintuna Ζ™alilan ciwon kai yakawomata ziyara, wanda har sai da yakaita ga kwanciya.. Ƙiran Dr.Sadeeq ne yashigo cikin wayarta amma tanaji tana gani takasa picking call Ι—in har wayan ta tsinke, taΖ™i Ι—aga wayan ne kuma don bataso yafahimci cewa tana cikin damuwa. Wani Ζ™iran nasa ne kuma yasake shigowa, still dai har wayan ta katse, Zahrah bata Ι—auka ba, domin har yanzu bata dawo cikin nutsuwarta ba.. Ƙira na uku ne yakuma shigowa cikin wayarta ta, Ζ™oΖ™ari tayi wajen Ι“oye damuwarta haΙ—e da Ι—aukan wayar ta kara akan kunnenta..

STORY CONTINUES BELOW

Ajiyar zuciya Dr.Sadeeq yasauΖ™e sakamakon ji dayayi ta Ι—aga wayan.

“Wani irin laifi me girma na’aikata haka da aka Ζ™i amasa wayata?” Dr.Sadeeq yatambaya.

Cikin sanyin murya Zahrah tace dashi “Bana kusa ne shiyasa”

Wata ajiyar zuciya yakuma sauΖ™ewa cike da kulawa yace “Naji muryarki ta sauya ina fata dai kina halin lafiya?” cikin kulawa ya Ζ™are maganar.

“Lafiya Ζ™alau” tabasa amasa a taΖ™aice.

“Yakamata nazo muyi magana domin inaso nasan irin shirye shiryen da zakiyi, idan lokacin auren mu ya gabato, kinsan yakamata ace anfarayin komai akan lokaci, yanzu ina tuΖ™i ne idan na tsaya zanΖ™iraki”

“To” kawai ta’iya cewa dashi, har ya katse Ζ™iran.

Tanacire wayar akan kunnenta saΖ™o yashigo cikin wayar.

“Nakan ji wani iri a jikina idan har kina cikin wani irin yanayi, ki daina sa kanki a damuwa, saboda zaki iya cutar da zuciyarki, nikuma bazan so haka ba, saboda kece muradina” abun da saΖ™on yaΖ™unsa kenan..

Tsuka Zahrah tayi bayan tagama karanta saΖ™on, haΙ—e da kashe wayarta ta baki Ι—aya, jira take kawai Allah yakaita gobe taga wayane yake raina mata hankali haka, daga goben kuma zata takamawa komaye birki, domin kuwa ko ma wayene bazai taΙ“a burgeta ba, zuwa yanzu babu wani Ι—a Namiji da zaiyi tasiri acikin zuciyarta.

Zaid ne kwance akan makeken gadonsa wanda yasha bedsheet na alfarma, kwanciyar nan yayi irin wanda ba kyau, wato rufda ciki, wata doguwar takarda ne riΖ™e a hanunsa, wanda take Ζ™unshe da duk wani abu daya Ζ™unshi Dr.Sadeeq daga kan sunansa aikinsa har zuwa mazauninsa, dakuma a halinsa, kyakkyawan bincike Zaid yasa a kayi masa akan Doctor Ι—in, saboda a cewarsa babu wanda ya’isa ya shiga huruminsa, saboda Zahrah tasace shi kaΙ—ai, saboda haka dole ne zaitakawa Dr.Sadeeq birki..

Murmushine ya bayyana akan fuskarsa bayan yasanya duka hanunsa biyu ya shafi sajen dake kwance akan fuskarsa,, shi kansa yaΖ™osa gobe tayi yaga Zahrah’n sa, duk da kuwa cewa yana biye da duk wani shiga da ficenta, amma kwata kwata baya gajiyawa da ganinta, sam baisan meke damunsa ba, zuwa yanzu yafara kokonto dakuma tunani anya ba wannan abun da yakeji shi ake Ζ™ira soyayya ba kuwa? Idan kuwa harda gaske abun nan da yakeji a game da Zahrah shi ake Ζ™ira soyayya, to tabbas yakamu da so matsananci, sai dai kuma bayida ikon tabbatarwa kansa cewa so yake, hakanne ma ya hanasa gane wanni hali yake ciki, ko da wasa bai taΙ“a tunanin cewa Zahrah zata Ζ™isa ba, saboda haka ako da yaushe cikin Ζ™arawa kansa Ζ™warin guiwa yake….

FRIDAY

Rana bata Ζ™arya, ranan yau ta kasance Friday kuma yaune Ɓoyayyen mutumin ta yayi mata alΖ™awarin baiyana kansa gareta, sai dai kuma baΖ™on al’amarin da ta wayi gari dashi yasoma tsinkar mata da zuciya, haΙ—e da sanyayewar jiki, domin kuwa yau ta tashi tana me jin faΙ—uwar gaba, haΙ—e da bugawan zuciya da akai akai, hakan kuwa baΖ™aramin tsoro yajefata ciki ba, saboda bata taΙ“a mantawa irin wannan faΙ—uwar gaban ta dinga ji a ranan da mummunar Ζ™addaranta zata rusketa,, sai dai kuma babu abun da yagagari Allah, don haka ta shiga yin addu’o’i acikin zuciyarta, saboda ta samu salama..

Ƙarfe Uku na yammaci de de suka fito a lecture’n Ζ™arshe da suke dashi na wannan ranan, gaba Ι—aya sukuku haka ta wuni a cikin school Ι—in, Husnah tayi tambayan har ta gaji, akan ta faΙ—a mata meke damunta amma tace ba komai, to me zatace mata? ita kanta batasan meyake damunta ba.

Su Husnah ne suka kawota har Ζ™ofar gida, saboda yanzu Dr.Sadeeq aiki yamasa yawa sosai, ga aikin office ga kuma hidiman hada hadan biki, gaba Ι—aya baya samun isashshen lokaci, hakan yasa idan sun tashi a school take shiga motar da ake zuwa Ι—aukar Husnah su sauΖ™eta a gida…

Tun azaure take ta kwaΙ—a sallama harta shigo cikin gidan nasu, amma babu wanda ya amsa mata, hakan yasa ta tabbatar cewa bakowa acikin gidan, har Ι—aki ta leΖ™a amma babu Inna babu alamarta, saboda haka kai tsaye ta wuce Ι—akinta. Zama tayi jigum tamkar wacce aka mawa mutuwa, fargaban haΙ—uwa da Ι“oyayyen mutumin nan take, hakanan takeji dama bata nemi ganinsa ba, saboda gaba Ι—aya jikinta yagaya mata babu alkhairi a haΙ—uwarsu, sai dai kuma babu yanda ta’iya tunda ya tabbatar mata da cewa yau Ι—in zaizo, ganin da tayi tunani na shirin damunta, yasa ta Ι—auko alΖ™ur’ani mai girma tasoma karantawa, saboda hakan yana sauΖ™ar da salama sosai acikin zuciyar wanda yake cikin Ζ™unci da fargaba….

STORY CONTINUES BELOW

Tana kai sujjadar Ζ™arshe ta sallan isha tafashe da wani irin kuka me tsuma zuciya, hakan yafarune kuma saboda ta kasa control Ι—in kanta, sosai faΙ—uwar gaban da takeji yake tsanan ta aduk bayan wasu mintuna.. Cikin kuka tasamu ta sallame sallan isha Ι—in, bayan ta gama faΙ—awa ALLAH buΖ™atunta, tana me kuma neman sauΖ™i a garesa, idanunta da suke cike da hawaye ta Ι—aga haΙ—e da maida kallon ta ga yagalgalellen agogon bangon dake Ι—akin nata, Ζ™arfe bakwai da arba’in, saura mintunan da basufi Ashirin ba yaΖ™araso kenan, domin Ζ™arfe takwas yace mata zai zo…

Bugawan da agogo yayi 8:00 pm, yayi dai dai da bugawar zuciyar Zahrah, har saida taji cikinta yabada wani sauti. Kallon agogo takumayi akaro na barkatai, bazata iya tantance me takeji ajikinta ba, tsoro ne kokuma ruΙ—ewa ne, takasa banbancewa.

Idanun Zahrah nakan agogo har Ζ™arfe takwas da minti biyar, ko Ζ™yafta idanun ta batayi ba, azahiri agogon take kallo, amma a baΙ—ini ba da idanunta take kallo ba, da Ζ™waΖ™walwarta take gani, kallon agogon kawai take amma bata fahimta saboda tunaninta ba a kansa yake ba.

SaΖ™one yashigo cikin wayarta, wanda yayi dai dai da kusan Ι—aukewar numfashinta.

“InaΖ™ofar gidan ku” bakinta na rawa haka takaranta saΖ™on saikace wanda aka turomata saΖ™on ranar mutuwarta.

