SHU'UMIN NAMIJI CHAPTER 14 KARSHE BY FATYMA SARDAUNA
SHU’UMIN NAMIJI CHAPTER 14 KARSHE BY FATYMA SARDAUNA
Www.bankinhausanovels.com.ng
Two years Later!+
Acikin shekaru biyunnan da suka wuce abubuwa da yawa sun faru, ciki kuwa hadda haihuwan Husnah, da kuma Ζarin girman da akayiwa Doctor Sadeeq a wajen aiki, Zahrah kuwa tazama lecturer acikin jami’ar da tayi karatu. Abubuwa dayawa sun faru acikin waΖ΄annan shekarun.
Tsaye take agaban wani babban table tana haΙa wasu takardu dake gabanta, ajikinta sanye take da Abaya gown, maroon colour, wanda jikinsa yaji adon duwatsu da kuma flowers masu kyau, yayinda Abaya Vail Ιin dake yafe saman kanta, ya sauΖo har zuwa Ζirjinta, babu wani kwalliya akan fuskarta, lipstick ne kawai sai kuma kwallin data sanya acikin Ιara Ιaran idanunta, sosai taΖara kyau, cika da kuma wayewa, duk da cewa a Ζ΄an shekaru biyun da suka wuce itaΙin ba baya bace wajen kyau, amma ayanzu komai nata yaΖara ninkuwa akan nada, yanzu tana amsa sunanta na cikakkiyar mace. Kallonta ta maida kan agogon dake Ιaure akan tsintsiyar hanunta. “4:30 pm” ta faΙa tana Ιan waro idanunta, da sauri tacigaba da tattare takardun, wasu tasa acikin jakarta, wasu kuwa ta sanyasu acikin wata drawer dake cikin office Ιin. Wayarta da jakarta ta Ιauka, kana ta nufi hanyar fita daga office Ιin.
STORY CONTINUES BELOW
Motarta Ζiran Corolla LE tashiga haΙe da bata wuta, ta fice acikin jami’an.. Bata wani jima sosaiba ta isa sabon gidansu wanda suka koma babu jimawa.
Da sallama Ιauke abakinta ta kutsa kanta cikin falon, babu kowa afalon, sai TV Plasma Ιinsu dake ta aiki shikaΙai. Direct wani Ιaki dake cikin falon ta nufa, tsayawa tayi ajikin Ζofar Ιakin tana sakin murmushi, idanunta nakan wani yaro da shekarunsa na duniya bazasu wuce uku ba, ya nata Ζiriniyansa shi kaΙai, yaron kyakkyawane sosai, gashin kansa kuwa kamar na larabawa. Cikin sanΙa tashiga takawa harta Ζarasa wajen dayake zaune, murya a hankali tace.
“Babyy!” Jin muryar mahaifiyarsa acikin kunnuwansa yasashi juyowa da sauri, yana ganinta, ya tafi ya faΙa jikinta, yana dariya, itama dariyan tayi haΙe da manna masa kiss akan bakinsa, cike da kulawa haΙi da Ζaunarsa.
“Aunty Sannu da dawowa” cewar Haulat me yi mata rainon yaron, idan zata aiki.
“Yauwa Haulat sannu da gida” Zahrah ta amsa mata fuska a sake.
Ζaukan yaronnata tayi suka fice daga Ιakin, direct sama ta haura inda anan bedroom Ιinta yake.
Aje yaron nata tayi akan gado haΙe da durΖusawa agabansa, chocolate irin marar zaΖi sosai Ιinnan ta ciro ajakarta, kana ta Ιare ta basa a hanunsa, da murna Asad ya karΙi Chocolate Ιin, matso da fuskarsa yayi daf da tata, kiss yayi mata akan kumatunta haΙe da cewa “Thank you Mummy!” yayi maganar ne cikin muryarsa dake Ιauke da tsananin yarinta.
Murmushi tayi kana taΙanja kumatunsa, miΖewa tayi ta wuce cikin bathroom acan ta cire kayan jikinta haΙe da sakarwa kanta shower.
Koda ta fito sama sama ta shafa mai domin yanayin garin ana Ιan busa zafi, wani dogon skin tight baΖi ta sanya, wanda yayi matuΖar bayyana surar jikinta, bama kamar hips Ιinta da suka sake cika, wata riga mai net tasanya, irin fitted Ιinnan, sosai rigan tayi mata kyau, Ζirjinta ne kawai yazamana a rufe, amma gaba Ιaya jikinta daga cikinta zuwa bayanta a bayyane suke, haka tsarin rigar yake.
Da Body Spray Ιinta me daΙin Ζamshi ta feshi jikinta, dogon gashinta dayasha kitson kalaba, ta kama ta Ιaureshi da ribbon, direct gaban Ιan madaidaicin fridge Ιin dake Ιakin ta nufa, buΙewa tayi ta Ιauko goran Yoghurt, buΙe murfin goran tayi tasoma sha ahankali.
Shigowarsa Ιakin kenan, amma kuma kokaΙan bataji motsin buΙe Ζofarsa ba, yana sanye da riga da wando na Suit navy blue colour masu kyaun gaske, tabbas ya sauya daga kamanninsa nada, yaΖara haske da kyau, ga lallausan sajensa da ya kwanta luf akan fuskarsa, yazama wani na musamman dashi, me tafiya da hankalin Ζ΄an mata, yaΖara zama Handsome, dagani kai kasan kuΙi sun zauna masa..
