RAYUWAR CAMPUS CHAPTER 10 BY Fateeyzah mbs✍️

RAYUWAR CAMPUS CHAPTER 10 BY Fateeyzah mbs✍️
RAYUWAR CAMPUS CHAPTER 10 BY Fateeyzah mbs✍️               Www.bankinhausanovels.com.ng   *_Marubuciyar_*  *_Gidan nagoggo_*   *_Doctor zahrah_*  *_Yakin Mata (aure)_*   *_Kuda wurin kwadayi_*  _Tukwicine ga daukacin matan jami’a_   *_ﺑﺴﻢ ﺍﻟﻪ ﺍﻟﺮ ﺣﻤﻦ ﺍﻟﺮ ﺣﻴﻢ_* Kallon da nayi ma Anisa bayan haihuwarta shine kallona da ita na k’arshe, har yau ban kuma sakata a ido ba, domin a daren ranar Aunty Yakurah ta sa Bukar yamin saki biyu, tare da cilla mini dubu biyar inyi kud’in mota dashi, hankalina ba k’aramin tashi yayi ba saboda ganin k’iri² an raba ni da ‘yata da ban gama warkewa daga nak’udarta ba, haka Aunty yakurah tamin koran kare, ina tafe jini na bin k’afata har tashar mota, inda Allah ya taimakeni ina zuwa wata trailer ta gama lodin kifi, nan na biyasu suka karani a baya, ganin halin da nake ciki yasa drivern ya siyo mun pad ya bani domin in gyara jikina, samin wuri nayi na k’ebe na saka, tukunna motarmu ta tashi, mun dauki kusan kwana hud’u a hanya kafin mu isa, saboda tsaye tsayen da drive…