Takai kusan minti huΙ—u tana sake maimaita karanta saΖ™on, sai kace wanda aka yo saΖ™on da wani harshe bana hausa ba, idan kaga yanda take karanta saΖ™on zakai tunanin bata iya hausa bane, kokuma bata gane abun da saΖ™on yake nufi ba, bakomai yasa hakan ba kuma face tsoro da taji ya daki zuciyar ta, yayinda gabanta yatsananta faΙ—uwa, tabbas wannan faΙ—uwar gaban bana haka kawai bane, lallai dole akwai abun da zai faru da ita, amma kuma yazama dole taje taga wanda yake turomata saΖ™onni, hanunta na rawa haka ta Ι—au hijib Ι—inta ta sanya, da Ζ™yar take iya jan Ζ™afanta ta fita daga Ι—akin…

Inna ta iske zaune a tsakar gida, tana jin radio, “Inada baΖ™o a waje Inna” Zahrah tafaΙ—a cikin wata irin murya me rauni. Yanayin yanda Inna taji muryan Zahrah yasanya ta Ι—ago da kanta ta kalle ta, “Lafiyanki kuwa, meke damunki?” Inna tatambaya cike da mamakin yanda taga jikin Zahrah a sanyaye.

“Babu komai Inna” Zahrah tafaΙ—i haka tana me nufar hanyar Ζ™ofar fita daga gidan..

Kasancewar akwai wadataccen haske a Ζ™ofar gidan nasu na Ζ™oyayen wuta wanda maΖ™otansu suka kukkuna hakan yasa wajen baida duhu, zaka iya hango duk wanda ke tsaye dakuma wanda ke tsugunne, kai harma wanda ke kwance zaka iya ganinsa.

Bugun zuciyarta ne yaΖ™aru yayinda Ζ™afofinta suka soma yi mata nauyi, wani mutumi tagani tsaye ajikin wata mota da ta amsa sunanta mota, sai dai kuma yajuya baya, saboda haka bayansa kawai take iya hangowa, sanye yake da wandon jeans black dakuma black Ι—in riga sannan kuma akwai hula irin fosin kaf Ι—in nan akansa. A hankali take taka Ζ™afafunta dasuka mata nauyi tanufi inda yake tsaye, yayinda ta sanya hanunta ta cikin hijab Ι—inta ta dafe Ζ™irjinta da takejinsa kamar zai daka tsalle yafito waje..

Abu na farko daya fara hargitsa mata Ζ™wakwalwa bayan ta isa gareshi shine fitinannen Ζ™amshin turarensa wanda har gaban abada bazata taΙ“a manta wan nan Ζ™amshin ba, wani irin killer smile Zaid yayi bayan yatabbatar da cewa ta karaso gab dashi, fuskarsa Ι—auke da murmushi ya juyo zuwa gareta, haΙ—e da sanya hanunsa ya cire hular dake kansa, take kyakkyawar fuskarsa ta bayyana, wacce take Ι—auke da murmushi.

Jikinta ne yaΙ—auki rawa yayinda idanunta suka Ζ™ara buΙ—ewa take numfashinta yasoma Ζ™oΖ™arin Ζ™wacewa, zuciyarta tashiga duka, Ζ™afafunta suka Ζ™age waje Ι—aya, yayinda hawaye suka dinga fitowa daga idanunta tamkar anyi ambaliyan su.

Kallon yanda jikinta yake rawa Zaid yayi haΙ—e da dawo da kallonsa kan fuskarta jefa idanunsa yayi cikin nata. “ZAHRAH!” yaΖ™ira sunanta da wata irin murya me sanyi, sakamakon ganin da yayi kamar cewa bata cikin hayyacinta…

“ZAHRAH” yasake Ζ™iran sunanta, de de lokacin ne kuma numfashin ta yashiga gudu yana neman Ζ™wace mata, aikuwa kasa fusgo numfashin nata tayi, lokaci Ι—aya numfashinta yayi nasaran fita daga jikinta, take ta yanki jiki tafaΙ—i warwas a Ζ™asa, cikin mugun tashin hankali Zaid yayi kanta, haΙ—e da sanya hannayensa duka biyu ya Ι—agota zuwa jikinsa, sunanta yashiga Ζ™ira cikin tashin hankali dakuma ruΙ—ewa, a matuΖ™ar firgice ya sanyata acikin motarsa haΙ—e da shiga cikin motar da wani irin gudun gaske Zaid yafigi motar ya cillata kan titi… Gaba Ι—aya ya ruΙ—e wani irin gudu yake shararawa baburuwansa da wanda ke gabansa ko bayansa, gaba Ι—aya ya ruΙ—e sunan Zahrah kawai yake ambata, Allah yasa ba zuciyarta ta haΙ—iya ba..

STORY CONTINUES BELOW

Matsanancin gudun da Zaid yakeyi har ya wuce hankali, da wani irin gudu yashigo cikin asibitin yayin da ya Ι—auko Zahrah caΙ—ak a hanunsa tamkar wata Ζ΄ar tsana, haka yashigo da’ita cikin asibitin, ganin haka yasa Doctors sukayo kansa da sauri, hankalinsa a matuΖ™ar tashe ya miΖ™a ta ga doctors sukayi emergency da’ita kai tsaye.. Taimakon gaggawa likitoci suka shiga bawa Zahrah domin kuwa bako maine ya haifar mata da Ι—aukewar numfashin ba, face razana dakuma tsananin firgita haΙ—i da tsoro da suka rusketa alokaci guda, sannan yanayin yanda zuciyarta ke bugawa, yawuce mizani, idan har zuciyar tata tacigaba da bugawa da sauri sauri haka, tofa lalllai rayuwar Zahrah tana cikin haΙ—ari…

(Niko nace idan Zaid yakashe mana Zahrah zamuci …. ko fans?)1

Iya ruΙ—ewa Zaid ya ruΙ—e yakasa koda zamane, damuwarsa Ι—aya shine Doctors Ι—in da suke kan Zahrah, su sanar dashi meke faruwa, lallai idan har Zahrah tasamu wani matsala, to bazai taΙ“a yafewa kansa ba, sannan kuma babu uban da ya’isa yazauna lafiya, matuΖ™ar likitocin nan suka kasa shawo kan matsalan Zahrah..

Kusan minti talatin likitocin nan sukayi suna Ζ™oΖ™arin shawo kan numfashin Zahrah, cikin ikon Allah kuwa sun samu komai yayi dai dai sai dai dole tana buΖ™atar hutu kodan zuciyarta ta samu salama…

Suna fitowa Zaid yayi kansu, gaba Ι—aya idanunsa sun kaΙ—a sunyi jajur dasu.

Kallonsa Ι—aya daga cikin manyan likitocin dasuke kan Zahrah yayi haΙ—e da dafa kafaΙ—unsa, “Ka kwantar da hankalinka, komai yayi dai dai, yanzu biyoni office Ι—ina”

Ba musu balle girman kai Zaid ya bi bayan liikitan.

Kasa zama akan kujeran da Dr Ι—in yabasa yayi, babban damuwarsa shine yasan wani hali Zahrah take ciki.

“Nace ka kwantar da hankalinka, kazauna saimuyi magana ko” likitan yafaΙ—a yana me nuna masa kujera..

“Kaga Doctor bazamane yadameni ba, babban damuwana shine nasan wani hali take ciki” Zaid yafaΙ—i haka cikin damuwa..

“Zan faΙ—ama ko wani hali take ciki, amma dole sai ka zauna”

Badon Zaid yasoba haka yazauna akan kujera haΙ—e da sanya duka hanunsa ya dafe kansa.

“Bawani babban abubane yake damunta, akwai abun da yafirgita ta ne, kuma dama anasamun irin haka, sau da dama firgici da tsoro, yakansa mutum yasamu Ι—aukewar numfashi naΙ—an wasu daΖ™iΖ™u, amma idan tadawo hayyacinta komai zaidawo dai dai, sai dai kuma tana buΖ™atar hutu sosai, saboda haka bayau zaku samu sallama ba, dole sai kunjira zuwa gobe da safe, saboda yanzu haka akwai alluran damuka mata kuma suna sa bacci sosai”

Ajiyar zuciya me Ζ™arfi Zaid ya sauΖ™e, saboda jin bayanan Doctor da yayi, sun sauΖ™ar masa da nutsuwa “Amma dole sai anan zamu kwana? me zai hana kabani ita mutafi gida, idan yaso saitayi baccinta acan” Zaid yafaΙ—i haka fuskarsa Ι—auke da damuwa.

Murmushi Doctor yayi haΙ—e da cewa “Hakan bazai samu ba, saboda zata iya farkawa da kowani lokaci, bamu kuma san a wani hali zata tsinci kanta ba, bayan ta farka, saboda haka zamanku anan Ι—in zaifi amfani” Doctor yafaΙ—i haka cike dason gamsar da Zaid.

Kai kawai Zaid yajinjina haΙ—e da kallon Doctor “Zan’iya ganinta kuwa? sannan kuma inaso akaita Ι—aki na musamman konawane kuΙ—in Ι—akin zan biya”

“Wannan ba’abun damuwa bane, zamu kaita Ι—aki na musamman sannan kuma zaka iya ganinta, bana Ζ™ira nurse sai a sanja mata Ι—aki daganan saikaje ka ganta ko” Dr yafaΙ—i haka bayan yakara waya akan kunnensa. Cikin mintuna Ζ™alilan aka sanjawa Zahrah Ι—aki inda aka kaita Ι—aki na musamman.