Dariyan Asad da taji ne yasata waigowa ta kalli yaron, atunaninta ko Ιarna yakeyi mata, gani tayi idanunsa nakan Ζofar shigowa Ιakin, saboda haka itama ta maida idanunta wajen, da taga Asad Ιin na kallo.
Idanunsu ne suka sarΖe a cikin na juna, wani irin murmushine ya Ζwace mata, haΙe da lumshe idanunta, ta kuma buΙesu alokaci guda, shima murmushin yayi mata, kana ya buΙe duka hannayensa, alaman ta taho garesa, babu musu ta Ζarasa garesa, haΙe da faΙawa cikin jikinsa, atare suka rungume juna, tare da sauΖe ajiyar zuciya.
Hanunsa yasanya yashiga shafa bayanta, haΙe da soma hura mata iskan bakinsa, cikin kunnenta. Luf tayi acikin Ζirjinsa, tana mai jin daΙin abun da yakeyi mata, idan har tanajin iskan bakinsa acikin kunnenta, sosai take samun nutsuwa acikin ruhinta.
Sun kusan mintuna 10 a haka kafun tace dashi cikin sanyin murya. “Sannu da dawowa!”
Bai amsa mata ba, saima hannayensa daya Ιaura a gefe da gefen cikinta, yashiga shafawa a hankali, shiru tayi aΖirjinsa tana sauΖe numfashi. Ζayan hanunsa yasanya ya Ιago haΙarta, suka jefa idanunsu acikin na juna, wani irin kasalane ya dirar mata alokaci guda, sakamakon tozali da kyawawan idanunsa da tayi. lumshe nata idanun tayi, tana sauΖe numfashi a hankali, matso da tasa fuskar yayi gaf da tata, harsuna iya jiyo hucin numfashin juna, bakinsa ya buΙe haΙe da kamo lip Ιinta na Ζasa, yasoma sucking a hankali, tsikar jikinta ne, ya shiga tashi, take wani shauΖi yasoma ratsa ta, kusan mintuna 6 yana sucking lip Ιinta, kafun ya tsagaita yashiga maida numfashi. Ganin haka yasanya ta sanya hanunta akan wuyansa, haΙe da sanya bakinta acikin nasa, ta laluΙo harshensa, tasoma masa shan sweet, yanda take sucking Ιinsa tausassun laΙΙanta na kai komo cikin bakinsa shine abun da ya Ζara hautsina tunaninsa, tsananin sha’awarta ne yasake ninkuwa acikin zuciya da jikinsa. Hannayensa yasanya yana ΖoΖarin buΙe gaban rigarta. Kukan Asad ne ya katsesu daga duniyar da suke ΖoΖarin faΙawa, gaba Ιaya su sunma manta da cewa yana Ιakin. shikuwa Asad chocolate Ιinsane yafaΙi Ζasa, shiyasa sa fashewa da kuka.
STORY CONTINUES BELOW
Da sauri Zahrah ta Ζarasa garesa haΙe da Ιaukan chocolate Ιin ta danΖamasa a hanunsa, dawo da kallonta tayi ga Doctor dake tsaye idanunsa sunyi ja. Murmushi tasakar masa, tare da takawa ta Ζarasa garesa, hanunsa ta kama ta zaunar dashi akan gado, kayan jikinsa tashiga rage mai, saida ya rage dagashi dai dogon wandon suit Ιin dake jikinsa. Bathroom tashiga ta haΙa masa ruwan wanka. saida taga shigansa wankan kafun ta Ιauki Asad suka fice daga cikin Ιakin, wajen Haulat tamaida Asad, itakuma ta wuce kitchine. Milk Shake tahaΙa masa, haΙe da Ιaukan wani tray na tangaran me kyau ta yayyanka kayan marmarin aciki. Ιaukan Ιan madaidaicin tray Ιin tayi, tare da cup Ιin da milk shake Ιin ke ciki, ta nufi Ιakinta.
Harya fito a wankan yana zaune akan gado, dagashi sai long jeans ajikinsa, tanashigowa cikin Ιakin, ya kafeta da tsumammun idanunsa, Ιan madaidaicin stool ta jawo ta Ιaura kayan hanunta akai, zama tayi akusa dashi. Da kanta tasoma bashi fruit Ιin abaki. Yanacin fruit Ιin amma gaba Ιaya hankalinsa na ga breast Ιinta da suka bayyana kansu ta saman rigar dake jikinta. Sarai ta kula da cewa hankalinsa naga breast Ιinta, hakan yasa da gangan ta kuma saΙule wuyar rigan don yagani da kyau. Tana kammala bashi fruit Ιin, aka soma Ζiran sallan Magriba, alwala yayi haΙe da Ιaura brown Ιin jallabiya akan wandon dake jikinsa yafita zuwa masallaci, itama alwalan tayi, ta gabatar da sallah, bata tashi akan sallayan ba har saida tayi sallan isha. Wanka takuma yi, yanzu kam wata fitinanniyar sleeping gown ta sanya wacce iyakarta guiwa, turarenta da tasan yana tafiya da imaninsa tashafa, haΙe da Ιaukan wani wanda Ζamshinsa ke haifar da kasala, tashafa aΖasan breast Ιinta dama duk wani lungu da saΖo na jikinta.
