SADAUKIN SADAUKAI CHAPTER 2 by Nura Muhammad
SADAUKIN SADAUKAI CHAPTER 2 by Nura Muhammad Www.bankinhausanovels.com.ng Yayinda suka qaraso se aljani DURFAN yalura da gimbiya SAFRAH data doki kan maridi yake mutuwa. nanfa shima yabude shafin sabuwar barna. da maridan suka lura da wannan saisuka fara tsalle suna dirowa akan aljanun suna latsesu. ita kuwa gimbiya kashesu kawai takeyi ba sassauci. takashe kusan 200. saida suka wuni sunayi yaqi sannan sukaci galaba akan maridan. sauran maridan duk suka gudu suna ihu suka 6oye dikda yawansu baiwuce kimanin 26 ba. Nanfa saisuka cigabada tafiya. kusan sa’a biyar sannan suka isa bakin baqin daji nabiyu inda komai nacikinsa bakine harta bishiyoyin. saisuka lura sauran aljanun basu wuce guda 130 ba sakamakon sauran duksun mutu awajan maridan nan. Aljani DURFAN ne yace mutsaya anan domin muhuta domin damunshiga nan xamu tararda aljanu wa’inda baku ta6a ganin irinsuba, su ake kirada “jinnul uyum” sunkasance bakake kuma munanan aljanu, zamu zauna anan yake shugabata sai gobe …