Zaid ne tsaye akanta yana me Ζ™are mata kallo, karo na farko kenan daya farajin wani irin matsanancin tausayin ta acikin zuciyarsa, haΙ—e da wani shauΖ™i mai fisgar zuciya. A hankali yaΖ™araso dab da gadon nataz haΙ—e da ranΖ™wafo da kansa dakuma Ζ™irjinsa zuwa gaf da’ita, lumshe idanunsa yayi haΙ—i da kai bakinsa gefen kumatunta ya yi mata kiss, haΙ—e da sa hanu yashafi gefen fuskarta, “I’m sorry Zahrah!” yafaΙ—i haka acikin maΖ™oshinsa. Karo na farko kenan a rayuwarsa daya soma bawa wata mace haΖ™uri.. Zama yayi a bakin gadon, haΙ—e da kama hanunta na dama yasanya acikin nasa hanun, a hankali yake murza hanunta haΙ—e da lumshe idanunsa.

Abu kamar wasa hankalin Inna ne yasoma tashi ganin Zahrah ta kwashe sama da awa Ι—aya, a waje batare da ta shigo gida ba, gashi ta leΖ™a waje bataga ko da me kamannin Zahrah bane, kasa zama inna tayi gaba Ι—aya hankalinta a tashe yake, Baffa ne yashigo cikin gidan bakinsa Ι—auke da sallama, ko amsa sallaman nasa Inna batayi ba tayo kansa tana cewa “Yau wa Malam gwamma da ka dawo, ko ka haΙ—u da Zahrah a waje kuwa?”

“Zahrah kuma, ina Zahrah’n take?” Baffa yatambaya cike da mamaki.

Nan Inna tashaida masa cewa tunΙ—azu tafita bata dawo ba,bayan tasanar mata cewa wani ne yaΖ™ira ta a waje.

Take hankalin Baffa yatashi, domin kuwa Zahrah bata taΙ“a irin haka ba, har maΖ™ota ya aika ko taje amma aka ce masa bata zoba, take Baffa da Inna suka zuba tagumi, sun marasa ta ina zasu fara, Inna cema takawo shawara akan cewa aΖ™ira Doctor Sadeeq koshine yazo ya Ι—auketa, aikuwa Baffa yayi na’am take yadannawa number’n Dr.Sadeeq Ζ™ira, bugu biyu Dr.Sadeeq yaΙ—aga wayan,, shima bakaΙ—an ba hankalinsa yatashi jin dayayi cewa wai su Baffa basuga Zahrah ba, ae take yashiga motarsa yataho gidansu Zahrah’n duk da cewa dare yayi…

Kallon agogon hanunsa Zaid yayi a karo na barkatai, Ζ™arfe 10 na dare kenan, ajiyar zuciya ya sauΖ™e akaro na uku, haΙ—e da furzar da iska a bakinsa, kallonsa yakuma mayarwa ga Zahrah, wacce take ta sharan bacci, hakanan yatsinci kansa da sakin murmushi mai sauti, komai na Zahrah me kyaune, tafiyin kyau ma idan tana bacci.

Zama yayi akan wata kujera dake kusa da gadon haΙ—e da jingina bayansa da jikin bango, lumshe idanunsa yayi tare da cije laΙ“Ι“ansa sai yanzu Ζ΄ake tunanin ya makomarsa zai kasance idan Zahrah tafarfaΙ—o, domin kuwa ya hango muguwar tsanarsa acikin idanunta.Lokaci Ι—aya hankalin Dr.Sadeeq yayi wani irin mummunan tashi, take Ζ™waΖ™walwar kansa tashiga charge, a iya tsawon sanin da ya yi mawa Zahrah, ita ba mace bace meson fitar dare, balle har tayi nisa da gida, sai dai kuma abun mamaki gashi yau annemeta an rasa, bayan ko Ι—azu suna tare a waya shida ita, baikuma ji wani sauyi a tattare da’ita ba, sai dai kawai muryarta da yaji cikin sanyi. “To ina Zahrah taje?”

Yayi mawa kansa tambayar da bayi da amsa.. “Kodai Zahrah tayi hakane don batason aurena da’ita?” yakuma tambayar kansa, sai da zuciyarsa ta buga, shi kansa yatambayi kansa abun daya faΙ—ar masa da gaba, kai amma Zahrah bazatayi haka ba, saboda ita da kanta ta tabbatar masa cewa ta amince da auren sa, saboda haka bazata bar gida saboda batason auren sa ba..

Kallonsa yamaida ga Inna wacce tayi tsuru tsuru da ido tamkar wata munafuka…”Da tazo fita bakiga wani alaman damuwa ko tashin hankali akan fuskarta ba?” Dr yatambaya cike da kulawa.+

“Ƙwarai kuwa da damuwa tafita, saboda kwana biyun nan gaba Ι—aya da damuwa take wuni sakamakon waΖ΄ansu tsinannun Ζ΄an mata da suka zo, acewar Ι—aya daga cikin su wai ita zaka aura Samira take ko Salma oho, haka nan suka zo hargida suka zagemu kaf, tamkar ma zasu mana luguden duka, to tundaga tafiyarsu dai take fama da Ζ™uncin rai har kawo yau, Allah dai yasa ma basune sukai mata wani abun ba” Inna tafaΙ—i haka cike da jimami..

Cike da mamaki Dr.Sadeeq yace “What Salima tazo har gidan nan taci muku mutunci?”

“Ƙwarai kuwa ashe dagaske kasanta, tabbas haka tace sunanta wai Salima, ita da waΖ΄ansu masu Ζ™oΖ™aΖ™Ζ™un fuska, kamar an gasa nama”

Hanu Dr.Sadeeq yasanya yadafe kansa, lallai idan de har Salima bata ji kunyar zuwa ta zagar masa abar sonsa ba, to tabbas shima bazaiji kunyar zuwa har gidansu yaci mata mutumci ba, Uwa mahaifiyarsa kaΙ—ai ze iya Ι—agawa Ζ™afa akan Zahrah, amma duk wacce tace zata ci mutumcin Zahrah tofa shima zaici nata mutuncin, lallai yakamata ne yafara nemo inda Zahrah take kafun yasan matakin da zai Ι—auka akan Salima. Sake dialing number’n Zahrah yayi amma still ce masa ake wai wayar akashe take, tun Ι—azu yake Ζ™iran wayar anacemasa akashe wayarta ta take.. Tunanin Ζ™iran abokinsa inspector Adam ne ya faΙ—o masa, saboda yalura lamarin dole sai anshigo da hukuma ciki, tunkan suyi sake lokaci ya Ζ™ure musu. Nan yashiga dialing Number’n inspector Adam amma har wayar ta katse bai Ι—auka ba, sake Ζ™ira yayi amma still bai Ι—auki wayar ba, tsuka Dr.Sadeeq yayi haΙ—e da maida wayarsa cikin aljihunsa….

Asibiti

Sai yanzu tunanin halin da iyayen Zahrah zasu shiga yafaΙ—o masa arai, tabbas yakamata ne yasanar dasu halin da ake ciki, wayarsa yaΙ—auka haΙ—e da soma rubuta saΖ™o, domin bayason wayar da zaiyi yatashi Zahrah a baccin da takeyi, saboda haka gwamma yatura saΖ™o,a ganinsa hakan zaifi… wata number yaturawa saΖ™on, batare da yajira amsar da wanda yaturawa saΖ™on zai basa ba, ya maida wayarsa cikin aljihu…..

Dr.Sadeq ne yadubi Baffa dake a halin damuwa. “Banaje nasanarmawa Ζ΄an sanda, akwai abokina inspector, inaga kawai gwamma naje gidansa na sanar dashi abunda ke faruwa, ina ga zaifi akan tsayuwan damuke” yafaΙ—i maganar yana me duba agogon dake Ι—aure a tsintsiyar hanunsa, Ζ™arfe sha Ι—aya na dare kenan agogon sa yanuna masa..

STORY CONTINUES BELOW

Sallaman da sukaji ana kwaΙ—awa a Ζ™ofar gidan ne yaΙ—auki hankalinsu, ae ba shiri Baffa da Dr. Sadeeq suka Ι—unguma zuwa Ζ™ofar gidan, Inna ma ba’a barta a baya ba ta rufa musu baya.

Wani mutumi me shigar cute baΖ™aΖ™e suka gani tsaye a bakin Ζ™ofar gidan, yayinda yarufe idanunsa da tabarau, da ganinsa dai zaka gane irin body guard Ι—in nan ne.

“Waye kai?” Dr.Sadeeq yatambaya yana me Ζ™aremasa kallo.

“SaΖ™o aka bani nasanar daku cewa Zahrah bata da lafiya, yanzu haka tana asibiti..” baikai ga idar da zancen nasa ba, Dr.Sadeeq yace “Meyasameta sannan kuma a wani asibiti take?” duka tambayar yayisune alokaci Ι—aya, kuma

cikin ruΙ—ewa..

“Zaku iya biyoni muje” Body guard Ι—in nan yafaΙ—a yana me nufar wajen da motar da yazo da ita ke fake.

Kallon su Baffa Dr.Sadeeq yayi haΙ—e da cewa su shigo motarsa subi bayan body guard Ι—in, hakan kuwa akayi motar Dr.suka shiga yayinda Dr.yashiga bin bayan motar body guard Ι—in. Gaba Ι—aya ba acikin nutsuwarsa yake driving Ι—in ba. Fargabane cike a zuciyarsa, bayi da wani buri da yawuce yaga Zahrah, yakuma ji meke damunta, har aka kawota asibiti batare da sanin su Baffa ba..