Tana tsaye agaban dressing mirror Ιin yashigo cikin Ιakin, dawowarsa daga masallaci kenan.
Lumshe idanunsa yayi haΙe da buΙewa, idan yabiyewa Zahrah zata zautar dashi ne kawai, gaba Ιaya yawani zama soko akanta, kullum Ζara kyau da cika take, sannan kuma duk kwanan duniya Ζara fito da wani sabon salo take, wanda take rikitasa da su, ga tarin soyayyarta dake Ζara wanzuwa acikin jini da jikinsa, shikansa baisan wani irin so yakeyi mata ba, amma yayi amanna da cewa, bayan Zahrah babu wata, ita kaΙaice bata da tamka, ita ta musammance acikin matan duniya. baisan wata mace ba aduniyarsa bayan ita, amma kuma yanaji ajikinsa cewa, yayi dace, yakuma samu gamdakatar wanda bayajin akwai wata wacce zata kama Ζafarta.
Ζarasowa yayi gaban mirror Ιin ya rungumeta ta baya haΙe da kwantar da kansa abayanta, yana sauΖe ajiyar zuciya, iya Ζamshin dake fita ajikinta ma kaΙai, ya isa yasanya masa feeling, ina kuma ga ya taΙa lallausan fatar jikinta.
Hanu tasanya ta shafi gefen fuskarsa, haΙe da Ιan zame jikinta daga nasa. Hijab Ιin dake aje kan gado ta Ιauka, haΙe da zurawa ajikinta.
“Hubby Nasan Babyna yayi bacci, banaje na dubasa” tafaΙi haka tana me nufar hanyar fita daga Ιakin.
Bai iya ce mata komaiba harta fice.
Tanazuwa Ιakin Asad Ιinkuwa tasamu yayi bacci akan lallausan gadonsa, yayinda Haulat mai kula dashi itama tuni tayi bacci, zama tayi ta tofeshi da addu’a, haΙe da gyara masa kwanciyansa. Rage musu hasken wutan Ιakin tayi kana ta yi ficewarta.
Tana shiga tasamesa tsaye dagashi sai towel Ιaure a Ζugunsa, yayinda jikinsa ke Ιauke da danshin ruwa, da’alama ruwa ya watsa wa jikinsa. Cire hijab Ιin jikin nata tayi, ta nufo inda yake, atare suka sakarwa juna murmushi, jawota yayi haΙe da mannata da Ζirjinsa, hanunsa yasanya acikin gashin kanta, murya asanyaye yace.
“Nayi kewarki dear, muna gida Ιaya amma yau two days kenan banji Ιumin jikin ki ba!” yaΖare maganar yana me cusa kansa acikin wuyanta. Lokacin da sajensa ya taΙa fatar wuyanta, saida taji wani yarrrrrr ajikinta, hanunsa yakai kan cikinta, ya warware igiyan da tazamo mahaΙin rigar dake jikinta, aikuwa take rigar ta buΙe ta gaba, hannayensa duka yasa ya juyo da ita suka zamana suna fuskantar juna. kallon juna suka shigayi cike da shauΖi, hanunta ta Ιaura akan chest Ιinsa tana shafawa a hankali, lumshe idanunsa yayi haΙe da laluΙar fuskarta ya haΙe bakinsu waje Ιaya. A hankali suke sucking lips Ιin junansu, suna fidda wani irin numfashi mai sauti, cike da nutsuwa ya zame gaba Ιaya rigar jikinta, tayi Ζasa, hannayensa yaΙaura abayanta yashiga shafawa yana yawo dasu ahankali har ya gangaro zuwa kan Ζirjinta, still bakinsu na haΙe dana juna suna bawa kansu hot kiss. Saida sautin numfashinsu dukansu ya sauya, alokacin da hanunsa suka shiga yawo akan breast Ιinta, cire bakinsa yayi acikin nata kana ya gangaro da bakinnasa zuwa wuyanta, tsotseta yake son ransa, yana fidda wani irin numfashi dake nuna yana cikin tsananin mayen sha’awa dakuma sonta. Ζafafunsu ne suka soma gazawa wajen Ιaukarsu, tana acikin Ζirjinsa suka nufi kan bed. MaΖalewa tayi ajikinsa, ahankali take goga masa breast Ιinta akan chest Ιinsa, hakan kuwa sosai ya ruΙasa, tana kwance aΖasansa yayinda shikuma ya yi mata rumfa da faffaΙan Ζirjinsa, sukansu basusan awacce duniya suke ba, gaba Ιaya sun zauce, alokacin daya gama ratsa cikin jikinta, sai da wasu hawaye masu Ιumin gaske suka gangaro daga cikin idanunta, sam hawayen bana baΖinciki ko damuwa bane, wannan hawayen sukan fitane alokacin daya dace, lokacin da mutum yakasance baya acikin duniyarsa, irin wannan hawayen sukan fitane, alokacin da mutum wanda ke acikin tsananin magagin sha’awa da kuma so yasamu abun dayakeso a lokacin daya kusa zautuwa, wannan hawayen na musamman ne, wannan hawayen sukan fitane alokacin da mutum yasamu cikar muradinsa.
