RAYUWAR CAMPUS CHAPTER 15 BY Fateeyzah mbs✍️ RAYUWAR CAMPUS CHAPTER 15 BY Fateeyzah mbs✍️ Www.bankinhausanovels.com.ng …….D’abi’ar tasa kuwa itace, Gaba d’aya rayuwarsa irin ta yahudawa ce, sannan ya tsani wani ya rab’esa, ke hatta dangi basu zuwa wurin mu bamu zuwa wurin su, saboda ni dai da girma na so d’aya muka tab’a zuwa bauchi sanda kakanmu ya rasu, shima bamu kwana ba muka dawo, saboda a labarin da muka samu shi kanshi Daddy ya taso babu mahaifiyarsa a gidan, kuma tunda ta bar gidan tana raye, ita ko wani d’an uwanta basu tab’a zuwa wurin shi ba, haka ya taso cikin wahala da musgunawar matan babansa har Allah ya d’agasa, shi yasa gaba d’aya ya yanke wata alak’a ta zumunci dasu, yanda d’abi’arsa take haka ya cusa mana ita, shi dai ayi boko kawai, saboda a ka’idarsa yaransa maza sai sunyi *PHD* zai aurar dasu, mata kuma sai mun kammala *Masters*, karatun addini kuma sai dai na sallah, shima shi ya koya ma manyan salla, mu kuma k’ananan muka koya a wurin manyan. Maganar tarbiya kuma babu ita, don ba yanda za …