Suna shiga cikin asbitin wannan body guard Ι—in ya kalli Dr.Sadeeq haΙ—e da cewa ya biyosa ciki, su Inna kuwa su jirasa, da su Inna sunso Ζ™i, amma sai Dr. Sadeeq yace su yarda su jirasu anan Ι—in, badon su Inna sun so ba, suka tsaya daga waje… Suna shiga cikin wani corridor guard Ι—in yaciro wayarsa, haΙ—e da karawa akan kunnensa.

“Oga na faΙ—a musu sunma biyoni, yanzu haka munatare da wani inazaton Ι—an uwanta ne, iyayenta kuma suna waje” Abunda Body guard Ι—in yafaΙ—a kenan cike da girmamawa.

Tsuka Zaid yayi sakamakon jin abunda guard Ι—in nasa ya ce, shirmen banza, cewa yayi yafaΙ—amusu bawai ya taho masa dasu ba, to yanzu dayakawosu ina zai sasu, wata tsukan yakuma yi, haΙ—e da sakai yafice daga cikin Ι—akin bayan ya sake rufe Zahrah da bargo..

Cakume kwalan guard Ι—in nan Dr.Sadeeq yayi cike da Ι“acin rai yace “Bamason iskancin banza kace tana asibiti bata da lafiya, gashi munzo kuma kana Ζ™oΖ™arin raina mana hankali, wlh idan wani abu yasameta saina Ι—aureka” Cikin Ι“acin rai Dr.Sadeeq yafaΙ—i maganan domin kuwa yulura guard Ι—in nema yake ya raina masa hankali….

“Idan har ka’iya Ι—auresa, to tabbas zan iya yarda na Ζ™iraka da suna jarumi !!” muryar Zaid takaraΙ—e wajen, wanda yake Ζ™arasowa garesu cikin takunsa na isa..

Kallon Kallo aka shigayi tsakanin Zaid dakuma Dr.Sadeeq, wanda kowannensu da irin manufar tasa kallon.

Sama da 5 minute Zaid da Dr.Sadeeq suka Ι—auka suna kallon juna, Zaid nayimawa Dr.Sadeeq kallon tsana, yayinda Dr.Sadeeq kuma kemawa Zaid kallon tuhuma, haΙ—e da son sanin koshi waye…

Kallon guard Ι—in nan Zaid yayi haΙ—e da taΙ“e bakinsa cike da isa yanuna Dr.Sadeeq haΙ—i da cewa “Wan nan kuma waye?” yayi tambayar cike da rainin hankali, yana me Ι—age kai sama bayan yajefawa Dr.Sadeeq wani irin kallo..

“Hmm ba buΖ™atar kasan koni Ι—in waye, kai de zaifi kyau kasanardani ko kai waye, amma shishshigi baikamace kaba, saboda bakayi kama da me kula da lafiya ba, kafi kama da masu shiga inda ba’a buΖ™atarsu” Dr.Sadeeq yafaΙ—i haka shima yana me Ι—auke kansa daga kan Zaid.

Murmushi Zaid yayi haΙ—e da kallon Dr.Sadeeq daga sama har Ζ™asa. Kansa kawai ya girgiza “Lallai bana buΖ™atar kowa, kasan yanda zakayi dasu” Zaid yafaΙ—i haka ga Guard Ι—insa, haΙ—e da juyawa yanufi Ι—akin da aka kwantar da Zahrah, lokacinsa bana me aikin duba lafiya bane, lokacinsa muhimmine kuma sai me mahimmanci yake bawa…

Hasala Dr.Sadeeq yayi lokaci Ι—aya yaji zuciyarsa tana masa zafi, yana da sauΖ™i amma watarana abu kaΙ—an ke Ι“ata masa rai, a zuciye ya juya yafice daga cikin asibitin.. Su Inna dake tsaye a harabar asibitin suna ganinsa sukayo kansa da sauri suna tambayarsa ko Zahrah tana lafiya?

STORY CONTINUES BELOW

Kasa amsa musu yayi saima cewa da yayi, su shiga mota su yasauΖ™esu a gida… Bayanda suka iya haka suka shiga cikin motar jiki a sanyaye, saboda sunga gaba Ι—aya fuskar Dr.Sadeeq Ι—in Ι“acin raine shumfuΙ—e akanta, kenan akwai abun dake faruwa.. Da wani irin gudu yaja motar suka fice daga haraban asibitin…

Gyara zama Baffa yayi haΙ—e da kallon Dr.Sadeeq wanda da’alama tunaninsa baya jikinsa.

“Meyake faruwa ne Likita? kashiga kakuma fito da Ι“acin rai, ina Zahrah’n takene me yasameta?” cikin damuwa Baffa yayi tambayar domin shi gaba Ι—aya kansa ya kulle.

Daure zuciyarsa yayi haΙ—e da cewa “Tana nan lafiya, gobe da safe zamu zo mu Ι—auketa”

Ajiyar zuciya Baffa yasauΖ™e me Ζ™arfi yagodewa Allah da ba wani abun bane yasamu Zahrah, to amma ae da anbarsu sun ganta…

A Ζ™ofar gida Dr.Sadeeq ya sauΖ™esu haΙ—e dayi musu saida safe yaja motarsa yayi gaba..

Suna shiga gida Inna ta kalli Baffa haΙ—e da cewa “Anya kuwa Malam bakaganin cewa akwai matsala?”

“Bawai gani nakeba, tabbas ma nasan akwai matsala Salame, sai dai fatana Ι—aya shine Allah yatsare Zahrah, amma tunda Likita yace gobe da safe zamu koma asibitin, saimu jira zuwa goben idan Allah yakaimu”

“To Allah yakaimu” Inna tafaΙ—a jiki a sanyaye… Da “Ameen” kawai Baffa ya amsa.

Kamar yanda Zaid ya kwana a zaune, haka Dr.Sadeeq yakwana juyi, gaba Ι—aya kansa ya kulle, yarasa meke faruwa, baisan waye wannan gayen ba, amma tabbas yaji tsanarsa fiye da misali, amma babban abun tambayar shine me yasamu Zahrah har aka kawota asibiti? sannan kuma meke tsakaninta da wannan mutumin? tambayar dayake buΖ™atar a amsa masa kenan, amma babu wanda zai amsa masa, tambayar da ta kuma hanasa bacci kenan…

Ƙarfe bakwai na safe Zaid yasa aka turo masa nurses guda biyu, suka zo dankula da Zahrah, saboda yana buΖ™atar yaje gida yayi wanka…..

Tamkar amafarki haka fyaΙ—en da yayi mata yasake dawowa cikin idanu da Ζ™waΖ™walwarta, wani irin nishi tayi haΙ—e da sakin Ζ™ara mai sauti, lokaci guda kuma ta ware idanunta da suka cika tab da Ζ™walla, da sauri nurses Ι—in nan sukayo kanta.

Kallon Nurses Ι—in tashiga yi, haΙ—e da soma Ζ™aremawa Ι—akin da take ciki kallo, tabbas idan Ζ™waΖ™walwarta bata juye ba, zata iya cewa nan Ι—akin asibiti ne sannan kuma waΖ΄an nan dake tsaye a gabanta nurses ne.

“Barkanki da tashi, me kike buΖ™ata yanzu a kawomiki?” Ι—aya daga cikin nurses Ι—in nan ta tambayi Zahrah cike da kulawa…

“Idanunta dasuke zubar da ruwan hawaye, ta Ι—aga ta kalli nurse Ι—in haΙ—e da girgiza kanta alamar batason komai.

Hanun nurse Ι—in takamo duka biyu haΙ—e da fashewa da wani irin kuka me ciwo, da’alama wani abu takeson faΙ—awa nurse Ι—in.. Dai dai lokacin aka turo Ζ™ofar Ι—akin aka shigo, Zaid ne yasha adonsa sai zuba Ζ™amshi yake.

Tsayawa yayi cak daga bakin Ζ™ofar sakamakon ganin yanda Zahrah take kuka..

“Me kukayi mata?” yajefawa nurses Ι—in tambaya cikin yanayi na rashin yarda dasu.

“Bamuyi mata komai ba,ranka ya daΙ—e tashinta kenan tasoma rusa kuka” su duka biyu suka haΙ—a baki wajen faΙ—an maganar…

Tamkar wanda aka zuba mata narkakken dalma haka taji sauΖ™an kalamansa acikin kunnuwanta, rumtse jajayen idanunta tayi, ji takeyi tamkar zuciyarta zata faso Ζ™irjinta ta fito.

A hankali Zaid yasoma takawa zuwa gare ta.

“Zahrah” yaΖ™ira sunanta dai dai lokacin daya Ζ™arasa kusa da’ita.. Tunkafun yagama rufe bakinsa yaji sauΖ™an wani irin gigitaccen mari akan Ζ™uncinsa, kafun Ζ™waΖ™walwarsa tagama tantance masa abun dake faruwa, yakumajin sauΖ™ar wani marin aΙ—aya Ι“angaren hagu na kumatunsa..

STORY CONTINUES BELOW

Kasa koda motsawa yayi saima hangame bakinsa da yayi haΙ—e da zaro idanu yana kallonta,, Gaba Ι—aya marukan nan Zahrah ce ta shararawa Zaid akan fuskarsa..

