MOON CHAPTER 7 BY NIMCYLUV MOON CHAPTER 7 BY NIMCYLUV Www.bankinhausanovels.com.ng Saurin zare jikinta tayi ta nasa ta shiga haɗe fuska, Murmushi Faizak yay mata yana jin ransa babu daɗi cikin ƙasa da Murya yace “Am sorry,i can’t control myself idan muna tare” banza tai masa sai hawayen da suke shiga zuba daga cikin idanunta zuwa saman fuskarta,da sauri kuma ta fara tafiya tabar masa lambun gaba ɗaya, iska ya fesar kafin yace “what should I do?” Ya faɗa yana dafe kansa dake juya masa,da sauri shima yabar cikin lambun kai tsaye ɓangaren dawakai ya nufa ya samu sarkin dawakai suka fara mgna kafin a ɗauko masa wani farin doki ingarma mai girman gaske,da sauri ya kama silken dokin ya hau cikin sauri kuma ya saki linzamin dokin yay waje da gudu.. washegari ta kama Friday tun asuba ta tashi da wani irin ciwon ciki mai a zabar gaske ga wani kumburi da mararta tayi mata, ciwon kai zazzaɓi duk suka taro waje guda sukai mata yawa, da ƙyar ta lallaɓa tai sallar asuba ta koma ta kwanta a hankali bacci yay g…