RUBUTACCIYA BOOK 4 CHAPTER 12 BY FATIMA IBRAHIM GARBA DAN BORNO
RUBUTACCIYA BOOK 4 CHAPTER 12 BY FATIMA IBRAHIM GARBA DAN BORNO RUBUTACCIYA BOOK 4 CHAPTER 12 BY FATIMA IBRAHIM GARBA DAN BORNO Www.bankinhausanovels.com.ng MUN TSAYA Umma ta sunkuyar da kai, hatta danta kunyarsa take ji sosai. Shi kansa Abba ta kasa~ ganin fuska a wurinsa. Sultan ya nemi? wuri ya zauna, duk suka yi shiru a dakin. Ya dubi Hafsat ya ce, “Zan sa a kama Salim, sai ya dandani irin bakin cikin da yasa mu -ciki. Hafsat har yaushe kika yi wayewar bin saurayi gida? Ina. tunaninki yake? Ina iliminki da wayonki? To sai kin haife cikin kuma dole ya aureki, bayan ya gama shan wahala gidan yari.” Ya mike kawai ya fice ‘yana jinjina wai Umma ce ta makantar da Nasreen saboda tsabar Kiyayya. Washegari Sultan suka wuce Abuja, kasancewar ya sami kiran gaggawa daga office ZAMU TASHI A gida ya ajiye Nasreen ya wuce abinsa. Tana shiga ciki ta kama gyara ba tare da ta duba bangaren Zakiyya ba, komai ta shirya shi a ma’adaninsa tana jin tunanin mutumin da aka kira a matsayin mahaifinta yana ci gaba da addabanta. Har ta gama abincin bata bar tunaninsa ba. …