Yanayin yanda idanunta sukayi ja kace barkono ko attarugu aka watsa mata a ciki.

“Kazone ka sake cutar dani? to gani kacutar dani, gani nace ka cutar dani!!” tafaΙ—i haka da wani irin tsawa..

Cikin matsanancin kuka Zahrah tasanya hannayenta duka biyu tashiga dukan sa, tako ina Zahrah ke kai masa duka tana kuka, ganin hanu bazai wadarta ba yasanya ta sanya bakinta, tashiga cizonsa a Ζ™irjinsa, hakama bai mata ba saida ta Ι—auki wani Ζ™arfe dake kusa da’ita tashiga kwaΙ—a masa a jikinsa tana kuka me tsuma zuciya… Haka Zaid ya tsaya tamkar gunki Zahrah na cizo da yaΖ™ushinsa, gakuma dukan da take kai masa, amma yakasa yi mata komai, yakuma kasa koda motsa hanunsa ne.. dai dai lokacin su Dr.Sadeeq suka shigo cikin Ι—akin, turus suma sukayi sakamakon ganin abunda ke faruwa.

“Kasheni zaifi maka sauΖ™i aduniyar nan, akan ace kabarni da raina, natsaneka, dan Allah ka kasheni!!” Abun da Zahrah ke faΙ—a kenan tana kuka. Kowa a wajen tsayawa yayi yana kallon ikon Allah, bakomai ke tashi a Ι—akin ba face kukan Zahrah, tun tana dukansa da’iya Ζ™arfinta har Ζ™arfin nata yasoma Ζ™arewa a hankali ta sulale zuwa Ζ™asa, saboda kuka har shiΙ—ewa take…

“Zahrah” Dr.Sadeeq yaΖ™ira sunanta, cikin wata irin murya.. Jin muryan Dr akunnenta yasa taΙ—ago kanta, tana ganinsa tsaye tatashi a guje haΙ—e da nufar inda yake da sauri tafaΙ—a cikin jikinsa haΙ—i da rungumesa Ζ™a Ζ™am,wani sabon kukan kuma ta sanya, haΙ—e da soma buga kanta akan Ζ™irjinsa..

Duka hannayensa shima yasanya ya rungumeta..

“Wayeshi?” Dr. Sadeeq yayi mata tambayar acikin kunnen ta..

“Shine wanda yaruguzamin rayuwata, shine yarabani da budurcina, shine yayi sanadiyar lalacewar farinciki na!!” Zahrah ta bashi amsa cikin matsanancin kuka, muryarta ko fita batayi da kyau tsabar kuka…

Iya kaΙ—uwa Dr.Sadeeq ya kaΙ—u dajin cewa wai wanda yayiwa Zahrah fyaΙ—e ne tsaye a gabansa, kallon tsana Dr.Sadeeq yashiga yi mawa Zaid..

Zaid kuwa tuni idanunsa sun rune sun zama jajur dasu, jikinsa har rawa yake, koda sau Ι—ayane baiji zafin duka dakuma marin da Zahrah tayi masa ba, babban abun da yayi masa zafi, shine yanda Zahrah taje jikin wani ta lafe. Tun da yake a rayuwarsa baitaΙ“a jin abun da yaji a yau ba… Takowa yashiga yi harzuwa inda suke tsaye ita da Dr.Sadeeq, hanunsa yaΙ—aga domin ya ciro Zahrah daga jikin Dr.Sadeeq. Da sauri Dr.Sadeeq ya tura Zahrah bayansa, haΙ—e da damΖ™e hanun Zaid wanda yakawo daniyar taΙ“a Zahrah..

“Babban kuskuren da zakayi a rayuwarka shine kayarda hanunka yasake taΙ“a jikinta, kayi na farko yakuma isheka, saboda haka ka kiyaye! ” Dr.Sadeeq yafaΙ—i haka cikin matsanancin Ι“acin rai…

Hanun Zahrah yakama haΙ—e da janta suka fice daga cikin Ι—akin, da sauri su Inna ma suka rufa musu baya, saurin dafe saitin zuciyarsa Zaid yayi, wanda yakeji tamkar zatayi tsalle ta fito waje.. Jingina bayansa yayi da bango haΙ—e da lumshe idanunsa.. Zafi yakeji a Ζ™irji dakuma zuciyarsa, take wani irin ciwon kai da zazzaΙ“i me zafi suka sauΖ™ar masa alokaci guda..

Dr.Sadeeq dakansa yasanya Zahrah a mota, wacce har yanzu kuka take, ataΖ™aice dai tsabar kuka numfashinta har Ι—aukewa yake…. Saboda tsabar gudun da Dr.Sadeeq keyi cikin mintuna Ζ™alilan suka isa gida, kowa acikinsu yana cikin tashin hankali. Inna ce takama Zahrah takaita Ι—akinta. Bayan minti kaΙ—an Inna tafito daga Ι—akin Zahrah da sauri. “Likita temaka numfashinta yana shirin Ι—aukewa, taΖ™i daina kukan” Inna tafaΙ—a a ruΙ—e.

Dr.Sadeeq yana shiga Ι—akin yace inna tabasa ruwa, aikuwa mintuna kaΙ—an Inna takawomasa ruwa, cewa yayi Inna taΙ—an basu wuri bamusu Inna tafita a Ι—akin…1

Ι—ago Zahrah Dr.Sadeeq yayi haΙ—e da kai kofin ruwan bakinta, sosai tasha ruwan, take ta soma sauΖ™e ajiyar zuciya, amma still hawaye na gangara akan fuskarta..

Idanunta dasukayi luhu luhu saboda kuka ta Ι—ago dasu takalli Dr.Sadeeq, saikuma tasake fashewa da kuka, haΙ—i da faΙ—awa cikin jikinsa tarungumesa Ζ™am, hanunsa duka biyu yasanya shima ya rungumeta, a hankali ya shiga hura mata kunnen ta, saboda hakan zai sa taΙ—an samu relief, koba komai kukan nata zai tsagaita. Har tsakiyar kansa yakejin kukanta.

Tsawon mintuna 15 yakai yana hura mata kunne, a hankali tasoma rage sautin kukan nata, bayan kamar mintuna 5 yajita shiru, sai sauΖ™ar numfashinta da yake ji akan Ζ™irjinsa akai akai..

Yana duba fuskarta yaga tayi bacci, hawayene yaji suncika masa idanu, tabbas Zahrah taga Ζ™addara a rayuwarta, wani irin tausayinta yakeji me tsanani, tabbas idan ya aureta zai yi iya Ζ™oΖ™arinsa wajen ganin ya mantar da ita duk wani damuwa da tshin hankalin da ta tsinci kanta ciki, zai kuma yi iyaka Ζ™oΖ™arinsa wajen ganin yabata farinciki me Ι—orewa.

A hankali ya kwantar da’ita, haΙ—e da sanya hanu ya gyara mata dogon gashinta da ya rufe mata fuska. Yajima yana kallonta kafun daga bisani ya tashi yafita daga cikin Ι—akin…

Zaune yasamu Baffa da Inna a tsakar gidan sunyi jigum. Yana fita suka tsaresa da ido da’alama bakinsu Ι—auke yake da tarin tambayoyi..

Ajiyar zuciya ya yi haΙ—e da cewa “Tasamu bacci, kada ayi wani abu da zai tasheta, ni zan wuce office anjima zandawo”

Har bakin motarsa Baffa yarakasa bayan sun tattauna wata magana me mahimmanci….

Zaid ne zaune a cikin falon sa dake guest hause Ι—insa, kallo Ι—aya zakai masa kafahimci cewa yana cikin tashin hankali, kwalaben giyane zube a gabansa, guda uku daga cikin kwalaben duk ya shanye giyan dake a

cikinsu, ba abun dake gigita masa tunani da Ζ™waΖ™walwa kamar yanda Zahrah ta nunamasa tsana a fili Ζ™arara, kallonsa yakai ga hanunsa na dama wanda yake fidda jini, bakomai yajawo hakan ba face Ζ™arfen da Zahrah ta kwaΙ—a masa akan hanun,, runtse idanunsa dasuka kaΙ—a sukai jajur yayi, haΙ—e da cije laΙ“Ι“ansa, wani irin zafi yakeji acikin zuciyarsa a duk sanda idanunsa suka hasko masa lokacin da Zahrah taje ta faΙ—a Ζ™irjin Dr.Sadeeq, jiyake kamar ya kurma ihu, ko zai samu salama acikin zuciyarsa…. Ahankali yamiΖ™e tsaye haΙ—e da nufar Ι—akinsa, Da Ζ™yar yake iya tafiya, saboda abuge yake mankas, kai tsaye Ι—an Ζ™aramin drowern dake kusa da gadonsa yanufa, wani tablet yaΙ—auko haΙ—e da Ι“arewa kusan guda takwas ya watsa a bakinsa, haΙ—i da korawa da ruwan swan… FaΙ—awa kan gado yayi yana me rumtse idanunsa, “Natsaneka” shine kalmar da tafi Ι—aga masa hankali aduk cikin kalaman da Zahrah ta faΙ—a masa. itace kuma kalmar da takeyi masa yawo acikin kansa, cikin wani irin yanayi Zaid yatashi tsaye haΙ—e da nufar wajen da yake aje kayan shafansa, watsi yashigayi da duk wani abu dake kan dressing mirror Ι—in nasa, lokaci Ι—aya yayi buji buji da Ι—akinsa, yayinda ya fasa gaba Ι—aya kwalaben turarensa, har sai da wasu kwalaben suka yankesa a hanu da Ζ™afarsa, amma don tsabar baΖ™in kishi ko zafi baiji ba, idanunsa Zahrah kawai suke hangomasa kwance a Ζ™irjin Dr.Sadeeq. Lokaci Ι—aya yaji wani irin juwa ta Ι—ebesa, harsai da yariΖ™e bango, a daddafe yaΖ™a risa kan gadonsa ya kwanta, ji yayi kansa yasoma juyawa, yayinda idanunsa suka soma rufewa, yasoma ganin komai bibbiyu, cikin mintuna Ζ™alilan idanunsa suka rufe ruf…..Ba’itace ta farka ba sai wajen Ζ™arfe Ι—aya na rana..+

