ZUMUNTAR KENAN BOOK 4 CHAPTER 6 by Sumayyah Abdul-kadir

ZUMUNTAR KENAN BOOK 4 CHAPTER 6 by Sumayyah Abdul-kadir
ZUMUNTAR KENAN  BOOK 4  CHAPTER 6 by Sumayyah Abdul-kadir                 Www.bankinhausanovels.com.ng  *** Washegari haka na tashi sukukui! Babu kuzari ko yaya a cikin jikina. A wannan lokacin, babu abinda nake tunani illa hanyar da zan bi na gyara girgidadden aurena tun lokaci bai kure min ba. Kaunar Fa’iz da soyayyar sa ke lallasa ni ta duk hanyar da suka ga dama. A duk lokacin da na daga ido na dubi tangamemen hotonmu (window size) da aka manna a (main-palour) kamar za muyi magana, sannan tsananin kamar mu da juna ta fito sosai a hotunan. Kyau ne ke bugun kyau na mallawan usili, sai kwarjini da ya dara mini da wasu ilhamomi na daban da aka halicci Fa’izun dasu da ban taba ganinsu a tare da wani da namiji ba. Nakan tuno abubuwa da dama na irin cin kashi da rashin arzikin da na shekara yiwa iyayena da ‘yan uwana akan auren mutumin da na tabbatar ban dace da kowa ba cikin duniyar nan face shi, sai inji na tsani kaina da mata masu irin halina na kafiya da taurin zuciya, riko da zuciyar rashin…