Yanayin da suka samu kansu aciki, yakasance me daΙi agaresu, gaba Ιaya daren sun Ζare shi ne cikin soyayya, yayinda Zahrah keta zuba masa shagwaΙa shikuma ya dage sai lallaΙata yake, koda sau Ιayane bayason abun dazai Ιata ranta. Gaba Ιaya yagama shagwaΙata, yamai da ita saikace wata Ζ΄ar 7 year. Yanzuma shagwaΙan tagama zuba masa, tana kwance luf acikin Ζirjinsa, yayinda shikuma ya kafeta da idanunsa, dake Ιauke da mayen sonta. Kissing Ιinta yayi akan goshinta, haΙe da maida duka hannayensa cikin Ζirjinta, har yau jinta yake kamar sabuwar budurwa, koda yaushe Ζara shiga zuciyarsa take, sannan babu wani abu na jikinta daya sauya daga mai kyau zuwa marar kyau, breast Ιinta har yau sunanan a yanda suke babu wani abu daya samesu, hakan nema yasa ako da yaushe yake nanuΖe mata, ya murzata son ransa, atunaninsa bacci take saboda haka yayi Ζasa da kansa zuwa Ζirjinta, wani numfashi ta sauΖe alokacin da taji hucin numfashinsa, na sauΖa akan Ζirjinta ahankali, dama baccinta baiyi nisa ba, duka hannayenta ta cusa acikin gashin kansa, tana yamutsawa slowly, ahaka har bacci ya Ιaukesu dukansu..
(Nima bacci nakeji, kuyi haΖuri typing Ιin dare nayi, yanzu nagama kuma dare yayi sosai, saboda haka da safe idan Allah Yakaimu zan sake muku shi. Please kubani Vote sosai a wannan page Ιin, Inason wannan page Ιin, da wanda zanyi gaba sufi kowanni page na baya yawan vote, next page na Zaidun mune.)
Rayuwa tana tafiya ne da gudu gudu batare da wani mai rai ya ankara da hakan ba, akullum kwanan dunia shekarunmu Ζara Ζarewa suke, sannan Ζara girma muke, sake kusantar mutuwa muke. Daga kwana Ιaya anzarce kwanaki daga kwanaki anwuce satuttuka daga satuttuka anwuce watanni daga watanni anΙarawa shekaru. Haka yake ako da yaushe, acikin waΖ΄annan kwanaki da shekarun kuma abubuwa ne masu yawa suke faruwa suke kuma shuΙewa, wani yasamu cigaba wani kuwa yasamu naΖasu, wani ransa yayi baΖi wani kuwa ransa yayi fari Ζal. To hakance takasance acikin labarin ZAID da ZAHRAH, shekaru sunja rayuwa ta haΙaka, shekaru sama da biyar kenan yanzu, har lau kuma rayuwa suke cike da farinciki….+
“MY SOUL! MY SOUL!! MY SOUL!!!” muryarsa daketa kwaΙa Ζiran sunan MY SOUL ta ΖaraΙe ilahirin farfajiyan gidan, tundaga cikin katafaren falonsa, keta kwaΙa Ζiran har ya kawo compound Ιin gidan.
Sanye yake da wando track suit sai kuma wata farar t-shirt Ζafarsa sanye suke cikin wani takalmi mai igiyoyi. Tsayawa yayi haΙe da sanya hannayensa akan Ζugunsa yana fesar da numfashi, yayinda yaketa baza idanunsa, ko zai hango wacce yake nema. Babu wani abu daya sauya ajikinsa, sai ma kyau da hasken fata daya Ζara, ga wani haΙaΙΙen Ζasumba daya daΙa Ζawata kyakkyawar fuskarsa, lallai shiΙin namiji ne cikekke, wanda zai Ιauki hankalin duk wata mace data gansa, ya haΙu sosai da sosai, duk da cewa shekarunsa sun Ζaru akan nada, amma duk da haka yana nan ayanda yake, kyawunsa da kwarjininsa suna nan, haryanzu shiΙin mutum ne mai tsananin son gayu, sam bayason Ζazanta, komai nasa me ajine. ZAID kenan namijin dayazamo abun kwatance acikin sauran mazaje, namijin daya iya jure dakon soyayya me tsananin zafi, namijin daya zamanto sadauki, akan soyayya.
Sake gyara tsayuwarsa yayi, haΙe da Ζara furta Ζiran sunan
“MY SOUL”
Da gudun gaske wata kyakkyar yarinya wacce bazata wuce 6 year ba ta Ζaraso tsalle Ιaya tayi ta haye bayanshi, lumshe idanunsa yayi, alokacin dayaji an Ιale kan bayansa, yasan babu wani ko wata da zaiyi masa wannan aikin idan ba MY SOUL Ιinsa ba. Hanunsa yasanya ya jawota daga bayansa, zamewa yayi akan guiwowinsa haΙe da Ιaura duka hannayensa akan kafaΙunta.
“MaΖoshina saura kaΙan yafashe My Soul duk kuma akanki ne, kinaji inata Ζiranki shine kikaΖi ki amsa ko?” tamkar wani Ζaramin yaro shagwaΙaΙΙe haka ya faΙi maganar.
Dariya fara kyakkyawan yarinyar da yanayin fuskarsu ke shige da tata tayi, haΙe da sanya hanunta akan dogon hancinsa.