A hankali take ware manya manyan idanunta da suka kaΙ—a suka zama jajur dasu, ba tun yanzu ta farka ba, kawai dai Allah ne be bata daman buΙ—e idanun nata ba sai yanzu. Tun farkawarta kuwa take cikin tsanani da kuma mamakin mutum mai taurin zuciya irin Zaid, lallai shiΙ—in yacika Ι—an iska kuma shu’umi, duk da irin girman laifin da ya aika ta mata, hakan baisanya yaji Ι—ar ko kuma shakkan tunkarar ta ba, lallai shiΙ—in acikin Ζ΄an iska ma daban yake,, haka nan taji gaba Ι—aya zuciyarta ta Ζ™eΖ™ashe takuma bushe, lallai tunda ya nuna mata shiΙ—in babban Ι—an iska ne yakamata ace itama ta nuna masa iyakar iskancinsa, tunda har baiji kunyar tako Ζ™afa yazo gareta ba, to tabbas itama yakamata tacire kunya, wajen ganin ta koya masa hankali… Sai dai kuma kome zatayi bazata huce ba, saboda iyaka kuma maΖ™urar cuta Zaid yayi mata, ya mata illa dakuma tabon da bazata taΙ“a mantawa ba, harta koma ga mahaliccinta kuwa, Zaid ne ya surka mata farincikinta da wani irin mummunan baΖ™in duhu, ya katse mata jin daΙ—i da kuma walwalanta, ya lalata mata rayuwa a rana Ι—aya, ya ruguza duk wani buri da fatanta, ya gwada mata Ζ™arfi ya amshi budurcinta cikin yanayi na tozarci, me yafi wan nan ciwo a rayuwar Ζ΄a mace? tasan Ζ™iyayya amma kuma zafin Ζ™iyayyar da takeyi mawa Zaid na daban ne, tabbas idan da kisan kai yana da kyau a addinance to haΖ™iΖ™a ba abun da zai hanata kashe Zaid san nan kuma itama ta kashe kanta, saboda Ζ™uncin da ya mamaye zuciyarta ba’irin Ζ™uncin nan bane da yake fita, lallai Ζ™uncin zuciyarta dawwa memme ne, sai dai kawai ta roΖ™i Allah daya sassauta mata…..

Hawayen da suka fito daga cikin idanunta suka gangaro ta gefen kumatunta ta sanya hanu ta share haΙ—e da miΖ™ewa zaune, babu amfanin Ι“ata hawayenta wajen fiddasu, yanzu lokaci yayi da shine yakamata yayi kuka ba ita ba. Kayan jikinta tashiga cirewa, haΙ—e da Ι—aura zani akan Ζ™irjinta kana ta sanya lufaya….

Tana fitowa daga cikin Ι—akin nata, Inna ta kalleta haΙ—e da cewa.

“Yauwa Zahrah kintashi ko? ya Ζ™arfin jikin naki de?” alokaci Ι—aya Inna tajero mata duka waΖ΄an nan tambayoyin..

“Eh Inna na tashi, ko zan samu ruwan zafi inaso nayi wanka ne, gaba Ι—aya banajin daΙ—in jikina, gashi ina so naje gidan su Husnah” tafaΙ—i maganar tana me Ι—an rumtse idanun ta, saboda wani juwa da taji yana Ζ™oΖ™arin Ι—ibanta..

“Kinkuwa ci sa’a yanzu na Ι—aura ruwan abincin rana, gashi can inaga yama tafasa saiki Ι—iba, amma idan kin Ι—iba ki Ζ™aramin ruwa acikin tukunyar” Inna tafaΙ—i haka tana meyi mata nuni da tukunyar abincin dake Ι—aure kan murhu…

Sosai taji daΙ—in jikinta sakamakon wanka da ruwan zafi da tayi, bayan ta idar da Sallan Azahar ne, tayi mawa kanta mazauni akan katifarta haΙ—e da Ι—aukan jakar kayan kwalliyanta, mai kawai tashafa sai kwalli da ta zizara a cikin idanunta, ko powder bata shafa ba…

Doguwar rigar atamfa irin me sauΖ™in kuΙ—in nan tasanya ajikinta, haΙ—ih da Ι—aura hijab akan kayan nata mai kalar blue, yakumayi shige da atamfarta saboda shima atamfar kalan blue ne dashi (shuΙ—i). Me kyau de me kyaune ko a yaya kuwa, duk da batayi kwalliya ba kuma fuskarta a kumbure take saboda kuka, amma hakan bai hana kyawun fuskarta bayyana ba….

STORY CONTINUES BELOW

Kallon Inna dake Ζ™oΖ™arin sauΖ™e tukunyar abinci Zahrah tayi, tana me gyara zaman lufayar jikinta tace.

“Inna ni zan je gidansu Husnah, zuwa yamma zandawo insha Allah”

“Wani irin maganar zuwa gidansu Husnah kuma Zahrah? inace Ι—azu Ι—azun nan muka dawo dake daga asibiti, har kin yi sauΖ™in da zaki soma fita yawo?”

(Su Inna anfara soyayya da Zahrah fans, lol)

“Kada ki damu Inna yazama dole ne naje, amma bazan jima ba zandawo, dan Allah kada ki hanani zuwa Inna!” Zahrah ta faΙ—i haka cikin yanayi na nuna zaΖ™uwa.

“Shikenan tunda kin matsa, ai de kya tsaya kici abinci, idan yaso saiki tafi”

“A’a Inna banajin yunwa yanzu, idan nadawo zanci” takai Ζ™arshen zancen nata tana me nufar hanyar fita daga cikin gidan. Da kallo kawai Inna tabita harta fice daga gidan…

Tsayawa tayi tana kallonsa cike da mamaki, yayinda shima kallon nata yake cikin yanayi na mamaki…

Giransa Ι—aya ya Ι—age haΙ—e dayin murmushi…. “Ashe ma kinyi sauΖ™i, dana sani da ban bar aikin da nakeyi nazo duba kiba ae” Dr.Sadeeq yafaΙ—i haka yana me takowa zuwa wajen da take tsaye.

Kunyarsa ne taji yakamata, sakamakon abun da yafaru Ι—azu a tsakaninsu, wato rungumarsa da tayi, wanda tasan hakan ba abu bane me kyau haramunne, mace ko namiji su taΙ“a mutumin da ba muharrami’n su ba, duk da cewa ba’acikin hayyacin ta ta rungumeshi ba, amma tabbas hakan bai dace ba…

“Yade naga kina wani sunkuyar dakai kamar amaryar da aka kaita Ι—akin mijinta” Dr.Sadeeq Ζ΄afaΙ—i haka cike da zolaya.

Sai alokacin ta’iya Ι—ago kanta ta aika masa da

hararan wasa,,,,, ” Yaushe kazo? kuma me yasa ka tsaya anan baka shiga cikin gida ba?”

“Ummm banjima da zuwa ba, dama inaso amin sallama dake ne, kinga bai dace ace koda yaushe ina shiga cikin gidanku kai tsaye ba, amma sai kuma naga kamar keΙ—in sauri kike zaki unguwa ko?”

YaΖ™are maganar yana me leΖ™a fuskarta wanda ta sunkuyar da ita Ζ™asa.

Wasa da yatsun hanunta tashiga yi, haΙ—e da sanya haΖ™orinta na sama taΙ—an datse leΙ“enta na Ζ™asa..

“Yajikin naki?” yatambayeta don yaga bata daniyar basa amsan abun da yatambaya.

“DasauΖ™i, dama ni lafiyata Ζ™alau” tabasa amsa a ta Ζ™aice..

“Eh hakane kuma dama kinsan wani lokacin, idan lafiya tayi mawa mutum yawa, takan iya sawa ya kwanta a gadon asibiti”

Saurin kallonsa tayi sakamakon jin abun da yace, “Lafiyan?” ta tambaya cike da mamaki.

“Eh itafa lafiyan, to baga example akan ki ba” yanayin yanda yayi maganar kaΙ—ai ya’isa ya tabbatar maka cewa zolaya ne kawai ke damunsa..

“Hmm” kawai Zahrah tace haΙ—i da Ι—an satan kallonsa, aikuwa karab suka haΙ—a idanu, saurin Ι—auke nata idon tayi.

