RUBUTACCIYA BOOK 3 CHAPTER 11 BY FATIMA IBRAHIM GARBA DAN BORNO
RUBUTACCIYA BOOK 3 CHAPTER 11 BY FATIMA IBRAHIM GARBA DAN BORNO RUBUTACCIYA BOOK 3 CHAPTER 11 BY FATIMA IBRAHIM GARBA DAN BORNO Www.bankinhausanovels.com.ng MUN TSAYA Haka ta kama hannunsa suka shiga daki. A ranar sai da dukkan Karfinsa ya Kare wajen Zakiyya, ya sha wahala fiye da tunaninsa. Haka ya kasa ko da motsawa. Ita dai Nasreen ko da ta ji shiru bata damu ba, saboda ta riga ta san da wahala Umma ta sake barinsa. Duk da zuciyarta tana gaya mata sai ya san yadda zai yi ya shigo. Shiru-shiru babu Sultan babu dalilinsa. Tun tana iya jurewa har hawaye suka fara aikin su. Har bayan Sallar isha’i babu wanda ya sa Sultan a idanunsa. Umma ta gaji ta aika Hafsat ta dubo shi. Hafsat tana shiga sashensa ta tsaya tana Kwankwasa Kofa. A lokacin Nasreen ta fito falo, haka itama Umma tana zaune da Kafarta, tana addu’ar Allah yasa lafiya Sultan bai fito ba, gaba daya ta shiga damuwa. Hafsat ta jima a tsaye, sannan Zakiyya ta bude Kofar ta tokare tana dubanta sama da Kasa. “Lafiya kike Kwankwasawa mutane Kofa?” Mamaki yasa Hafsat Kare mata kallo, sannan ta …