“I’am Sorry My Papa luv, ina cikin garden ne, kuma na amsa amma bakaji ba” yarinyar tafaΙa tana Ιan juya idanunta.
STORY CONTINUES BELOW
Murmushinsa mai kyau yayi mata haΙe da jawota jikinsa ya rungume.
“Bazaki daina juya idanunki idan kina magana ba ko?” yatambayeta yana me shafa bayanta ahankali.
“Papa luv banice fa nakeyin hakan da gangan ba, nima banasanin najuya idanuna idan ina magana!” tafaΙi haka a shagwaΙe hartana Ιan buga Ζafafunta a Ζasa.
Lumshe idanunsa kawai yayi yana maijin Ζarin Ζaunar Ζ΄artasa na ratsa jini da tsokan sa, sosai yanayinta ke kama dana Zahrah babba, haka kuma Ιabi’ar Zahrah ne wani lokaci idan tana magana takan juya idanunta, to itama wannan haka ta keyi, sau da dama idan tana abu, kallon real Zahrah kawai yakeyi mata, domin kuwa yanzu da ta Ζara girma kamanninta da Zahrah sai ya sa ke fitowa, baisan wani irin soyayya yakeyiwa ZAHRAH Ζ΄arsa ba, gaba Ιaya soyayyan da yayiwa Zahrah itace ta dawo kan yarinyar, wani irin so yake yi mata da baida misali, jinsonta yake ako ina na jikinsa, Zahrah Ζ΄arsa itace rayuwarsa, itace Hasken sa, itace madubinsa, wacce idan ya duba ransa keyin sanyi, samunta yafiye masa komai aduniya, samunta wani alkhairi da ginshiΖi ne acikin rayuwarsa, domin kuwa tunda yasameta, arzikinsa suka yalwata akan nada, shikansa ayanzu baisan iya adadin dukiyarsa ba, itakanta yarinyar kamfanoni masu tarin yawa ya buΙe mata, sosai yake samun alkhairi adalilinta.
“Papa Luv!” yarinyar ta Ζirasa murya a sanyaye.
BuΙe idanunsa yayi ahankali haΙe da sauΖesu akan babyn ta sa “Na’am My Soul” ya amsa mata.
Ya mutse fuska tayi haΙe da cewa “Yunwa nakeji Papa Luv banyi breakfast ba”
Waro kyawawan idanunsa yayi haΙe da miΖewa tsaye ya sungumeta suka nufi inda zai sadasu da babban falon gidan.
Tana tsaye agaban dining area tana nunawa hause girl yanda zata shirya musu dining Ιin, tasha adonta cikin wani jan lace me kyau da burgewa, taΖara cika ta zama babbar mace, dagani kai kasan tana murza naira son ranta, domin wani haske ta Ζara tayi fat da ita. Shigowarsu cikin falon suna dariya yasanya ta maida hankalinsu gareta, batasan wannan wace irin soyayya bace ke tsakanin Zahrah da Babanta Zaid, soyyace irin ta bugawa a jarida.
Tana tsaye tana kallonsu suka Ζaraso dining area’n kujera yaja ya zauna akai kana ya Ιaura Zahrah akan kujeran dake gefensa na dama, dama kuma haka suke zama koda yaushe.
Murmushi Afrah tayi haΙe da cewa “Nashiga Ιakinka banganka ba ae, sainayi tunanin kana wajen yin gym, ashe ma kuna tare da Zahrah”
Murmushi kawai yayi haΙe da sanya hanu ya shafi kan Zahrah, baitankawa Afrah ba saima duban Zahrah da yayi cike da so yace “Me zan zuba miki?”
“Duk abunda zakaci Babana nima shi zanci!” Zahrah tafaΙi haka tana kashe masa idanunta Ιaya.
Dariya suka sanya atare haΙe da bata hanunsa suka tafa, abinci yasoma zuba musu da kansa, acikin plate Ιaya, dama kuma a yanzu baya taΙa cin abinci saida Zahrah, zaiΖi ci da kowa amma zaici da ita, kujera Afrah taja ta zauna itama, haΙe da soma yin serving Ιin kanta, don ta lura babu wani wanda yake ta ita, daga Zaid Ιin har Zahrah, su dama kansu kawai suka sani.
Shida kansa yaciyar da Ζ΄artasa, itama haka ta dinga basa abincin abaki har ya Ζoshi, sama sama suke hira da Afrah, nan ma itace take jansu da hira, amma daba haka ba bazasu kulata ba, ita har mamakinsu ma take, Zahrah sam bata damu da ita ba, kamar ba itace ta haifeta ba, zancenta baya wuce mahaifinta dakuma Momyn Friend Ιinta, wanda suke makaranta Ιaya dashi.
Tana gama goge bakinta da tissue ta kalli Papa Luv Ιinnata ashagwaΙe tace. “Please Papa luv yau muje shan ice cream mana!”
“My Soul yau inada aiki, mubari sai gobe mana, kinga fa next week zamu koma U.S.A, akwai abubuwan danakeso nayi kuma kafun mu koma” yafaΙi haka bayan ya aje kofin tea Ιin dake riΖe ahanunsa.