Hmm yalura sarai kunyarsa takeji, kuma shiΙ—in ma kusan hakanne, kawai de dauriya dakuma shariya yafita, shiyasa ya share abun, amma shikansa yasan cewa ya aikata ba dai dai ba, saboda da ta rungumesa baikamata ace yabiye mata ba, kamata yayi ace ya Ι“anΙ“areta daga jikinsa, sai de kuma babu yanda ya’iya saboda alokacin tana cikin halin buΖ™atar taimako, kum san nan shi be rungumeta don yaji daΙ—i ba.

“Inazakije ne haka, da rana tsaka?” yajefo mata tambaya…..

“Gidan su Husnah zani” ta basa amsa a taΖ™aice, saboda ba da kowani lokaci tacika son dogon magana ba…

“Shikenan muje saina kaiki, domin kinsan samun abun hawa zaimiki wahala, saboda rana tayi sosai”

Kallonsa tayi naΙ—an sakanni, kafun ta rausayar da kanta gefe cikin yanayi na shagwaΙ“a tace “Dama kabarni, koda Ζ™afana ai zan iya zuwa, idan har bansamu abun hawa ba, balle ma nasan zan samu”

STORY CONTINUES BELOW

“Da gaske zaki iya takawa da Ζ™afa daga nan har gidansu Husnah? to shikenan tunda zaki iya, zaimafi kyau ki taka da Ζ™afan, saboda kisamu ki Ι—an rage wan nan Ζ™iban dakika haΙ—a, gaba Ι—aya duk yasa kin yi muni, kin zama wata super mama dake” yafaΙ—i haka yana me Ζ™are mata kallo.

Waro idanu Zahrah tayi haΙ—i da soma kallon kanta, wai tayi Ζ™iba, takuma zama super mama.

Take idanunta suka yi raurau dasu, yayinda ruwan hawaye ya soma cika cikin su, “ashe da gaske tayi Ζ™iba bata sani ba? gashi harya fara goranta mata, to me yasa ita bataganin Ζ™ibanta?” tatambayi kanta…

Dariya Dr.Sadeeq yasanya domin kuwa yalura tayarda da maganarsa, shikuwa wasa yake mata, bawai dagaske tayi Ζ™iban bane, gashi har tana Ζ™oΖ™arin yin kuka, shikam ya lura gaba Ι—aya kuka baya bata wahalar yi, hawayenta a maΖ™ale suke, mintuna kaΙ—an saikaga sun tsiyayo”

“Kintsorata ne dan nace kinyi Ζ™iba? hmmm nan gaba kaΙ—an zakiyi bindiga ki fashe saboda tsabar Ζ™iba”

Sake waro manya manyan idanunta tayi zuwa yanzu kam har Ζ™wallan cikin idanunta sun gangaro akan fuskarta….

“Au kinfiso ki kumbura ki fashe Ι—in kenan?” yatambayeta yana me danne dariyar da ta taso masa…

Kai ta girgiza masa alaman “A’a”

“To kinaso na faΙ—amiki me zakiyi wanda zaisa bazaki fashe ba?”

Dasauri ta Ζ™aΙ—a kai alamar tanaso yafaΙ—a mata…

“Yauwa Ζ΄ar gari ashe de kema bakyaso ki fashe, to abu Ι—aya zakiyi wanda shizai hanaki fashewa, kinga de ni likita ne ko? nakumayi zurfi cikin karatun likitanci, saboda tsabar zurfin da nayi ina karatune ma yasanya nagano cewa idan mutum yacika matsantawa kansa da damuwa da kuma yawan koke koke to yakan iya kumbura kamar de yanda kikayi yanzu, daga nan kuma bayan kamar 1 week shikenan sai dai yayi bindiga yafashe fush, shikenan kuma sai de wani bashi ba, kinaso haka ta faru dake?” yafaΙ—i haka yana me zura mata manya manyan idanunsa.

“A’a” tabashi amsa cikin murya me sanyi, domin kuwa a haΖ™iΖ™anin gaskiya ta yarda da kalamansa, ko kaΙ—an bata gano cewa shiya shirya abunsa ba. take fargaba ya Ι—arsu a zuciyarta….

Wata irin dariyane takama Dr.Sadeeq amma kuma ba halin yasaki dariyar tasa, dolensa ya danne ta matuΖ™ar yanaso Zahrah ta gamsu da bayanan sa hundred percent,,, lallai yau yaΖ™ara tabbatarwa kansa cewa Zahrah yarinyace kuma yarinta na damunta, amma inbanda haka ta’ina ta taΙ“a jin ance mutum ya yayi bindiga yakuma fashe da ransa.

Gyara tsayuwarsa yayi haΙ—e da cewa “To yanzu de zaΙ“i ya rage gareki Yarinya, ko ki daina kuka ko kuma ki fashe, saboda haka zaki biyoni muje ne ko kuwa a’a nayi tafiyata?”

“Zanbika” tafaΙ—a cikin muryar tsoro saboda gaba Ι—aya kalaman likita sun rikitata…

Murmushin gefen baki Dr.Sadeeq yayi haΙ—e da juyawa yanufi wajen motarsa, yana me danne dariyarsa…

Zahrah kuwa tamkar wacce Ζ™wai yafashewa haka ta bi bayansa.

Saida suka hau titi kafun yajuyo da kallonsa gareta, gani yayi tayi jigum da’ita, da’alama tunani takeyi….

“Amma nace miki yawan sakai a damuwa shike sa mutum ya fashe ko? hala don ba Ι“angaren likitanci kike karanta ba shiyasa bakisan da hakan ba”

Kallonsa tayi haΙ—e da Ζ™waΙ“e fuska, cikin murya me sanyi tace “Ni ae yanzu bawai a damuwa nake ba, kawai de ina kallon hanya ne” ….

Kansa ya jinjina haΙ—e da cewa tayi masa kwatancen gidansu Husnah’n domin shi basani yayi ba….

A dai dai Ζ™ofar gidan su Husnah ya tsaida motar tasa, haΙ—e da dawo da kallonsa ga Zahrah wacce ke Ζ™oΖ™arin buΙ—e murfin motar tayi ficewarta…

“Da yaushe zaki koma gida?”

STORY CONTINUES BELOW

Ɗan jim tayi kana tace “Ko zuwa bayan la’asar ma, irin Ζ™arfe biyar Ι—in nan haka” yanayin yanda taΖ™ai Ζ™arshen zancen nata tana me juya kyawawan idanunta, shi ya shagaltar dashi har ya tsaida idanunsa akan ta, sosai takeyi masa kyau idan tana juya idanunta, ya kuma lura cewa hakan al’adarta ne, idan hartana magana, to takan juya idanunta masu kyawun gani, musamman idan maganar tazo Ζ™arshe..

“Ya de?” Zahrah ta tambayeshi sakamakon ganin da tayi yakafeta da idanunsa..

“Babu, kikulamin da kanki kinji, zan zo na Ι—aukeki idan 5 Ι—in tayi, inafata babu wata matsala?” yatambayeta cike da nuna kulawa.

Murmushinta me kyau tayi masa haΙ—e da cewa

“Babu wata matsala”

Yana kallonta tabuΙ—e Ζ™aramar Ζ™ofar dake jikin gate Ι—in gidan su Husnah tashige… Yana tabbatar da shigewarta yayiwa motarsa key haΙ—e dayin reverse yaΙ—auki hanyar asibitinsu, saboda dama aiki yabaro yazo gareta, to yazaiyi tunda tazama wani Ι“angare na jikinsa…

Da matuΖ™ar farinciki Husnah ta rungume Zahrah tana mejin daΙ—in ziyarar bazata da Zahrah’n takawo mata, saboda bata faΙ—a mata zata zoba. Bayan Zahrah ta gaisa da Momyn Husnah ne, suka rankaya zuwa Ι—akin Husna’n,,, ba Ι“ata lokaci Husnah ta cikawa Zahrah gabanta da kayan ciye ciye dasu drinks.

“Naji daΙ—in zuwanki sosai Ζ™awata, kamar kuwa kinsan ina kewarki, jiyafa har mafarkin ki nayi, da safe naΖ™ira wayarki kuma najita switch off, ina fata dai kina lafiya?”

Hijabin dake jikinta ta cire haΙ—e da cewa “Lafiya amma ba sosai ba”

Da sauri Husnah ta dawo da kallonta ga Zahrah

“Meyafaru dear?” Husnah tatambaya cike da kulawa.

Kallon Husnah Zahrah tayi na tsawon minti guda….

“BabuΖ™atar tuna abun da yafaru Husnah, saboda kinsan inada raunin zuciya, tuna abun zai iya sake jefani cikin wani hali”

Damuwane ya bayyana Ζ™arara akan fuskar Husnah haΖ™iΖ™a tamkar Ζ΄ar uwa ta jini take kallon Zahrah saboda haka duk wata damuwa ta Zahrah damuwar tace itama.

“Zaki iya Ι“oyewa kowa damuwarki amma bandani Zahrah, sai de kuma babu amfanin takuraki akan cewa lallai sai kin sanar dani, saboda bansan wani hali zaki samu kanki aciki ba bayan kin faΙ—amin”

Dafa kaΙ—an Husnah Zahrah tayi haΙ—i da daure zuciyarta…

“Nasake haΙ—uwa da…. da….wanda ya yimin fya…….” kasa Ζ™arasawa tayi saikawai tafashe da kuka.

