ZUMUNTAR KENAN BOOK 4 CHAPTER 5 by Sumayyah Abdul-kadir
ZUMUNTAR KENAN BOOK 4 CHAPTER 5 by Sumayyah Abdul-kadir
ZUMUNTAR KENAN BOOK 4 CHAPTER 5 by Sumayyah Abdul-kadir Www.bankinhausanovels.com.ng *** Na wayi gari ne yau cikin matsanancin nishadi, irin wanda ban taba tsintar kaina a ciki ba. Don haka na share ko’ina na goge lungu-lungu da sako-sako na gidan ya zama tas, sai sheki yake kamar lomarka zata fadi ka sanya baki ka side, duk da gidan ba wani datti yayi ba, don akai-akai nake kula da tsaftarsa. Na samu kaina da son shiga dakin Fa’iz, ko na rage kewar sa data addabe ni. A hankali na murda kofar na shiga dakin ga mamakina a bude ya barshi, sallama dauke a baki na. Fa’eez ya kawata dakin baccinshi da duk wani nau’in kayan jin dadin rayuwa. Duk da A/c a kashe yake, amma dakin da sanyinsa, wanda ya hadu ya cakude da sassanyan kamshin ‘212’n da Fa’eez ke amfani dashi (on a regular basis). Babu komi dake cikin dakin da aka saye shi cikin Kadunan, bayan gidan Fa’iz kadai abin kallo ne, wanda bai cika girma ba. Banda katifar ruwa data mamaye gadon shi, karamin ‘frame’ din dake aj…