STORY CONTINUES BELOW
Sake shagwaΙewa tare da narke fuskarta tayi, Ιan Ζaramin bakinta taturo gaba haΙe da cewa
“Ae Dan Allah Nace Papa Luv, inaso naje ne!”
“Shikenan zo muje na shiryaki” yafaΙi haka yana mai miΖo mata hanunsa.
Tsalle ta doka haΙe da faΙawa jikinsa ta rungumesa, cike da farinciki ta kai masa sunbata akan Ζuncinsa.
“Thank You Papa Luv”
Ζagata yayi caΙak akan kafaΙunsa haΙe da sanya hanu ya kwashe wayoyinsa dake kan table, direct suka wuce Ιangarensa.
Kai kawai Afrah ta girgiza haΙe da cigaba da cin abincinta, sam abunsu baya damunta, tasaba da hakan, koda yaushe haka suke, kamar tip da taya basa rabuwa.
Shida kansa yayi mata wanka yashiryata cikin wasu riga da wando na jeans masu matuΖar kyaun gaske, naΙe mata dogon gashinta yayi a tsakiyar kanta, da wani babban ribbon, lokaci Ιaya kyawunta da tsananin kamaninta da Zahrah suka sake bayyana, shima wanka yayi kana ya shirya kansa, cikin wasu riga da wando masu kyaun gaske, sosai yayi kyau sai tashin Ζamshi yake, Little Zahrah dakanta saida tayaba kyawun da Papa Luv Ιinta yayi.
Yana riΖe da hanunta suka fito harzuwa falo, kallonsa ya maida ga Afrah wacce ta mato akan kallonsa.
“My Wife bazaki zo kirakamu bane?” ya tambaya.
Murmushi kawai tayi haΙe da lumshe idanunta, akasalance tace “Kuje kawai Dear nikam inanan, amma ku tahomin da nawa ice cream Ιin”
Hanu Zahrah ta Ιaga mata alaman bye bye kana suka fice daga cikin falon.
Barinta yayi awajen sayan kayan maΖulashe irinsu chocolate da sauransu shikuma ya nufi wajen turaruka. Tana tsaye ta Ζurawa wani babban ledan chocolate dake can sama idanu, so take ta Ιaukoshi ta sanya acikin kayanta amma kuma wane ita, ya Ιarawa tsayinta, jitayi anrufe mata idanu a hankali, a iya saninta mutum Ιayane keyi mata hakan, saboda haka yanzuma tasan cewa shiΙinne, dariyan farinciki tasaka haΙe da cewa “ASAD!”
Dariya yayi haΙe da sake mata fuska ta juyo zuwa garesa, kyakkyawan yarone wanda bazai wuce 7to8 year ba, yarone fari tas dashi tamkar ajinsin larabawa yafito, tsallen murna Zahrah tasanya haΙe da rungumesa, shima rungumeta yayi cike da jin daΙin ganin Ζawartasa wacce rabonsa da ita yau tsawon sati uku kenan, tun da aka basu hutun makaranta rabonsa da ita..
Cike da Ιokin ganinsa Zahrah tace. “Laaa Asad dama zanganka anan? kaida waye kukazo? nidai nida Papa Luv Ιina mukazo, aibansan zamu sameka anan ba da munzo tunda wuri”
Hanu yasanya ya Ιan murΙe bakinta cikin halayyarsu ta yara yace “Baki gajiyawa da Surutu Soul ina Papan naki?” yaΖare maganar yana me baza idanunsa.
“Asad me kakeyi anan, bacemin kayi chocolate zaka Ιauka kazo ba?”
Daga Asad har Zahrah atare suka juya suna kallon mai maganar. Kyakkyawar mace wacce ta amsa sunanta mace mai aji da kamala, sanye take da abaya gown black colour ta yane jikinta da mayafin abayar, komai nata na burgewa ne, kallo Ιaya zaka mata, kakuma son sakewa domin ba irin Ζananan matannan bane, duk da cewa bata da wani jiki, haka kuma bata wani sanja ba, har yanzu tana nan da kyawunta mai fusgar hankali.
“Itace Mamanka?” little Zahrah tafaΙi haka Ζasa Ζasa tana kallon Asad.
Kai Asad ya kaΙa mata alamar “Eh”
Da gudunta ta Ζarasa wajen Momyn Asad ta rungumeta, cikin surutunta daya zame mata sabo tace.
“Oyoyo Mom Asad, dama inataso mu haΙu dake, amma bakya zuwa school Ιinmu, Dad Ιin Asad ne kawai yake zuwa, ni da Asad abokaine sosai, kuma dan Allah kudawo U.S.A kunji, muma kunga can zamu koma” tunda little Zahrah tafara zuba bata tsagaitaba sai yanzu.
STORY CONTINUES BELOW
Hakanan Zahrah taji yarinyar ta burgeta, durΖusawa tayi agaban yarinyar haΙe da sanya hanu ta shafa fuskarta, hakanan taji bugun zuciyarta ya Ζaru, “Idanunta ne ke mata gizo kokuwa dagaske kamanninta take hangowa akan fuskar yarinyar?” tambayar da tayiwa kanta kenan, cike da son sanin amsa.
Murmushin da Little Zahrah tayiwa Mom Asad ne yayi sanadiyar kusan rugujewar zuciyarta. “ZAID” tafurta sunan acikin maΖoshinta da kuma kan laΙΙanta, sai dai kuma amon sauti baifito ba.