Ko bata Ζ™arasaba Husnah tafahimci me Zahrah take nufi.

Cike da tashin hankali Husnah tasoma salati…

Sake jawo Zahrah jikinta tayi haΙ—i da rungumeta….”Ki daina kuka, yanzu ba lokacin kuka bane Zahrah, kinmaci abinci kuwa ?” Husnah ta tambayi Zahrah cikin kulawa…

“Banajin yunwa Husnah!” Zahrah tafaΙ—i haka cikin shaΖ™ewar murya, wani yunwa zataji ita da take cikin bala’in sake ganin Zaid…

“Kinsan de ba kyau zama da yunwa ko, kinga yau ni namayi abincin dakaina, bana zuba mana muci tare, kuma dan Allah kada kicemin a’a”

Babu yanda Zahrah ta’iya dole tabiyewa Husnah taci abinci, gaba Ι—aya Husnah se zuba take tamkar kurna, takasa yin shiru koda na minti biyu ne, tayi hakanne kuma saboda ta gusarwa da Zahrah da muwarta, daga Ζ™arshe de har game, Husnah ta jona musu a tv suka buga, sosai kuma hakan ya Ι—ebewa Zahrah kewa….

Tare sukayi sallan la’asar daga nan kuma Husnah ta Ι—ebi Zahrah, suka tafi shoprite, dangin su ice cream da chocolate suka jida, daga nan sukayo gida.

Kamar yanda yafaΙ—a Ζ™arfe biyar da minti Ι—aya dai dai ya Ζ™araso Ζ™ofar gidansu Husnah.. Ƙiran Zahrah yayi a waya ya tabbatar mata cewa yana Ζ™ofar gidan su Husnah….

STORY CONTINUES BELOW

Zahrah na ajiye wayarta Husnah ta kalleta haΙ—e da kashe mata ido Ι—aya.

“Ƙawata tazama Ζ΄ar soyayya, sosai yanayin soyayyarku da Man Ι—in nan yake kasheni, kinfasan gayen naki ya haΙ—u over, da badan ke bace danayi snatching Ι—in sa!” cike da zolaya Husnah ta faΙ—i maganar…

Dariya suka sanya su dukansu, haΙ—e da rungume juna.

Har bakin motar Dr.Sadeeq Husnah ta raka Zahrah, bayan Momyn Husnah ta cikawa Zahrah leda da dangin su turare dakuma kayan shafa hadda kyautar wani haΙ—aΙ—Ι—en leshi, sosai Zahrah tayi godia, hakan kuma yana Ι—aya daga cikin abubuwan daya sanya bata son zuwa gidansu Husnah, saboda idan dai tazo tofa sai mahaifiyar Husnah tayi Ι—awainiya da’ita wajen bata kyautan kayayyaki masu kyau da tsada…

Harsaida Husnah taga tashin motar su Zahrah kafun takoma cikin gida…

“Kinsamo abun daΙ—i shine kokimin tayi ko?” Dr.Sadeeq yafaΙ—i haka ga Zahrah wacce ta Ι—aura ledan sayayyar da sukayi a shoprite ita da Husnah akan cinyarta…

“Murmushi me sauti tayi haΙ—e da cewa “Ba’abun daΙ—i bane, kayan shafa ne”

“Um um ni banyarda ba, kitaimaka kiban ko chocolate Ι—aya ne, naci yunwa nakeji, yau duk banci abinci ba” yaΖ™are maganar yana me shagwaΙ“e fuska, sai kace wani Ζ™aramin yaro…

Dariya Zahrah tayi haΙ—e da satar kallonsa “wai ma ya’akayi yasan cewa acikin ledar hanunta akwai chocolate?” ta tambayi kanta.

“Kina mamakin ya’akayi nasan cewa a ledarki akwai chocolate ko?, ai ba abun mamaki bane, tunda nasan shiΙ—in favorite Ι—in ki ne” yafaΙ—i haka cikin yanayin shauΖ™i, amma still idanunsa naga titi..

BuΙ—e ledar tayi taciro wani chocolate mai kyau da daΙ—i kusan yafi kowanne ma daΙ—i acikin sauran chocolate Ι—in da ta saya, ta miΖ™a masa haΙ—i da cewa “Ga wan nan amma bazan iya baka kyautarsa duka ba, saboda haka kaci rabi kabarmin rabi”

Saurin kallonta yayi fuskar sa Ι—auke da murmushi… ” NaΖ™i wayon, idan har kinaso na karΙ“a saide kibani kyautansa duka”

Turo Ι—an Ζ™aramin bakinta tayi gaba, haΙ—e da noΖ™e kai alamar hakan bazai yiwuba, kallon bakin nata yayi, harsai da yaji tsikar jikinsa Ζ΄a zuba, hmmm lallai idan ya auri Zahrah, zai tsotse wan nan Ι—an Ζ™aramin bakin nata ne yanda ya kamata?…

“Kici chocolate Ι—inki ke kaΙ—ai nikam na gode” yafaΙ—i haka a taΖ™aice domin dama wasa yake mata baci zaiyi ba, shi da yake fama da ciwon ciki idan yaci chocolate kuma yake nan?

Lokacin da suka iso gida biyar da rabi har ta gota… kallon Zahrah Dr.Sadeeq yayi haΙ—e da Ι—an nisawa.

“Nagama haΙ—a miki kayan lefe da kuma sauran abun da suka dace, wace rana kikeso a kawo?”

Saurin Ι—aga idanu tayi ta kallesa jin abun da yace.

Idanunsa Ι—aya ya kashe mata, wanda yasanya taji gabanta yafaΙ—i, saboda a wajen mutum Ι—aya ta saba ganin irin wan nan kashe idon, kuma shi hakan yazame masa al’adarsa ne, bakowa bane kuma face ZAID.

“Zamuyi waya” Zahrah tafaΙ—i haka don son kawar da tambayar tasa, saboda a yanzu bata da amsar da zata basa..

Ajiyar zuciya ya sauΖ™e haΙ—e da dafa steering motar da duka hannayensa biyu. “Shikenan idan kin nutsu zan Ζ™iraki” yafaΙ—i haka cikin sanyin murya..

Murmushi tayi masa irin me tsayawa a rai Ι—in nan, kana tabuΙ—e murfin motar tayi ficewarta, sai de batare da yasani ba, ta aje masa wan nan chocolate Ι—in…

Bayan kamar 2 minute da shiganta cikin gida yaja motarsa shima yayi tafiyarsa…

*ZAID*

Tunda yasha wan nan Ζ™wayoyin baisan inda kansa yake ba harsai Ζ™arfe uku na yammaci,, ko da ya buΙ—e idanunsa ji yayi duniyar na juya masa, amma haka adaddafe ya shiga bathroom yayi wanka haΙ—e da Ι—auro alwala, sai yanzu zaiyi sallan Azahar don tsabar asara, gashi har la’asar ma takawo kai….

Yana idar da sallan azahar ya miΖ™e daga kan sallaya haΙ—e da zura slipper Ι—insa yafice daga Ι—akin… Kai tsaye masallacin jikin gidansu yanufa don gudanar da sallan la’asar wanda ake Ζ™ira yanzu.. Ko a cikin masallacin mutane sai mamakin ganinsa suke saboda abune mawuyaci ka gansa a masallacin da wan nan time Ι—in, yafi yawan zuwa sallan isha ko asuba, amma banda azahar da la’asar saboda a wan nan lokacin ma kwata kwata baya gida, sai de yayi sallah a wani wajen. Baidamu da kallon da mutane suke masa ba, yana idar da sallan sa yatashi yayi shigewarsa cikin gida…

Tsab yagama shirya kansa cikin Ζ™ananan kaya, riga da wando na blue jeans wanda suka matuΖ™ar amsar jikinsa. Ba abun da yake sai tashin Ζ™amshi.

Zama yayi abakin gadonsa haΙ—e da sanya hanunsa duka biyu ya dafe kansa dake yi masa ciwo kaΙ—an kaΙ—an,, wani irin sabon al’amari yakeji a cikin zuciyarsa, baisan da wani suna ze Ζ™ira abun ba, amma tabbas jiyake zuciyarsa na azalzalarsa akan Zahrah, san nan yanajin cewa itace muradinsa, saurin buΙ—e idanunsa da ke lumshe yayi sakamakon hasko masa marukan da Zahrah ta sharara masa akan fuskarsa da sukayi, hanunsa yakai kan Ζ™uncinsa ya shafa haΙ—e da sakin murmushi, tunda yake a a rayuwarsa wata mace banda mahaifiyarsa bata taΙ“a kai hanunta jikinsa da sunan duka ba ballan tana har akai ga mari, sai gashi yau, Zahrah ta shararamasa lafiyayyun maruka harguda biyu akan fuskarsa, takuma haΙ—a masa hadda duka, amma ko kaΙ—an baiji zafin abun ba, anya kuwa shine? kodai an musanyashine bai sani ba? meke damun Ζ™waΖ™walwa da zuciyarsa ne? shine Zaid kuwa? Yajerowa kansa waΖ΄an nan tambayoyin….

Post a Comment for "SHU'UMIN NAMIJI CHAPTER 7 BY FATYMA SARDAUNA"