SHU'UMIN NAMIJI CHAPTER 5 BY FATYMA SARDAUNA

SHU'UMIN NAMIJI CHAPTER 5 BY FATYMA SARDAUNA
SHU’UMIN NAMIJI CHAPTER 5 BY FATYMA SARDAUNA                  Www.bankinhausanovels.com.ng  Dai dai ta ɗaura hanunta kan handle ɗin ƙofar kenan, aka turo ƙofar daga waje, cikin rashin sa’a ƙofar ya bugeta a goshi, saurin ja da baya tayi haɗe da rumtse idanunta gam, ji takeyi tamkar ta shaƙesa ya mutu, ta tsani ganin kowani irin namiji ne a rayuwarta, musamman ma shi,domin kuwa yanayinsu yana ma ta shige da Zaid, kuma gani take tamkar kowani namiji irin halin Zaid garesa,, “Ganinki tsaye anan yatabbatarmin cewa guduwa zakiyi, Miye ribarki a rayuwa idan kika gudu daga gaban i yayenki ? nasan duk inda zaki bazakiyi rayuwa mai kyauba, idan kika zaɓi tafiya can wata uwa duniya mai zaki tsinta? ina mai tabbatarmiki cewa babu wani abun da zaki tsinta sai, zallan takaici, dakuma ƙuncin rayuwa, zaman bariki kikeso kiyi? kokuwa zaman kanki kike so kiyi? ” da sauri taɗago manya manyan idanunta dasuke cike tab da ƙwalla ta watsa masa wani irin mugun kallo… “Babu abun daya shafeka da rayuwata, idan na…