“My Soul”
Taji wata murya dabazata taΙa mantawa da ita ba tafaΙa.
Dagudu Little Zahrah takamo hanun Papa Luv Ιinta dake tsaye.
“Yauwa Papa zokaga Momyn Friend Ιina Asad, wacce nafaΙamaka tana da kirki, tana bawa Asad abun daΙi, shikuma yana bani.”
Idanunsa ya sauΖe akan bayan wata mace dake durΖushe a Ζasa tabasa baya, cigaba da jansa little Zahrah tayi harzuwa inda Mom Asad ke durΖushe amma bata Ιago fuskarta ba.
“Momyn Asad, ga Papa Luv Ιina nima, tare dashi mukazo” little Zahrah tafaΙa cike da kauΙi.
Ahankali ta Ιago manya manyan idanunta ta ta kalli mutumin da Zahrah ke cewa shine Papa Luv Ιinta.
Atare bugun zuciyarsu suka tsananta, take wani irin abu ya tsarga jiki da jijiyoyinsu.
Da Ζyar ta’iya daure zuciyarta ta ΖaΖalo murmushi.
Shima murmushin yayi haΙe da sunkuyar da kansa Ζasa.
Hanun Asad ta kama jiki asaΙule ta juya daniyar barin wajen.
“Asad” taji muryar Zaid yaΖira sunan yaron.
Tsayawa sukayi cak amma ita bata juyo garesa ba, takowa yayi har inda suke ya durΖusa haΙe da kamo hanun Asad.
“My dear ya hutu?” yatambayi Asad.
“Lapiya” Asad yabashi amsa yana murmushi.
Kallonta yayi haΙe da cewa “Dama Asad Ιanki ne?”
Kanta kawai ta jinjina masa alamar “Eh” gaba Ιaya ta Ζosa subar wajen shikuma yakama Asad ya riΖe Ζam.
Murmushin dake Ζarawa fuskarsa kyau yayi haΙe da cewa “Fine boy, natayaki murnan samun wannan kyakkyawan yaron, amma kuma saidai inajin tsoron abunda zai faru anan gaba, Asad abokin Zahrah na ne, idan nan gaba yasan nayiwa mahaifiyarsa laifi mai girma yakike tunanin zai Ιauki abun?”
Kanta ta girgiza masa haΙe da Ιanyin murmushi. “Kada kace haka Zaid, abu idan ya wuce yana da kyau amantasa, afuskanci gaba, banafatan Asad yasan abun da ka aikata agareni” Ιan numfasawa tayi tare da kama hanun Asad. “Sauri nake zanwuce gida” kallonta ta mayar ga Little Zahrah da ta Ζura mata idanu tun Ιazu, murmushi Zahrah tayi mata, haΙe da shafa kanta, sosai taji son yarinyar acikin ranta.
“Allah ya albarkaci rayuwarki Rabin raina” Tana faΙan haka taja hanun Asad suka bar wajen.
Saida ta Ιacewa ganinsa kafun yasaki wani murmushi haΙe da cusa duka hannayensa acikin aljihun wandon jeans Ιin dake jikinsa. Little Zahrah ce tataho zuwa garesa haΙe da maΖalewa acikin jikinsa, murya asanyaye tace “Papa dama kasan Mommyn Friend ne?”
Murmushi yakumayi akaro na sau babu adadi, hanunta yakama suma suka bar wajen, batare daya bata amsar tambayar da tayi masa ba.
Tunda suka shiga mota batace da yaronnata Ζalaba, shima baitanka mata ba, domin dama shi hakanan yake ba mutum ne mai son yawan magana ba, yana da miskilanci wani lokaci. Ganin da yayi cewa kamar Momyn nasa na cikin damuwa ne yasanyashi gyara zama haΙe da cewa.
“Momy wani laifi ne Papan Friend yayi miki? naji kamar yace wai bayaso muji ko mu sanine oho”
STORY CONTINUES BELOW
Harara ta watsa masa, hakan yasashi yin gum da bakinsa, shidama gulmace ke cinsa, da yasani ma da baitambaya ba.
Tana isa gida tasamu Husnah da Areefa matar Asad, sunzo suna jiranta, sam basu sanar da ita zuwansu ba, batayi mamakin ganinsuba kamar yanda tayi mamakin ganin yanda aka sauya mata tsarin falonta, aka mamaye gaba Ιaya falon da decorations masu kyaun gaske, tsayawa tayi tana Ζarewa falon nata kallo.
“Happy Birth Day to you my dear Wife!!!”
muryar Dr.Sadeeq ta karaΙe ilahirin kunnuwanta, kallonta ta maida inda taji muryartasa na fitowa.
Fitowarsa daga Ιaki kenan yasha ado cikin riga da wando na jeans masu matuΖar kyau. Murmushi tasakar masa, gaba Ιaya ita tamanta da cewa yaune birth day Ιinta.
Hanunta yakama suka nufi wani Ιan keΙeΙΙen waje dake cikin falon, sosai aka Ζawata wajen da decoration’s mai kyau, kusan suman tsaye tayi alokacin dataga irin hidiman da mijinnata ya shirya mata, manya manyan cake masu kyau da tsada yasa akayi mata har guda uku, ga kayan ciye ciye dana shaye shaye, tsananin farinciki da Ζaunarsa ne suka mamaye zuciyarta, juyawa garesa tayi ta rungumesa, haΙe da cusa kanta acikin Ζirjinsa tana shaΖan daddaΙan Ζamshin jikinsa.
