SHU'UMIN NAMIJI CHAPTER 7 BY FATYMA SARDAUNA SHU’UMIN NAMIJI CHAPTER 8 BY FATYMA SARDAUNA Www.bankinhausanovels.com.ng Idanu ta ƙara zarowa domin tabbatar mawa kanta cewa abun da tagani gaskiya ne, ko kuwa, gizo idanunta keyi mata. Tabbas dagaske ne bawai gizo bane, hoton zanen fuskarta ne raɗau ajikin takardan. Hanunta na rawa haka ta durƙusa ƙasa, haɗe da sanya hanu ta sake ware takardan, tabbas itaɗince babu ko kokonto, zanen fuskarta ce kwance ajikin takardan, amma saboda tsananin kyawun da zanen yayi tamkar azahiri haka zaka gani, hanu tasanya ta shafi zanen, cike da fargaba haɗe da ɗaurewar kai. Lallai yazama dole a gareta tanemo wanda yake aikata mata waƴan nan abubuwan, kusan kwana uku yanzu kenan ana turo mata da saƙonni, bata kuma san daga waye bane. Bata damu da ta duba sauran kayan dake cikin kwalin ba, ta tattara shi ta ɓoye acikin kayanta. Zama tayi dirshan akan katifa tana mai da numfashi akai akai, sosai abun yabata mamaki, tabbas ko ma waye ne wanda yake bibiyarta ta tabbata yayi mata farin sani,…