RUBUTACCIYA BOOK 4 CHAPTER 4 BY FATIMA IBRAHIM GARBA DAN BORNO

RUBUTACCIYA BOOK 4 CHAPTER 4 BY FATIMA IBRAHIM GARBA DAN BORNO
RUBUTACCIYA BOOK 4  CHAPTER 4 BY FATIMA IBRAHIM GARBA DAN BORNO    Www.bankinhausanovels.com.ng  MUN TSAYA soyayya tana matuKar riKe aure, musamman ma idan ladabi yana ciki. Domin ladabin aure shi ne magin cikin aure, soyayya kuma ya goya masa baya ya zama gishirin da ke cikin aure. Haka suka ci gaba da hira cike da annashuwa, haka kamar ba kudi ake cirewa ba. Ya ce mata ta riKe wayar zai dinga kiranta. Ta yi godiya ta ajiye wayar tana jin natsuwa tana shigarta. Jidda ce ta shigo tana murmushi, sai dai Nasreen ba ganinta take yi ba, don haka ta yi shiru. Jidda ta ce, “Wallahi muna dawowa Najeriya zan ziyarci shagon Jafar dinnan da kaina ba sako ba. Kai amma dai Yumnah ta ci amanar zaman tare, shegiya sai shige-shige ka rasa wa yake gaya mata irin  Www.bankinhausanovels.com.ng  wadannan sirrikan.” Nasreen ta yi murmushi ta ce, “Wa zai gaya mata idan banda ‘yar mutan Borno? Ita ta gaya mata komai. Shiyasa na gama kula kamar ta fi son Yumnah akan mu.” Jidda ta girgiza kai, “Ke kike ganin hakan…