“Thank you so much my lovely husband!!!” tafaΙa cikin sanyi yayinda Ζaunarsa ke Ζara ratsa zuciyarta.
“Babu godiya atsakaninmu My Wife kina da babban matsayi a wajena, keta musamnan ce, inasonki da duka zuciyata!” Dr.Sadeeq yafaΙi haka yana Ζara matseta acikin Ζirjinsa.
Kwantar dakanta tasakeyi ajikinsa cike da Ζaunarsa, haΖiΖa tasamu duk wani abu da takeso, farinciki, soyayya, da kuma zaman lafiya, sosai Doctor ke bata kulawa, bayason Ιacin ranta ko kaΙan, yana Ζaunarta har acikin jininsa, itama kuma tana Ζaunar mijinnata sosai, ayanzu yafiye mata kowa da komai, yabata farinciki haka kuma yabawa iyayenta, yamantar dasu komai na Ιacin rai da talauci, ya wadatasu da komai na rayuwa, bata da wani TAURARO sama da shi, shiΙin na musamman ne arayuwarta, koda sau Ιayane bata taΙa yin danasanin kasantuwarsa amatsayin mijinta ba, ko da kowa aduniya zai juya mata baya, tasan banda Mijinta Haskenta Abun Alfaharinta. Rayuwarta tayi mata daΙi akoda yaushe saidai tace ALHAMDULILLAH..
***
Yana tsaye agaban dressing mirror yayinda little Zahrah ke tsaye agefensa, tana shan chocolate, Afrah ce tashigo cikin Ιakin hanunta Ιauke da kofin coffee wanda take haΙamasa kullum daren duniya.
MiΖo masa kofin coffee Ιin tayi, ya amsa yana murmushi, aje kofin yayi haΙe dasanya hanu ya jawota jikinsa ya rungumeta, bakinsa ya kai dai dai saitin kunnenta, ahankali yace “Inasonki Ζ΄ar lukutar matata!”
Dariya Afrah tasanya haΙe da cewa “Nima inasonka Ιan lukutin mijina”
Murmushi kawai yayi haΙe da sanya hanu yashafi kumatunta.
“Nima inasonka Papa na!!” little Zahrah dake tsaye a gefensu tafaΙi haka da Ζarfi.
“SON SO nake miki farincikina, idan babuke acikin rayuwata, to babu wani haske dazan sake gani, Allah yarayamin ke na aurar dake ga miji na gari!!” yafaΙi haka yana dariya, acikin zuciyarsa kuwa, har yau tsananin danasanin yanda halayansa suka kasance a baya yake, yayi danasani sosai, har gobe kuma akan danasani yake, bazai kuma taΙa daina Istigfari ba har Ζarshen rayuwarsa.
Duk da Little Zahrah bata fahimci me maganganunsa ke nufi ba, amma tasan cewa mace da namiji suna aure, domin wancan satin daya wuce ma sunje auren Ζanwar momynta.
Dagudu taΖaraso ta rungumeshi, Ζasa Ζasa tace “Nidai ko zanyi aure bakowa zan auraba sai Friend, aishima yanasona ko Papa?”
DurΖusawa yayi agabanta cike da soyayyarta yace “Yanasonki mana, ai aduniya babu wani wanda zaiΖi me wannan kyakkyawar fuskar, ke Ιin ta musammance My Soul!”
DaΙine yakama Zahrah, sake rungume mahaifinnata tayi, aranta tana Ζara Ζaunar papan nata, domin adunia tasan bayan shi babu wani wanda zaiyi mata irin wannan soyayyar dayakeyi mata a yanzu……
*** *** ***
Duka ahali biyun rayuwarsu ta miΖa komai suna yinshine cikin farinciki da jin daΙi, akowacce rana ta duniya Ζara Ζaunar junansu suke, saidai muce MASHA ALLAH.
*Alhamdulillah anan nakawo Ζarshen labarin SHU’UMIN NAMIJI ina fatan zakuyi aiki da abun dayake dai dai aciki, inda nayi kuskure kuma Allah Ubangiji yayafemin, nagode sosai da sosai masoyana, haΖiΖa kunbani haΙin kai nakuma ji daΙin haka Allah Yabar Ζauna, waΖ΄anda na Ιatawa rai don Allah kuyi haΖuri, balaifina bane, haka labarin yake, haka kuma Ζaddaran ZAID da ZAHRAH yake, babu wanda ya isa sauya Ζaddaransa.
*Ku ci gaba da bibiyana Insha ALLAH Zakujini da labarai kala kala wanda ina da tabbacin zasuyi muku daΙi, Ina muku SON ΖAUNA!!! Insha ALLAH Ina zuwa muku da wani sabon labarin wanda zai Ιare ma Shu’umin Namiji, ina kuma da tabbacin cewa zaku ji daΙinsa sosai, na katse muku labarinne saboda wani babban uzuri.*
Post a Comment for "SHU'UMIN NAMIJI CHAPTER 14 KARSHE BY FATYMA SARDAUNA"