TAWA TA SAMENI CHAPTER 10 BY HALIMA ABDULLAHI K/MASHI
TAWA TA SAMENI CHAPTER 10 BY HALIMA ABDULLAHI K/MASHI TAWA TA SAMENI CHAPTER 10 BY HALIMA ABDULLAHI K/MASHI Www.bankinhausanovels.com.ng MUN TSAYA Mami tace nawa yayanmu ya baki?nace ban kirga ba nan ta shiga zayyane masu wai wannan wace irin yarinyace,Anty Hadiza tace ai wannan daga ita har uwarta annoba ce,Anty Mimi ta cigaba da cewa kunga jiya a gabana ya bata waya irin tawa ce sak koda ganin kwalin sannan yau zamu taho nan ta zo ta rabe ya dauko mu tare kunji biyu,cikon na uku kuma sai gashi ya raba mana kudi kilan ma daidai ya raba tamkar wasu kishiyoy,nan suka taru a kaina wannan ya kai mani bugu kowa dai na fadin albarkacin bakinshi, Mami ta iso daidai lokacin da wasu kawayen Anty Mimi suke cewa asiri tayi mishi daga gani,in ba haka ba me zaiyi da wannan mummunar yarinyar gara ma ki dauki mataki tun da wuri akan abin, Mami tazo tana cewa Anty Mariya kuzo anguna sunzo fa ana ta nemanku,kan suyi magana Anty Mimi tace Mami muga jakar wannan jakar,sai sannan Mami ta ganni ina kuka tace Iman menene?Bilki tace ba’a sani ba ZAMU TASHI ke dai …