RUBUTACCIYA BOOK 4 CHAPTER 3 BY FATIMA IBRAHIM GARBA DAN BORNO

RUBUTACCIYA BOOK 4 CHAPTER 3 BY FATIMA IBRAHIM GARBA DAN BORNO
RUBUTACCIYA BOOK 4  CHAPTER 3 BY FATIMA IBRAHIM GARBA DAN BORNO  Www.bankinhausanovels.com.ng  MUN TSAYA  Nasreen ta ce, “Kullum sai na yi maka  maganar ibada, amma sai kayi fatali da maganata, ka nesanta kanka da Allah shiyasa wannan abubuwan suke ta faruwa da kai. Kadage da addu’a ka yaki duk mai nufinka da ; sharri.” Ya ce, “Babu komai zan sake dagewa, idan zan je Masallacin sai in ji kamar ansa igtyoyi andaure ni.” Suka sake yin shiru, can yace “Barci nake ji ko za ki raka ni?” Bata karga mayana ba, wayarsa ta dauki kara. Ganin lambar Umma yasa ya dauka, “Gidan uban wa kaje? Ashe da kai za a tafi lagos din shi ne bani da mutuncin da zaka gaya min?” Sultan ya shafi kansa kamar tana ganinsa ya ce, “Umma ki yi hakuri don Allah, gobe insha Allahu zan dawo.” Umma ta ce, “Ya yi maka kyau Sallamammai. Saura ka takura mata tunda kana sane aiki za ayi mata.” Umma ta fada haka cike da damuwa da addu’ar kada Sultan ya aikata wani kuskure da zai hada jininta da shegu. Sultan ya dubi Nasreen yana…