TAWA TA SAMENI CHAPTER 8 BY HALIMA ABDULLAHI K/MASHI
TAWA TA SAMENI CHAPTER 8 BY HALIMA ABDULLAHI K/MASHI TAWA TA SAMENI CHAPTER 8 BY HALIMA ABDULLAHI K/MASHI Www.bankinhausanovels.com.ng MUN TSAYA min kwatancen gidan su Anty Mimi sai tace min me zan je inyi?nace yayanmu ne ya aikeni,suka rakani suda Amira don na hau mashin tayi ma mai mashin din kwatancen inda zai saukeni muka tafi yanda Mami tayi mani kwatance haka nabi bayan na sauka a mashin nan da nana sai gani a gidansu anty mimi na shiga kannanta na samu suna wasa a harabar gidan sune suka yi min jagora har ciki nan na sami Haj Laura da wata kawarta suna hira na gaishesu da farko bata ganeni ba sai da na gaya mata daga inda nake sannan ta murtuke fuska tace zauna nan na zauna.Ta daga murya ta kwala ma Mimi kira kan Mimi ta fito sai wannan kawar tata take tambayarta wannan yar gidan wacece?maman tace yar gidan kishiyar hajiya ce yar’uwata itama ta yatsuna baki tace ai har ta haifi yar da takai girman haka?ko ba amaryasu ba?tace itama mana amma ai wannan agola ce sai shegen kankanba kan ta kuma cewa wani abu sai ga Anty Mimi ta fito tace ga…