SHU'UMIN NAMIJI CHAPTER 2 BY FATYMA SARDAUNA SHU’UMIN NAMIJI CHAPTER 2 BY FATYMA SARDAUNA Www.bankinhausanovels.com.ng ” Lafiya kuwa Zaid wakake nema ne ?” Bash yatambayeshi,, ɗan taɓe baki Zaid yayi haɗe da cewa ” bakomai kawai ina duba yanayin unguwar ne ” yaƙare maganar yana mai komawa cikin motarsa yazauna,,, sama sama Bash da Zaid sukayi magana, domin kwata kwata hankalin Zaid baya jikinsa, burinsa kawai shine idanunsa su sake yi masa to zali da wannar kyakkyawar fuska da jikin, daya gani…..+ Tunda Zahrah tafito daga gidan su Husnah tafuskanci cewa da akwai mai binta a baya, hakan yasanya taji wani irin tsoro ya ɗarsu acikin zuciyarta, don haka ta ƙara ɗaga ƙafufunta, “Assalamu Alaikum !!” muryan Namiji mai cike da kamala ya doki dodon kunnuwanta, cak ta tsaya da tafiyan da takeyi batare da ta juyo ba,, cikin takunsa na burgewa ya ƙaraso gareta, kyakkyawan saurayi ne, mai ɗauke da launin fata choculate colour, dogo ne amma ba har canba, yanada faffaɗan jiki mai burgewa, sannan yana da kwarjini ba laifi,, m…