ZUMUNTAR KENAN BOOK 4 CHAPTER 9 by Sumayyah Abdul-kadir
ZUMUNTAR KENAN BOOK 4 CHAPTER 9 by Sumayyah Abdul-kadir
ZUMUNTAR KENAN BOOK 4 CHAPTER 9 by Sumayyah Abdul-kadir Www.bankinhausanovels.com.ng Rausayar da kai yayi, a cikin kallona, ya lumshe idanunsa ya bude. “Yaya akayi kika sauya haka? ‘What a sudden and awkward change! I need an explanation if you want to go out”. Idanuna suka wani irin lumshe da kansu, na debo karfin zuciya na bude su tangararau akanshi. “Allah Ya hana bincike, kaga Allah Yaya Fa’iz yunwa nake ji… ka bude min kofa”. “Allah Ya hana bincike, amma ke kika yi?” Na fiddo ido na ce, “Binciken me nayi maka?” Murmushi yayi (again), “Za ki rantse da Allah baki shiga dakina ba?” “Na shiga mana, amma ban bincika komai ba wallahi, gyarawa kawai nayi”. Ya miko min hannun shi na dama na alamar karbar abu. “Bani DIARY dina!’. Na kai tafukana na rufe fuskata cikin matsananciyar kunya. “Koda na gani, ba lallai ne ya zamo na karanta ba. Kuma ma ai duk rabi Larabci ne ba iyawa nayi ba”. Ya girgiza kai, “Fa’eezah! Kin dauka ban san cewa tun kina ‘yar ficikar ki kike yara Larabci ba? Kin…