ZUMUNTAR KENAN BOOK 4 CHAPTER 3 by Sumayyah Abdul-kadir
ZUMUNTAR KENAN BOOK 4 CHAPTER 3 by Sumayyah Abdul-kadir
ZUMUNTAR KENAN BOOK 4 CHAPTER 3 by Sumayyah Abdul-kadir Www.bankinhausanovels.com.ng Tayi dariya sosai, “Ni kuwa ake maganar arziki dani, ‘yar Abubakar uwar Abubakar da Fa’izah, uwa ga Zanira uwa ga Ummi, sha lelen Muftahu autar Hajjah. Kirarina kenan, na zama duwawu dole a zauna dani. Tafiya ta tashi ko? Birtaniya ko Murtaniya? Na so ace nazo rakiya Allah bai yi ba, naji tafiyar taku ne ba shiri, a tabbatar in za a dawo da baby aka taho min sai inzo in zauna zaman dabaro mai dalili…”. Nayi tsaki na katse wayar don nasan in ta Ya Rabi ne sai mu kwana muna yi bata gaji ba. Ga haushin da take kara kuma mini ta barni inji da wanda nake fama dashi. Mama ta dubemu duka tana murmushi bayan ta karbi wayarta. “Komai lafiya ko?” Tana duban Fa’iz. Ya hade gira ya ce, “Tambayeta mana Mama!”. Mama ta ce, “Fa’izah ta ina Fa’iz ya kuskuro ki ko ince yake bata miki?” Na girgiza kai kaina a sunkuye. “Babu Mama”. Ta dube shi, “Fa’iz Giwa fa?” Ya ce, “Mama ba sharri ba, tunda dai gatanan a zaune …