NA SHIGA ALJANNAH BOOK 3 CHAPTER 9 BY MAIMUNA IDRIS SANI BELI
NA SHIGA ALJANNAH BOOK 3 CHAPTER 9 BY MAIMUNA IDRIS SANI BELI
NA SHIGA ALJANNAH BOOK 3 CHAPTER 9 BY MAIMUNA IDRIS SANI BELI Www.bankinhausanovels.com.ng MUN TSAYA Salmanu na gefe yana yi masa jinjina, wannan ne ya sanya shi Kara Bata murya ya ce, “To kar ki je ko ina, na fasa_ barin unguwar’. . Www.bankinhausanovels.com.ng “Sai ta sauke ajiyar zuciya kafin fargabar abinda hana ta fitar zai haifar mata ya biyo baya, kar ta fita ta je gidan bokanta? Abinda ba zai yiwu ba kenan. Ita ma ta dan bata rai ta ce, “Gaskiya Yaya Adamu A’a, har fa na yi waya da su gwaggo, suna nan suna ta shirya gangamin hidimar zuwana…”. Dayake wayar Adamu na da Kara, Salmanu_. yana jiyo abinda Salma ke cewa, don haka yake ta yi wa Adamu inkiyar budewa Salma wuta, Adamu kuwa ya tunzuru, don haka ya iya tare. Salma da baKar magana, In don abincin da zasu shirya miki ne. wanda ba kya cin irinsa a nan gidan, idan na taso daga sabgata na biya gidan gwaggon na taho miki da shi, ai zasu ba ni ko?”. Mamaki da haushi ya Kara turniKe Salma, . bakinta na karkawa ta ce…