RAYUWAR CAMPUS CHAPTER 12 BY Fateeyzah mbs✍️ RAYUWAR CAMPUS CHAPTER 12 BY Fateeyzah mbs✍️ Www.bankinhausanovels.com.ng Bangaren mummy kuwa, irin matan nan ne wad’anda basu damu da kowa ba sai kansu, ciki kuwa har da ‘ya’yan da suka haifa, sannan kuma tana da wani hali, na bata iya taimakawa miji da ko k’wandala a harkar da ta shafi gida, don acewarta duk wannan hakk’in namiji ne, wannan yana d’aya daga cikin abunda yasa bata kula damu, duk abunda zamu tambayeta zata ce muje wurin Daddynmu ai ba hakk’inta bane ta mana, a rayuwarta bata son kowa ba sai kanta, zan iya ce muku da wayau na ban tab’a cij k’wandalar mummy ba. Sannan suna da wata ak’ida ta fad’a a tsakaninsu, a gaban kowa zaku ji suna maida ma junansu da magana, saboda dukkansu babu mai hak’uri, wani halin nasu baxan iya fad’anshi ba don kasancewarsu iyayena. Haka muka taso a wannan rayuwar, wannan yasa daga ni har Alameen muka tsiro ma kanmu wata irin rayuwa, da farko muna d’aura ma kanmu dogon buri, da kuma d’aura ma kai wahala wanda ya samo asali…