NA SHIGA ALJANNAH BOOK 4 CHAPTER 7 BY MAIMUNA IDRIS SANI BELI
NA SHIGA ALJANNAH BOOK 4 CHAPTER 7 BY MAIMUNA IDRIS SANI BELI NA SHIGA ALJANNAH BOOK 4 CHAPTER 7 BY MAIMUNA IDRIS SANI BELI Www.bankinhausanovels.com.ng MUN TSAYA Salmanu ya ga Adamu na gyara wajen kwanciya zai kwanta, ya ce masa, “Ni fa ban gane maka ba”. Adamu ya dago cikin rashin hayyaci ya dubeshi, “To hayatu, ina fatan ba wani daga hankalin zaka yi min ba…” “Haba sai na sake daga maka wani hankalin ban da wanda kake ciki?” Adamu ya dan yi nishi, “Hnm!” Sannan ya mayar da kai ya kwanta. Salmanu yace, “Allah sarki, yanzu kiyayyar Husna ta shafi Salma kenan? Dalilin kin Husna ka zabi ka kauracewa Salma ma?”. Adamu yayi shiru bai tanka ba, amma fuskarsa tana nuna alamun rauni. Sun jima cikin shiru dukkansu, sannan babu zato babu tsanunani suka ji Adamu na shasshekar kuka. Tanimu da Salmanu suka dubi juna, cikin su babu wanda ya tanka. Sai da Adamu yayi abinsa ya ishe shi sannan ya dago ya dubi Salmanu, “Wai wa yace maka ba na son Husna ne? ZAMU TASHI Salma ce bata son ta, ina tsoron zuwa gidan ta yi min umarnin in sake ta”. Duk…