MY BESTIE'S HUSBAND CHAPTER 6 BY REAL FAUZAH TASIU
MY BESTIE'S HUSBAND CHAPTER 6 BY REAL FAUZAH TASIU
MY BESTIE’S HUSBAND CHAPTER 6 BY REAL FAUZAH TASIU Www.bankinhausanovels.com.ng Shiru ce ta ratsa gurin na dan wani dogon lkc kowa zuciyarsa na searching abubuwa da dama mabambamta, zumbur Ja’afar ya miqe ya nufi qofa zai fita Mai martaba ya rufa masa baya shima Jamal miqewa yayi suka fita daga gdan duk wani guri da suke tunanin rafi’ah sun kasa samunta wasa wasa sai ga lkc yanata tafiya har goma na safiya shikam Ja’afar ya zamana kamar wani robbot ko bakinsa bai iya budewa sai tafasa da zuciyarsa takeyi. Mai martaba ne yace da Jamal su juya suje gdansu Rafi’ah sugani ko taje can hakan ce ta faru suka nufi gidansu Rafi’ah Mai martaba yasa akayi masa sallama da Abba dake asabar ce Abba ya fito ganin Mai martaba da kansa yasashi qarasowa da saurinsa yanayi musu sannu da zuwa yanda yaga dum jikinsu a sanyaye ya fadar masa da gaba yace “meye yake faruwa ne naga kamar Kuna cikin damuwa?” Ja’afar ne ya magantu a karon farko yace “Rafi’ah batazo ba ko Abba shikenan na shiga ukuna ta…