ZUMUNTAR KENAN BOOK 4 CHAPTER 7 by Sumayyah Abdul-kadir
ZUMUNTAR KENAN BOOK 4 CHAPTER 7 by Sumayyah Abdul-kadir
ZUMUNTAR KENAN BOOK 4 CHAPTER 7 by Sumayyah Abdul-kadir Www.bankinhausanovels.com.ng *** Cikin wannan mawuyacin hali da sabuwar rayuwa mai wahalar da dan Adam a zuci da gangar JIKI da RUHI, duk da tarin jndadi da daular da ke zagaye dani, na cigaba da gurgurawa har tsayin wata guda. Ya zamanto ba abinda ke burgeni, ba abinda zan ci inji dandanonsa sai dai inci don in zauna da hanjin cikina lafiya, ba abinda nake son ji da gani sai FA’EEZ da MURYARSA… Wadanda ya haramta min haihata-haihata ya kuma toshe duk wata kafa da zan same su daga iyaye da ‘yan uwa. Hutunsu Walida tuni ya kare amma nayi tsalle na dire na hana su komawa gida balle su koma makarantar, in sun bar gidan ban san makomar rayuwata cikin wannan fankacecen gida ba. Domin dai komai na gidan tun zuwansu su suke tafiyar dashi, girki da tsaftace shi. Abinda nasan ina iyawa kawai shi ne jefawa Dawisu kwayoyin dawa da sake musu ruwan sha idan yayi kura. Na daina ado, na daina wannan kwalisar. Hana rantsuwa nasan ina…